Dawowar Alhaji da takeaways ne yasa umma ta kafeshi da idanu tana kallo,inde Alhaji Na kusa da ita bata bukatar Komai ta rasa ,yana sanin halin Datake ciki tun kafin ta fada mashi damuwarta,zama yayi yana cewa

"Nasan baki ci komai ba,ki daure kici wannan ko kya samu karfin jikinki".

"Thank you,jazakallahu bil jannah"umma tafada tana goge hawayen daya zubo mata.sakin baki hjy kwaise tayi tana kallon su cikeda b'acin rai mai tsanani,duk wanda yasan hjy kwaise yasan she's the jealous type from day one,shiyasa Alhaji ke takatsantsan da alamuran shi agaban ta,sedai duk da haka abinda yayi ya b'ata mata rai,wanda ya bayyana asaman fuskarta,tabbas umma so take ta kwace mata matsayin ta takarfin tsiya,abinda baze taba yiwuwa ba kenan!.
*****
Sosai mutane suka zagaye accident spot din suna jimamin yadda za'a ciro Na cikin motar,saboda yadda motar tayi kaca kaca bazaka ce za'a fitar da mai rai ba,Sosai kowa yayi mamaki sanda aka fito da Aliyu,he was standing on his feet,but looking devastated and hurt,gefen kanshi ne ke bleeding bayan haka he's perfectly fine,nearest pharmacy suka kaishi aka mishi dressing ciwon,Sosai yama mutanen godiya sannan yakira mechanic dinsu domin ya tafi da motar,bolt yayi domin baya son tayar wa mamanshi hankali ta waya,baida energy din convincing dinta that he's okay har sai ta ganshi,10 minutes drive ne yakaishi gidansu dake ahmadu bello way,kallo daya zaka mishi ka tabbatar yana cikin damuwa mai tsanani,he loved Eman with all his heart and soul,he loved everything about her,especially her flaws,amma wannan mistake din baze tab'a goguwa acikin zuciyar shi ba.

"Aliyu meya same ka?"hajiyar shi ta tambaya cikeda tashin hankali,yayar shi Anty Hind tayi saurin zaunar dashi tana kai glass cup saitin bakin shi mai cikeda ruwa mai sanyi,ba musu yasha ruwan yana kallon hajiyar su da jajayen idanunshi yace

"Abinda yafaru da Eman is true,she told me that herself,mommy I'm so disappointed,I feel betrayed and used".ajiyar zuciyah ta sauke sannan tace"abinda nake fada maka kenan,ba wai haka kawai ne banason eman ba,auren irin wannan nake guje maka,yanzu first thing first,what happened to your head?".

Murya adashe yace"I had an accident while coming back from the hospital ".da masifa mommy ke cewa"wannan Yarinya ta zamar min masifa arayuwar yarona,Allah ya cigaba da karemin kai,you just need to forget about her existence,stay far away from her,for the betterment of your life and future ".

Hawaye masu dumi Na zubo mishi yace"but how?taya zan iya mantawa da Eman?my very fiancée wacce sauran 2months bikinmu?".Anty Hind ce tayi saurin cewa"kada ku yanke hukunci cikin fushi,mommy ki barshi yayi wanka ya huta,akwai lokacin dayakamata ayi wannan maganar,but now isn't the right time ".

Cikeda b'acin rai mommy tabar falon,tana kissima yadda zata bullowa lamarin,domin bazata tab'a yadda Aliyu ya auri Eman ba saide bayan babu rai agangar jikinta.!

Bedroom dinshi ya shiga wanda yake cike da pictures din Eman,yana mata wani mahaukacin so wanda shi kanshi cannot explain,everything in his room is about Eman,komai Na Cikin bedroom dinshi is her choice hatta color din furniture's din shi are her favourite,meyasa zata mishi haka duk irin son dayake mata?ahankali ya runtse idanunshi yana fashewa da kuka Sosai,saida yayi mai isar shi sannan ya cire kayan jikinshi,hatta adduar shiga toilet reminds him of her,idan ya rufe idanun shi ita yake gani,she's always in his thoughts,always on his mind,tayaya zai iya rabuwa da eman?.

Few hours Later...

    Hawayene ke fitowa ta gefen idanun Eman,she was lost in thoughts,lost in the world of her own memories,ina ma she can went back in time and change everything,few hours ne suka wargaza mata rayuwa daga farin ciki zuwa bakin ciki da damuwa mai tsanani,wacce zata cigaba da bibiyarta mataki bayan mataki na rayuwa.ahankali na bud'e idona ina kallon umma da alhaji da hajiya wanda suke zaune can nesa dani,kowanne acikin su na cikin damuwa,ahankali na furta

EMAANWhere stories live. Discover now