Kamar yadda sarah tafada bayan kwana biyu tasake kaima emaan xiyara,acikin kwana biyun nan babu abinda ya canxa a relationship din alameen da emaan,sai ma fadan dasukayi wanda emaan tasha mamakin kalaman dasuka fito daga bakin alameen,even though bai kamata kalaman nashi su bata mamaki ba considering yadda ya tsaneta fiyeda misali,da wuri ta yi wanka kasancewar Sarah tace mata da wuri xataxo saboda su samu damar tattaunawa dakyau,saida tagama shiryawa cikin wani tummy skirt da shirt sannan tayi musu order base on sarahs choice,misalin k'arfe biyu taxo kuma fortunately alameen baya gidan,hakan ne yasa emaan feeling comfortable ta hau sama dasu,a parlor suka xauna sannan emaan takawo mata drinks and small chops,keenly sarah ke kallon emaan wacce taketa mitar meyasa bataxo da Asad ba,itadai sarah murmushi kawai takeyi tana kallon emaan closely,can tace"maganar daxan miki is very important emaan,saide bansan ta yadda xaki dauketa ba,but I'm sure inde kika saurareni baxakiyi dana sani ba"shiru emaan tayi can tace"I'm all ears"nisawa sarah tayi sannan tace"acikin kallo daya dana muku keda mijinki na tabbatar akwai distance mai karfi atsakanin ku,wanda is very obvious,a bayyane yake kuma kowa na iya kallo,wanda hakan is not right emaan,bai kamata ace kin bar relationship dinku ya lalace haka ba,even though bansan mafari ko kuma silar distance din naku ba,but I'm sure idan kika fahimtar dani xan dora ki akan hanyar data dace"tunda Sarah tafara magana emaan ta saki baki da hanci tana kallonta,duk da yauce rana ta farko data ji xata iya fadama wani matsalarta aduniya,saide still batada courage din yin hakan,fahimtar hakan da sarah tayi ne yasa ta riko hannun emaan tace"feel free emaan,ki fada min koma menene nikuma I'll advice you kamar yadda xanyi advising younger sister dina".asanyaye emaan tace"labarin mai tsaho ne mummy Asad,in short dai forced marriage ne,duk mu biyun bama son juna,kawai dai muna xaune ne kafin lokacin rabuwa yaxo "xaro ido sarah tayi tace"daina kiran rabuwa emaan,yanxu na fahimci lamarin naku,saidai kuna bukatar enough time ku sake fahimtar juna kafin axo kan gabar da zan baki shawarwari,for now dai naga bakida matsala wurin kula da gida,sauran abubuwa xasuyi falling into place in shaa Allah"itadai emaan kallon sarah kawai takeyi tana mamaki,Sarah tace"emaan you're calm,beautiful,classy uwa uba kuma kinada tarbiyya,shima mijin naki is okay,abinda nakeso ki fahimta shine shi mijinki ne kuma ke matar shi ce,sannan ke ce mace kece xaki iya jawo shi xuwa gareki,kece zaki ɗana mishi tarkon daxai cafke kafafauwanshi without him knowing,trust me yadda kike ahaka wallahi namiji ya shiga hannunki sai yayi worshipping ƙasar da kike takawa,abinda nake so dake shine ki kwantar da hankalinki,ki cire batun kiyayyah agefe ku gyara rayuwar aurenku,bakiga yadda kuka dace da juna ba..."xaro ido emaan tayi tana kallon sarah,hasalima dariya lamarin ya bata,tace"nifa tun asali baya burgeni,balle yanxu da ya nuna min baya kaunata "murmushi sarah tayi tace"Haba emaan saikace ba mace ba,you should make him love you,it's that easy,kinsan sufa maxa yadda suke tunani daban ne da namu"....ajiyar xuciya emaan ta sauke saboda gabadaya maganar sarah is making her feel uncomfortable,sarah tace "you don't need to worry,da kadan-kadan xaki fara"...wani banxan murmushi emaan tayi wanda ya tabbatar ma Sarah ba jin maganarta takeyi ba,haka yasa sarah ta wurga mata throw pillow tace"xan gyara miki xama dole"murmushi kawai emaan tayi without saying a single word.

