"Umma,Aliyu ya tafi ko?".shiru tayi min tareda sunkuyar da kanta kasa,Alhaji ne yayi saurin mikewa zuwa gabana ya tsaya,yace"don't overthink,focus on getting better,komai zai Daidaita in shaa Allah".

Bakina Na rawa nace"Abba kaji abinda yafaru dani ko?".asanyaye ya daga kai sama sannan yace"I trust you Eman,zamuyi magana idan kin samu lafiya".Sosai naji sanyi araina,bance komai saboda shigowar da akayi,Da sauri umma ta mik'e ganin hajiya Maryam kanwar mahaifina,wacce ta zamar ma rayuwarta a living hell,Shigowar Babana ce ta kara daga mata hankali,domin tasan zuwansu bazai haifar da d'a mai ido ba.

Kallo d'aya zaka musu kasan masifa Na cinsu,babu b'ata lokaci hajiya mairo tace"miye na saurin mikewa?dodanni kika gani?bayan kin lalata rayuwar ki shine baki tsaya anan ba saida kika lalata ta Eman,dake da yarki kun jawo mana abin kunyah da gori da aibatawa adangi da gari baki daya,kun shafa wa kanku babban tab'o wanda baze tab'a goguwa ba musamman arayuwar Eman,yanzu wani mahaukacin ne zai auri eman saide d'an gaba da fatiha ko kuma d'an iska irinta me yawon bola,alokacin baya idan nayi magana ace Na fiye masifa bana sonki,aiga irinta nan".

Alhaji yace"Allah ya huci zuciyarki Mairo,amma wannan ba lokacin tattauna maganar bace dubaga Eman batada isasshiyar lafiya".

"Da yarka ce ai bazakace haka ba,shiyasa tun farko naso hanata zaman agolanci domin babu yadda zaka riketa daidai da 'ya'yanka,kun had'a baki da fatima kun cuceni,kuna ganin hakan zai illata rayuwata,ina me tabbatar muku kun tafka babban kuskure domin Na yanke duk wata alaka da Eman,taje can ta nemi wani uban baniba,koda wasa karki kuskura ki kara danganta ni da sunan mahaifinki,Na yanke duk wata alaqa tsakaninki da dangina gabadaya,tur da 'ya irin ki wallahi nayi danasani dakuma asarar haihuwarki ".cewar babana cikin kunar zuciyah.

Alhaji ne ya tari numfashin shi yace"haba Alhaji kabeer,kana cikin hankalin ka kuwa?baki kake mata fa,innalillahi wainna ilaihi raji'un,eman bata cancanci haka ba."
Turus umma tayi atsaye sai binsu takeyi da ido ta kasa furta koda kalma daya wacce zata kunce ta daga daurin zato.

Kuka mai sauti Na fashe dashi,I can't believe what's happening acikin rayuwata,
"Rufe mana baki munafuka kawai algunguma,kukan me zaki mana?"cewar Hjy mairo.

Babana ya cigaba da fadin"kamar yadda nafada kinemi wani uban bani ba,Na zare hannuna daga kanki,mairo zo mu tafi ".yana gama fadin haka suka fita,daga hjy kwaise har Alhaji bawanda ya iya cewa komai,balle umma datayi Suman tsaye,dama babana kadan yake jira ya cire ni daga sahun 'ya'yan shi,abin nema ne yasamu and i blame myself for everything,tabbas nina jama kaina.

Da hanzari Alhaji ya tare umma me shirin faduwa kasa,yayi mata kyakkyawan masauki a kirjin shi sannan ya zaunar da ita yana bata assurance,inde yana raye baze tab'a matsawa daga gefen ta ba,zai iya mata komai domin farin cikinta,haka ya rika lallashin ta kamar ya maidata ciki.

Washegari da safe dr Mansoor ya shigo ya k'ara dubani,lokacin Na fada can cikin kogin tunanin Aliyu,ina mamakin rashin dawowar shi gareni,dr Mansoor yace"yanzu zan sallameku in shaa Allah,saide ta kamu da high blood pressure,ku kiyaye shigarta cikin damuwa sannan tariqa shan magani bisa qa'ida".

Cikeda damuwa umma da Alhaji suka amsa da toh,already umma tagama hada mana kaya,hijab ta ajiye agefena,jiki ba kwari nasa muka fito daga cikin asibitin,a bayan mota na kwanta hawaye na zubo min,zan jure komai amma banda rashin Aliyu na,domin shine farin cikina.

tafiyar 30minutes ce takawo mu gida,ganin motoci da jikokin gidan ya tabbatar mini yau kowa ya hallara,kasancewar duk weekend haka gidan ke cika kamar gidan biki,gabana yayi mugun faduwa ina tunanin dawani ido zan kalli mutanen gidan,kunya da danasani suka dirar min alokaci daya,tabangaren  umma ma haka lamarin yake,saide babu yadda zamuyi muka shiga babban falon gida wanda kaf iyalan Alhaji ke ciki.

'Ya'yan hjy kwaise 10 cif,mata 5 maza biyar,aciki mata uku da maza biyu sunyi aure,babbar ciki Anty Fauza,sai Anty Mariya,Al'ameen ne Na uku,sai Suraj,Abba,Salim,Salima,Nurain,inteesar da Afnan...Alameen ne kawai bai samu zuwa ba.

