13&20

67 4 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

    Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_

*BOOK ONE*

*Wannan page din naki ne Pharteemarh kankia much luv🥰*

*PAGE 13&20*

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

"Zaku shigo mu tafi ko sai na fito na balballaku."? Cikin tsawa ya ida maganar da sauri Zulaihat ta toshe kunnenta har rige rigen bude motor suke dan shiga da sauri Zubaida ta bude baya ta riga Zulaihat shiga tana lumshe idonta gami da sauke ajiyar zuciya. dan ta tsorota sosai da tsawa da ya daka masu,ita kuwa Zulaihat tsaye tayi bakin motor tana share hawaye ,kallonta yayi ya girgiza kai yana sakin karamin tsaki zuge glass din yayi yana wulla mata harara cikin masifa da tsare fuska yace..." Mudun na sake magana akan ki shigo wallahi ranki sai ya b'aci zaki shigo ko kuwa."?

Kuka ta fashe dashi tana balle murfin motor ta shiga gaban da bata bukatar shigar ko kulle marfin batayi ba ta daura kanta bisa cinya tana kukanta,tsaki yayi yana kulle motor da kan shi gami da bissmillah yayi ma mota key suka tafi shuru kake jin motar ba abunda ke tashi sai sautin kukan Zulaihat.

Har cikin kasan zuciyarshi haka yake jin saukar kukan nata,ji yake kamar ana yankar mashi naman jikinshi tsabar yanda yake jin rad'adin kukan a cikin jini da bargo,da karfi ya rintse idonshi yana kaima sitirarin motor duka gami da danna giyar motor ji kake k'iiiiiiii haka sound din ya fita, salati Zulaihat tayi tana fadawa jikinshi gami da makalkaleshi tana rushewa da wani sabon kuka,zuciyarta da sauri sauri take bugawa fat fat haka sautin bugawar zuciyar yake fitowa,rintse idonshi yayi yana sauraren yanda zuciyar tata take bugawa sai da ya bata kamar 5min sannan ya tureta daga jikinshi yana  balla mata kallon banza natsuwa tayi tana kama bakinta da ke rawar kuka,tsaki yaja mai tsawo yana kallon ta fuskar nan babu annurin murmushi a saman yace.

"Na sake jin koda tarinki sai nayi ball dake ,na kasheki da maruka tunda  baki da hankali har yanzun idoit." Rintse idonta tayi da karfi tana budesu gami da goge hawayen da suke zuba bisa fuskarta, tabbas taji ciwon zagin da yayi mata ta rasa mai tayi mashi har haka ya tsaneta?bata da ansa sai kawai ta kalle gefe tana sauke ajiyar zuciya gami da goge hawaye a zahiri tayi shuru kamar yanda ya  bukata din,amman zuciyarta taki tayi shuru sai tafasa take tana zubda hawaye sake yi ma motar key yayi suka dauki hanya.bai sake kallon idan take ba har sai da ya iso har kofar gidansu yayi parking sannan ya kalleta.

Itama kallonshi take da idanuwanta da sukayi luhuluhu sun sha kuka, sai ta kara mashi kyau ma,ita kuwa mamaki ne fal a zuciyarta taya hakan ta faru?ya akayi yasan gidansu?fuskarta kasa boye mamakinta tayi sai dai kash tasan ko giyar wake tasha bata isa tayi mashi wannan tambayar ba.ai wasa ma waje gareshi ita a rayuwarta batason taga abunda zai hadasu koda na second d'aya ne.maganar Zubaida ce ta dawo daga ita daga duniyar tunanin da ta tafi...da sauri tabi Zubaida da kallo da har ta kusa shiga gida,sauke ajiyar zuciya tayi tana mai kokarin bude motar itama ta shiga gida, sai dai taji motar a lock take. waigowa tayi tana kallonshi hawayen dai basu daina zubowa ba,so take ta samu ta fita ta shiga gida ko ta samu yin kukanta yanda take so ko zataji sausaucin a zuciyarta.

Girgiza kai yayi gami da kafe ta idonunshi masu sata gigicewa da shiga taitaiyinta a take kuwa,kallonta yake kamar ya samu TV haka yake kallonta kuma yana mamakin yanda take maida kuka abokin hirarta ace ita bata da aiki sai na kuka,ko gajiya batayi idan bata gajiya ai ta rage kodan lafiyarta dan ai ciwon kai ba kanwar uwa bane balle tace,lumshe idonshi yayi yana budewa yace.

"Sannu da aiki."

Dan shuru yayi yana dauko mata wani farin handkerchief sai kamshi mai dadi yake,  ya bata babu wasa a fuskarshi yace mata.."maza goge wannan sakarcin  banzan a fuskarki tun ban karyaki anan ba."ansa tayi tana goge hawayen sai da ta gogesu tas sannan ta mik'a mashi tana maida kanta kasa dan a takure take sosai da sosai, ansa yayi yana dan sakin tsaki yace.."kuka kuma ba zan hanaki yi ba, idan kin shiga gida ki cigaba daga inda kika tsaya ni nasan abunda zan maki gobe a school fita ki ban waje."

DA'IMAN ABADAN Where stories live. Discover now