9&13

73 4 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

    Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_

*Wannan page din naku ne Aunty Binta Abbale da Adda maidambu  much luv🥰*

*BOOK ONE*

*PAGE 09&12*

Rintse Idanu tayi da taji ance.."yes come in." Da karfi ta rintse idanunta tana share hawayen da suke zarya a bisa kuncinta,dakewa tayi tana mai tura Office din a hankali ta bude k'aramin bakinta cikin muryarta mai sanyi da dadin saurare tayi assalama tana mai ida tura kanta a cikin office .

Aikinshi ya cigaba da yi bai nuna yasan da shigowar mutun a cikin Office din ba,cigaba da hidimar gabanshi kawai yayi.dan ko kallon kofar baiyi ba balle ya motsa yayi ma wanda ya shigo magana,duk da kuwa yasan wacece sai dai mai a halin da yake ciki baya da lokacinta.

Ta kusa Shafe minti 20 tana tsaye a wajen ko kallon inda take baiyi ba,duk'ewa tayi wajen tana mai rushewa da wani uban kuka dan d'aura hannu tayi akai  ta cigaba da kukanta,dan karamin tsaki yayi yana mai d'ago kanshi daga kan aikin da yake ya daurasu a kanta tsaki yayi yana girgiza kai sannan yace.

"maza tashi kibar man Office useless."

D'ago raunannun idanuwanta tayi tana saukewa a kanshi gami da had'e hannunta wajen daya bakinta na karkarwa cikin dutsewar murya saboda da kukanta da tasha tace.

"so..r.ry..sir."

Da in'ina ta ida maganar share hawayenta tayi da gefen hannunta ta cigaba da cewa..."wallahi ba laifi na bane matsalar abun hawa na samu kuma Umma ce tace dole sai na sha koda tea ne sune sukasa ka rigani zuwa." Ta ida maganar tana mai cigaba da sauke ajiyar zuciya kanta kasa,tsab ya k'arema Zulaihat kallo duk da ita ba fara bace  sosai amman ba ankirata da bak'a ba kuma ba za'a ce mata chocolate color ba ita dai wata kalar fata Allah ya wadata da ita mai shek'i da daukar hankali,ga baiwar hanci da Allah ya wadata da shi ga idanu dai dai dan ba'acewa tana da lulu eyes dan kuwa ba'a cewa tana da kananun idanu sai dai sexy eyes ,da dan karamin bakinta, sauke ajiyar zuciya yayi yana furzar da iska mai zafi a bakinshi gami da tura hannunshi cikin lunlunsar sumarshi da tasha gyara dan kallo daya zakayi ma sumar kasan ana zuba kudi a saman ta.

         Da hannun yayi mata nuni yana cewa..."maza taso ki zauna."ya ida maganar yana nuna mata sit,tashi tayi ta dawo inda ya umirceta ta zauna kanta k'asa tana wasa da yatsun hannunta hawaye kuwa sai tarara suke kamar an kunna famfo haka suke shatata,girgiza kai yayi yana cewa.

"Hala kuka baya saki ciwon kai ko?Zulaihat."

D'ago kai tayi sake da baki tana kallonshi dan kuwa mamakine fal a ranta, taya akayi yasan sunanta? lura da mamakin da ke rainta  sai ya tab'e baki ya cigaba da cewa.

"maiyasa kike son wasa da karatunki."

Runtse ido tayi tana mai Jin ciwo furincinshi a kanta wai tana wasa da karatunta,bayan sau daya tayi late har suka samu wannan sabani kuma a course din shine kawai take da problem duk da kuwa tafi maida hankalinta 100% a kan ko wani course da take yi kuma shine yake kadata.

Share hawaye kawai tayi ga gaskiya amman bata faduwa k'irik'iri,amman sai dai ido kawai shine nata tana ji tana gani ana neman lik'a mata sheri,maganar da yayi ce ta dawo da ita daga duniyar mamaki tana cewa.."Sir kayi hakuri akasi ne a kasamu."

D'ago kanshi yayi yana cewa.."kinji ko?baki dauki karatunki da muhimmanci ba tunda har ake samun abun da zai sa ya samu targard'a." Amman Sir sai...daura hannunshi yayi bisa bakinshi yana cewa..

"ya rage naki Zulaihat ki chanza ko karki chanza course dina  70mark ya kasance lower mark ne zaki samu. wanda maybe nayi maki favour akan haka,karki kuskura naga result dinki kasa ga 70 duka course din da kike,zuwa school akan lokaci ya zama dole.maza tashi ki barman office."

DA'IMAN ABADAN Where stories live. Discover now