'Yayan mummy 4 mata,biyu sunyi aure sauran 2,Afiya ce babba,sai Rafee'ah,Sadiya da Afeefa.

Sai 'ya'yan Mama 4,uku mata d'aya namiji,usman ne babba,sai sameeya,Ruqayya da Khairat. Sai 'ya'yan umma na biyar maza,sau biyu tana haihuwar twins,nafarko Amir da Sameer,na biyu Asad da areef sai autanta Musaddiq...

Alhaji Abdulhameed Abubakar Safana aka rubuta da ajami a daidai kofar shiga falon,falo ne mai girma Sosai wanda ya sha expensive Royal furnitures,wanda kallo daya zaka ma falon ka tabbatar ka shigo cikin gidan hamshakin mai kudi,wato multi millionaire.

Kamar tsohuwar munafuka Na tsaya cak akofar falon,I couldn't make another step,saida Alhaji ya yazo,hannuna ya riqe muka shiga falon umma na biye damu abaya,ya zaunar dani akasan kujerar daya zauna yana amsa gaisuwar 'yayan shi,suna gamawa ya sallami qananun yaranshi yana bin kowa da kallo,Anty fauza ce tafara yima umma jaje sannan gabadaya suka hada baki wurin jajanta mata,basu wani bi takaina ba,Salima ce kawai take bina da kallon tausayi.

Gyaran murya Alhaji yayi sannan yayi mana nasiha mai ratsa jiki,wacce tasani zubar da hawaye,ya karashe maganar yana fadin"ban amince wani ya aibata eman ba saboda abinda ya faru wanda har yanzu ban gamsu ta aikata ba,zanyi bincike kwarai har na gano gaskiyar lamari".

"Ai mai hali baya fasa halinsa,idan halinta ne dole zata cigaba,kaga alokacin dole ka dauki babban mataki akanta,dan bazamu zuba idanu ba ta gurb'ata mana tarbiyyar'ya'ya.ko kadan banji haushi ba saboda nasan komai ya faru nina jawa kaina,cikeda damuwa umma tace

"Ina me baku hakuri,nima banida niyyar eman ta cigaba da zama anan".

"Eman batada uban daya wuce ni,kamar yadda bazan iya canza alaqa ta dasu musaddiq ba ,haka wannan dalilin bazai sa Eman tabar gidana ba,this is my final decision,sannan ina me jaddadawa kowa kada Na karajin wannan maganar abakin kowa matukar bani nazo da ita ba".yana gama fadin haka ya miqe tsaye yana kallon yaran nashi sannan yace"hjy kwaise ayi musu gargadi,gudun fuskantar bacin raina".

Yauce rana tafarko da Alhaji ya bata maximum girmanta dakuma matsayin ta amma hakan bai mata dadi ba for the first time,saboda tsantsar son umma ne yasa yayi hakan,watau ta gargadi kowa,yarinya ta tafka iskancin ta sannan yace a gargadi matanshi da yaran shi,saboda umma,ta jinjina kai tana kallon umma,yayinda mummy tacika kamar zata fashe,ga mari ga tsinka jaka,ga magana amma babu damar magantuwa matukar ba hjy kwaise bace ta bada damar ayiba.

Jiki ba kwari Na shiga part din umma,ban tsaya koina ba sai bedroom dina,na kwanta kan italian bed dina sabbin hawaye na zubomin,wannan rayuwar na zab'arwa kaina,rayuwar kunci da bakin ciki,ga tunanin Aliyu dayake kokarin haukatani,I really want to talk to him,saide banida halin tambayar wayata dake wurin umma,ina tunanin halin dayake ciki,tabbas yana cikin tashin hankali,wannan tunanin ne ya kara daga min hankali,kamar ance na kalli gefen side drawer,idanuna suka sauka akan landline,da sauri naje nai dialling house number din su ina adduar Allah yasa shine zai daga ko wani daga cikin worker's din gidan.saide har tagama ring babu wanda yayi answering,banida yadda zanyi na Mike na shiga bathroom,alwala na yi jiki ba kwari nagabatar da sallar la'asar ina kuka,bana gajiya da kuka tun lokacin da abin yafaru.

Shigowar umma cikin dakin ce yasa na dago ina kallonta,daga tsayen tace min"Eman yanzu da lokacin baya ba daya bane,akwai banbanci,kada ki sa ran ganin daidai daga gareni domin baza ki ganshi ba,kin jawo mini abin kunyah acikin dangi da kishiyoyi wanda kad'an suke jira suyi yamad'id'i dani,dan haka expect the worse from me,zan miki gashin da gobe idan ance ki maimaita haka bazaki kara ba,ina mai tabbatar miki Na qara kamaki da irin wannan laifin saide ki nemi wata uwar bani  ba,idan duniya kike son shiga,tashi ki shigeta,ina me tabbatar miki ta isheki Riga da wando".

Har ta juya zata fita tace"gobe mahaifiyar Aliyu zatazo muji matsayar su akan aurenki".gabana ne yayi mummunan faduwa Na miqe tsaye babu shiri hawaye na zubo min...

EMAANWhere stories live. Discover now