YADDA ƘADDARA TA SO 20

67 5 2
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: (Salma Ahmad Isah Sai Kaska)
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Na sadaukar da wannan babin gare ki Bilkisu H Muhammad*

*BABI NA ASHIRIN (20)*

.........“A duk sanda zanyi sallah, dana na yi takbiratul ihram sai na ji kamar wani abu ya fita daga jikina, kamar akwai wani gingimemen dutsi a kaina da aka sauƙe min, kamar da a ɗaure nake sai aka sakeni, kamar kuma ina ƙarƙashin sarrafawar wani abune, bana tantance yanayin amma sai naji ni wasai, ina jin cewa nine, nine ni a karan kai na, inayin sallahta a nutse, amma daga zarar na yi sallama, wannan nauyin dake kaina da zai dawo, wannan ɗaurin da a kamin zai dawo, zanji kamar ana sarrafani, kamar bani bane, bani bane akaran kai na, rayuwata akwai wahala WIFEY, shi yasa nake ganin lefin su Fulani da suka sakoki a cikin rayuwata, rayuwata bata da alƙibla, rayuwa nake ba irin ta sauran mutane ba, na banbanta da sauran mutane, sam bana farin ciki, duk dariya ko murmushin da zan yi yakan tsaya akan lebena ne kawai, baya kaiwa har cikin zuciyata, ko kaɗan bana farin ciki, saide kuma inasan naga na saka wasu farin ciki, tunda ni bazan samu ba me zai hana na bawa wasu, amma kuma Maryam shigowarki rayuwata ya sauya wasu abubuwan, a da baƙin ruhina baya kusanta ta sai raina ya b'aci, amma a wattanin nan da muke ciki sai abun yayi ƙamari, ya dawo yana tashi kullum, saide tun daga ranar da aka ɗaura mana aure bai ƙara tashi ba, saide kl nayi wannan....”
Ya ƙarashe yana nuna mata ƙwayar idonsa.
“Kuma kece kaɗai kike sakani naji cewa bani kaɗai ba ne, ina da wani, duk da ina da ƴan uwa amma kullum cikin kaɗaice nake jina, abubuwa sunmin yawa akai na, banajin daɗi jikina kullum, ko kaɗan wanna ba rayuwata ba ce”
Sai yaji wani nauyi dake zuciyar sa ya sauƙa, kamar wani dutse aka ɗora akan kirjin sa kuma aka sauƙe haka yake ji, yaji shi free domin ya amayar da abinda ke damunsa tsawon shekaru, bai tab'a zama ya bajewa wani ciwonsa haka ba, ko Neha da yafi kusancin da ita fiye da kowa bai tab'a magana da ita irin haka ba, bai tab'a ba, amma kuma kullum abun na ci masa zuciya, har yana barazanar hanashi numfashi, kuma duk abinda ya faɗa mata haka ɗin ne, baya jinsa daidai, baya farin ciki, yanajin kamar rayuwar tasa ba tasa bace, kamar ana sarrafashi ne, yanzu haka sai da yayi kokawa da wani abu sannan ya iya amayar da wannan maganganun.
“Ke kalleni nan”
Maryam na goge hawaye ta kalleshi, har idonta ya sauya kala zuwa ja, matsowa kusa da ita yayi ya kai ɗan yatsansa ya goge mata hawayen, a tarihin zamansu karo na farko daya fara tab'a jikinta kenan.
“Ki dena kuka is not good for you”
Maryama ta gyaɗa masa kai, wayarsa dake tsallaken island ɗin ta shiga playin waƙar Teri meri khani, hakan ke nuna wa Tafida cewa kira ne ya shigo, dan haka ya miƙe, ya dafa kan maryam sannan ya ɗauki wayar tasa da glasses ɗinsa ya fita.
Bayan Maryam ta iya ƙarfafa kanta ta dena kukan ta ɗauki sauran cake ɗin da bai ƙarasa ci ba, dama wanda ta haɗa ɗin duka ta saka a fridge, ta tattare duk abinda ta bata ta saka a cikin dishwasher na cikin dishwasher ɗin kuma wanda ta wanke ta ɗebesu ta sakasu a inda ta saba ajewa.
Batajin ko cake ɗinma zata iya ci, dan haka ta fita daga kitchen ɗin, fitowar tata ta yi dai-dai da shigowar Tafida daga Ƙofar waje.
Ido suka haɗa sai ta ganshi da baƙin glass har yanzu, taji tausayinsa ya ƙara kamata, hannunsa ta kalla taga ledoji har biyu, bata ce masa ƙala ba ta yi hanyar hawa sama.
“Wifey tsaya mana”
Maryam ta tsaya da tafiyar da take, a hankali ta ɗaga kanta sama tana so ta hana hawayen dake san zubowa sauƙa. Sai da ta tattabar da bazasu sauƙo ba sannan ta juyo, a lakocin Tafida har ya zauna akan kujera, da hannu ya yafito ta, dan haka ta dawo cikin parlon.
Gefensa ya nuna mata alamun ta zauna, sai ta zauna ɗin tana kama hijabin jikinta, yayin da shi kuma yake fitowa da wani kwali daga cikin leda.
“Desktop led ring light ne, tunda zaki fara food blogging”
Ya faɗi a lokacin da yake ciro kwalin, Maryam kawai kallonsa take, tana mamakin yanda yake iya b'oye abunda ke ƙarƙashin ransa.
Shi da kansa ya haɗa ring light ɗin, ya jona da wuta hasken ring light ɗin ya haske fuskar Maryam dan a setinta ya ajeshi, Maryam ta kai hannu ta tare fuskarta.
“Ha kawo ko ?”
“umm”
Ta amsa shi da ƙyar, sai kuma ya zare shi daga socket ɗin, sannan ya dawo ya zauna a inda ya tashi.
“Kinga yanda yake working ko ?”
Maryam ta gyaɗa masa kai, sai kuma ya janyo ɗayar ledar, ita kuma bai buɗe ta ba ya miƙa mata kawai.
“Kije ki, a ina zan aje miki ring light ɗin ?”
Maryam ta karb'i ledar tana miƙewa, bata amsa shi ba, sai kama ring light ɗin da ta yi ta aje shi a kusa da TV stand sannan tayi sama.
A kan gadonta ta zazzage ledar daya bata, hijabaine kusan kala goma, Maryam ta zauna a bakin gadon tana kallon hijaban hawaye na cika mata ido, ya kamata ace tayi wani abu akan rayuwar bawan Allahn nan.
Bai kamata ace ta barshi cikin wannan halin ba, ya zama dole ta temaka masa, kamar yanda ya temaki rayuwarta, sam bai kamata ta zuba ido tana ganinsa haka ba, she need to do something.

YADDA KADDARA TA SOWhere stories live. Discover now