91-100

116 6 4
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

    Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_

*BOOK ONE*

*PAGE 91-100*

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*NO EDITING❌*

_Ba damuwarka bace hawana online please malan I beg ka fita daga harkata_

kurama sakon nata ido yayi yana kallo.ya kuma maimaita karanta sakon nata yafi sau ba adadi,maimakon yaji haushin sakon nata sai yaji ya tsinci kanshi a cikin farinciki ya nemi fushi ya rasa.kalma Malan  ka fita daga harkata shine yafi bashi dariya ma,wai ya fita daga harkarta bayan kuma yanzun ya fara shiga harkar tata tunda dai ko tana so ko bata so shine dai zai zama mijin nata,yana cikin sake kallon sakon nata Moha ya shigo yana cewa.."ka tashi mu shiga cikin gida kasan su Mom sun dawo." Kallon Moha yayi kamar ba zai magana ba sai kuma yace.."Ina sane so nike sai su Dad sun shigo sannan dan akwai maganar da nike son nayi dasu."

"Wace magana kenan."?

Cewar Moha yana ajiye wayar hannunshi dan daman gama wayarshi kenan Zubaida ya shigo room din,dan  tabe baki yayi yana ajiye wayar tashi yace.."maganar wanann yarinyar mana." Murmushi Moha yayi yana cewa.."Broth wace yarinyar kuma." Harararshi yayi yana cewa.."ban sani ba please Moha wace yarinyar zan maka magana idan ba wanann marar kunyar yarinyar ba Zulaihat?dole nayi maganinta sai na koya mata hankali."

Fuuuu ya tashi ya shige toilet sai daure fuska yake,shi Moha murmushi yayi yana dage kafadunshi ya cigaba da wayarshi da Zubaida cikin so da kaunar juna,Koda Najib ya fito daga wanka direct gaban mirror ya nufa ya fara shiryawa kamar mace dan lotion din da yake using dasu wata macen ma bata dasu dan  sun kusa kai biyar banda cream kuma ko wane sai ya shafa da yake bai tara suma kasunbace kawai da gemu ya gyarasu ya shafa masu mai da yake using dasu.wardrobe yaje ya fiddo wani white yadi mai kyau da tamsi ya saka yasaka hula white da takalmi hadda agogonshi apple ce white mai kyau ya saka ya fashe jikanshi da turaruka masu kyau da tsada ya dauki wayoyinshi ya kalli Moha yace.

"Zaka iya tasowa mu tafi."

Murmushi yayi yana cewa.."Babe byee zamu shiga cikin gida love you muaahhhh." Murmushi Zubaida tayi tana ajiye wayar tana kallon Zulaihat tace.."Sis fatan kinyi ma Dr Najeeb ya gajiyar hanya ko."?tsaki tayi tana girgiza kai tace.."Banyi ba kuma ba zanyi ba,Kinga Sis pls ki daina yi man maganarshi dan bansan ji sam."

"Amman Sis a gaskiya baki kyauta ba kaso mai sonka fa." Tsaki tayi tana cewa.."ce maki yayi yana sona?yaushe yayi dake sona yake?tom bari kiji na lura kema ya sanyenki kamar yanda ya sanye Umma da kalaman banza da wofi irin nashi.Najeeb ba sona yake ba kamar yanda nima bansonshi kawai zai aureni ne saboda wata muguwar manufa tashi nima kuma na shirya bi dashi da yanda yazo haka zan ansheshi."

Dafata Zubaida tayi tana cewa.."wallahi Sis Dr Najeeb yana sonki yana balain sonki so sosai ma tun kafin ya furta maki nasan da haka,kin manta number da ke maki text a da HA shin kin taba zaunawa kiyi tunanin waye HA kuwa Sis."?

"Bazanyi ba.ya kamata ki sani Sis banda lokacin tsayawa tunanin waye wani HA.ina hama da karatu ban damu da nasan waye shi ba dan ba matsala ta bace."murmushi Zubaida tayi tana cewa.."wai Sis yaushe kika zama haka?kamar ba ke ba." Turo baki kawai tayi bata sake cewa komai ba sai  goge hawaye da ta kamayi dan zuciyarta zafi take mata sosai idan aka anbaci Najeeb a gabanta.(nidai nace Zulaihat ayi dai a sannu fah ahtoh lol🥂)

★★★

Ko wane part sun shiga sun gaida iyayen nasu sannan suka wuce part din Hajja dan sunsan a can ne zasu tadda su Dad a wajen Hajja dan acen suke firar dare.duk ranar duniya da sallama dauke a bakinsu suka shiga zaka samu waje a kasan carpet suka zauna suka mika gaisuwa a wajen su Abbu sannan suka kalli Hajja Najeeb ya fara gaisheta ,tsaki Hajja tayi tana cewa."Dan Ubanka ba zan ansa ba,ka gama yi man tsakin dazun shine yanzun dan kaga su Hamisu shine zaka wani gaisheni kamar na kirki?daman zama.jiranka nike wallahi yau sai naci ubanka Hamisu gashi nan zaune a gabana." Fashewa tayi da kuka tana face mijina ta nuna Dady ta cigaba da cewa.."Kai Hamisu kayi ma danka magana idan kuma ba haka ni zan tashi na bar maku gidanku na koma asalina daman Ina zaman zamana a wudil kuka daukoni kuka maidoni nan.dan kawai yaranku su ringa yi man rashin kunya da tabbata bayan ni na haifeku da ban haifeku ba ai ba zaku haifesu ba."

DA'IMAN ABADAN Where stories live. Discover now