7&8

97 4 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

    Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_

*BOOK ONE*

*PAGE 07&08*

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*Inajin dadin comment dinku sosai d sosai yana sani farinciki much luv🌹*

Idanunsu sarkewa sukayi da juna suna kallon-kallon,Beauter tayi saurin sauke kanta kasa zuciyarta na bugawa da karfi da karfi dan tunda take a rayuwarta bata taba ganin kyawkyawan namij mai kwarjini da haiba irin A-Kaɗir ba,sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa..."Sorry." gaba tayi da sauri bata tsaya taji abunda zaice ba,duk da tarin barnar da tayi mashi,binta yayi da ido yana mamakin wannan wata irin yarinyarce?anya kuwa tana da cikaken hankali? dukawa yayi ya dauki Sim card dinshi ya kama gabanshi zuciyarshi fal da tunanin wacece ita?anya ma musulmace duba da irin shigar dake jikinta bata da banbancin da akirata tsirara,rintse idonshi yayi yana dafe kanshi wani bakin ciki na taso mai,da zuciyarshi ta hasko mashi breast dinta da suke tsaye a cikin rigarta da ko arzikin breziya bata sa masu ba,kuma tsaye suke a cikin net din rigar dan rigar gabanta net ne shiyasa suke waje kowa yana gani,iska ya kaima nushi yana cewa.

"Astagafirullah." dan tunda uwar da ta haifeshi bai taba ganin tsiraici ba sai yau,ji yayi bai iya tafiya har sai ya gano inane gidansu sannan wani addini take,idan har kuwa musulmace to tabbas taci amanar musulcin dan kuwa addininta bai koya mata irin wannan shigar ba ta banza,Allah kadan yasan adadin mazan da zata jefa ga halaka masu raunin zuciya mundun ta cigaba da irin wannan kazamar shigar koda kuwa kiristen ce.

Ya kusa daukar minti arba'in zaune a cikin mota yana jiran fitowar Beauter,kamar ance waiga ya ganta rungume jikin wani kato suna tsotsar bakin juna sai wani shafata yake,ita kuma ta narke mashi sai tura hannunta take cikin sumarshi tana sosawa,a tsakiyar gari ba ko kunya take ji yanayinshi ya fara sauyawa sakamakon gamon da yayi sitarin motar ya kaima bugu yana cewa da karfi...."Auzubillahi minas'sheɗanar rajin ya Allah ka shirremu baki daya." sun kusa minti goma suna laluben juna ita da saurayinta sannan ya rakota har bakin mota ya bude mata ta shiga bayan kudin da ya ajiye mata da wani abu cikin leda wanda baisan ko maiye ba,ready shima yayi ya tada motar 5min ya bata sannan ya fara bin bayanta cikin wayau da dubara yanda duk tsiyarta ba zata gane ana bin bayanta ba.

*NIGERIA🥀*

_Kano_

"Ki kula da kanki." ta maimaita karanta text din bata san sau nawa ba,mamaki fal a zuciyata kallon Zubaida tayi tana miƙa mata wayar,kallon Zulaihat tayi tana cewa.."waye wannan kuma." girgiza kai tayi tana sauke ajiyar zuciya tace."nima bansani ba." kwantawa tayi tana dafe kanta dan wani irin ciwo yake mata kamar zai tarwatse mata haka take ji,ko motsi mai karfi bata son tayi dan gani take kamar kan nata zai tarwatse tsabar bala'i kwantawa tayi kawai tana lumshe idonta.

"Sis ko ki kira number kiji waye."? Girgiza kai tayi a hankali tayi magana tace.."A'a Sis,ki saman number ma a blacklist." zaro ido Zubaida tayi tana cewa...."Ayya Sis ba kyau aikata haka fa,ki kasan ko dashi za'ayi." tsaki kawai tayi bata sake ce mata komai ba,adduar bacci tayi kawai.

Dariya Zubaida tayi tana duba lokaci tace. "Banda ansa kenan?and tun yanzun zakiyi bacci ko ten batayi ba,kuma sai 12pm muke da lecture fa." waigowa tayi tana kallonta tace.."har kin manta da neman da Dr yake man ko."?murmushi kawai Zubaida tayi bata sake cewa komai ba,ta cigaba da danna wayarta.

       ★★★

Ajiye wayar hannunshi yayi yana murmushi ya kalli Moha yace..."Yarinyar tana bani tausayi sosai,gashi kuma tsoranta na burgeni sosai." Dariya Dr Moha yayi yana cewa."ina ruwan Zulaihat,ai na lura matsoraciya ce aiki ya ganka Najeeb." harararshi yayi yana cewa..."aiki kuma?kamar ya aiki ya ganni."?

DA'IMAN ABADAN Where stories live. Discover now