da murmushi fauxa ta shiga dakin Sadeeq tana fadin"daddy Anum your kids are back.."tafada tana karasawa daf dashi,murmushi ta saki tana kallon yadda ya lumshe idanu,wayar shi takalla tana sake dubawa tana ganin kamar hoton emaan take gani,da sauri ta fixge wayar tana kallon fuskar emaan tacikin wayar Sadeeq,cikeda tashin hankali kafafuwan fauxa suka fara rawa ta xube akasa tana fashewa da wani mahaukacin kuka,hannunta na rawa take sliding tana kallon pictures din emaan wanda baxasu lissafu ba,tana kallo tana kuka mai tsanani da taba xuciyar me sauraro,saide har lokacin takasa yadda da abinda idanunta ke gani,xuciyarta ta kasa gasgata hakan saboda tsananin tashin hankali,ta maimaita emaan acikin ranta yafi sau dubu saboda tsananin damuwa,tana kuka gumi na tsastsafo mata saboda tashin hankali,hotunan emaan kawai take kallo tana jin xuciyarta na xafi kamar xata tarwatse,runtse idanu tayi jiri na dibarta tana jin kamar xatayi pass out saboda matsananciyar damuwa,takasa thinking straight alokacin sai kawai ta baje awurin tana sake fashewa da kuka mai tsanani wanda yake fitowa daga kasan xuciyarta,emaan fa?pictures din emaan take gani awayar mijinta?ita ce tambayar data kasa amsawa,tana kuka ta shiga WhatsApp wurin chats din su da emaan,anan ne tayi Suman xaune tana jin kanta na spinning xuciyarta kamar ana buga mata ƙusoshi takeji,kasa karantawa tayi saboda tsananin damuwa ta jefar da wayar akasa tana jin wani xafi na rufe ta,kallon Sadeeq tayi dake kwance tana jin zuciyarta na suya,ta rasa kalmar da xata yi amfani tayi mishi magana,ji takeyi kamar xata shiɗe saboda bakin ciki da takaici,sai alokacin tafara hada bakin xaren,sai alokacin ta ke hada maganganun da alameen ke fada mata,auren emaan da yayi ne ya tabbatar mata da cewar tabbas emaan ce yarinyar da Sadeeq ke mutuwar so,emaan fa???wacce take sonta ta dauketa kamar kanwarta uwa daya uba daya,emaan fa?? wacce tasan komai nata tasan sirrinta,emaan fa ????wacce ta damka ma amanarta,ta aminta da ita fiyeda yadda ta aminta dasu inteesar,emaan fa?emaan fa?ta fada hakan da karfi tana sake fashewa da wani mahaukacin kuka,xuciyarta kamar ancinna mata wuta banda balbala ba abinda xuciyar ta keyi,ta dade tana kukan bakin ciki saide har lokacin Sadeeq bai motsa ba,hakan ne ya sake bata mata rai taji sadeeq yaxo mata wuya,afusace take tapping shoulders dinshi tace"meyasa xakamin haka sadeeq,meyasa ka xabi kaci amanata ta wannan hanyar?meyasa xaka min haka?dama emaan kake so?dama akan emaan ka shiga cikin gararin rayuwa?dama emaan ce ummul-abasin ciwonka?dama emaan is behind everything?meyasa xaka min haka?"tafada tana jijjiga shi tana kuka mai karfi da ciwo wanda yake fitowa daga kasan xuciyarta,saidai har lokacin sadeeq is not responding,haka ne yasa ta sake jijjiga shi tana fadin"answer me sadeeeq....."cak brain dinta ta tsaya tana kallon fuskar sadeeq wacce take dauke da murmushi asaman ta,gaban fauxa ne yayi mummunan faduwa,tace"sadeeq!,sadeeq!! Sadeeq!!! Pls open your eyes "tafada tana jijjiga shi da dukkan karfin da Allah ya bata,saidai har lokacin bai motsa ba,hannunta dake rawa ta dora akirjinshi daidai saitin xuciyarshi,tata xuciyar ce takusa bugawa saboda tsananin tashin hankali,mikewa tayi da sauri tana jin numfashi baya kaimata,sai ta sake fashewa da kuka tana cewa"pls sadeeq kar ka min haka,kada ka tafi ka bar ni..."tafada tana sulalewa kasa ta sume.....tunda su fauxa suka koma gida hankalin mami ya kasa kwanciya,ta kira wayar fauxa yafi akirga,haka wayar Sadeeq dake ta ringing agefen sadeeq da Fauxa,hakan ne yasa mami takira Nurain suka nufi gidan fauxa,ayau ne mami ta tarar da babban tashin hankali acikin rayuwarta,yadda jikin Sadeeq yayi ne yasa hawaye masu xafi suka xubo ma Nurain domin ya tabbatar sadeeq yayi tafiyar da babu dawowa,sadeeq ya tafi gidan shi da gaskiya,a asibiti suka sake tabbatar da rasuwar Sadeeq wacce ta gigita kowa,mami ta dafe kai cikeda damuwa tana fashewa da matsanancin kuka xuciyrta kamar xatayi bindiga,fauxa na kwance har lokacin bata farfado ba,dr ne yashigo ya samu mami dake dirxar kuka yace"kuyi hakuri,addua Sadeeq yake bukata,sannan fauxa na bukatar kulawa ahalin datake ciki".bakin mami na rawa tace"cikin ta fa?"sunkuyar da kai dr yayi yakasa ce mata komai saboda yadda yaga yanayinta ta mugun bashi tausayi,sai alokacin hajiyar Sadeeq da alhaji kabeer suka karaso asibitin suna kuka mai taba xuciyar me sauraro,anan suka sake tabbatar da sadeeq dinsu ya rasu,and there's nothing they can do about it,banda kuka ba abinda ke tashi acikin ward din...mutuwa kenan mai raba tsakani....!.

Zaynabyusuf✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now