Jinjina kan sa Abba yayi yana addu'a ƙara mata lafiya, sannan suka gaisa da Aliyu.

Sajjad yace, "Yaya Aliyu yanzu sai da ka fito kana fama da jikin ka?

"Uhmm".

Kawai yace masa, ganin haka yasa Sajjad jan bakin sa ya tsuke sai kuma sauran suma suka ƙarasa shigowa daman suna waje,  Abba ya tashi ya fice, Sajjad ya biyo shi a baya har wajen motar sa, za'a buɗe masa Sajjad yayi saurin buɗe masa yana riƙe ƙofar. A wani zafafe Abba ya ɗaga hannu zai wanke shi da mari, ya tsaya kawai shi be mare shi ba shi be ɗauke hannun sa ba, yayin da Sajjad ya runtse idan sa yana jiran saukar mari a fuskar sa. Jin shiru yasa shi buɗe idan yana kallan Abba da ya sauke hannunsa ya goya ya shi a baya. Ya masa wani irin kallo da sauri Sajjad ya sunkuyar da kan sa ƙasa.

"Kayi dai-dai kenan?

"Na'am?

"Nace kayi dai-dai kenan?

Girgiza kan sa alamar a'a, kafin ya taho da sauri ya tsugunna a gaban ya riƙe kafar sa gam gam.

Yace, "Abba Dan Allah kayi haƙuri bana san abinne ya shafi buɗe asibitin Daada kuma kaga abubuwa dayawa suna faru shi yasa ban sanar da kowa ba, suma da suka sanar da kai dan sunga gida na ne a buɗe shine suka zo, amma Abba ba wai ba zan sanar sa ku bane, Abba idan baku sani ba waye zai sani Abba. Abba na roƙe ka kayi haƙuri".

Ya rasa ya zai yi da soyayyar da yake yiwa Sajjad, wannan soyayya yasan da cewa daga Allah ne, ba wai yin sa bane ko da wayon sa, Allah ta taimake shi baya da ɗan da yake hassada da kuma ƙyashin fifita soyayyar da yake yiwa wannan yaro. Mai ya kamata yayi wa Allah idan ba godiya ba? Wannan kallan da yayi masa kawai yaga nadama da kuma ban haƙurin abinda ya aikata, to me zai sa ya hukunta shi?

Ɗago shi Abba yayi, kawai ya rungume shi, shima Sajjad rungumo shi yana sakin wata irin ajiyar zuciyar da Abba sai da yaji ta. Sun jima a haka kafin Abba ya kama fuskar sa kamar wani ƙaramin yaro, yara abinda zai ce masa yayi.

Yace, "Ina san ka ɗa na. Ina matuƙar ƙaunar ka, kaji ko?

"Nima ina san ka Abba".

Ya faɗa yana rungume shi jikin sa.

"Ina san ku yarana kun ji ko?

Daada ya faɗawa su Hafiz da suke bayan su, suna kallan su kawai. Abba ne ya sake shi ya juyo ya kalle su sannan ya bubbuga kafaɗar Sajjad ya shiga mota.

Hafiz yace, "Daada faɗa musu de, muma muna da masu san mu, mai tsaya mana a koda yaushe".

Sajjad yace, "Ai sai da kuka bari Abba ya tafi sannan zaku wani ce waye waye waye".

Girgiza kai kawai sukayi alamar Allah ya shirya, sannan suka masa sallama suka wuce. Sai dare za su su ɗauki matan su, su tafi. Koda ya koma ɗakin a ciki yake sosai kuma hakan be hana shi tsallakewa ya hau kan gadan da matar sa take ba, duk da gadan akwai mutane shima, aka ɗaura hirar dashi daga inda aka tsaya babu wanda yace da shi uffan sai ma Bintu sa tayi masa magana ya zabga mata harara.

Mama ce ta fito daga toilet ta ganshi, akan gado.

Tace, "Sajjad tashi ka fita, bana cikin da rashin kunya. Fitaaaa naceeee".

Yatsine fuska yayi ƙasa ƙasa. Yace, "Ita Mama sai faɗa". Ya faɗa yana dirowa daga kan gadon, ya fice. Bata kuma haƙura ba sai da ta bishi da faɗan.

******

Washegari aka sallame ta suka dawo gida, can gidan su aka wuce da ita, a ɗakin Ummi ake ajje ta, sosai ake nuna mata gata, taga yaran ta, yarda suka sauya sosai kamar ba su ba, haka ma Sultan shima yayi haske da shi na sauyi yana yi, ya zaman ɗan ɓulbul dashi, ranar a wajen ta suka kwana dan sunyi kewar ta itama kuma tayi kewar ta su. Washegari sai ga su Baba garko sun zo dubiya hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata, kwanan su ɗaya suka juya.  Gata kam tana shan shi, a wajen wannan mutanen, shin me zata ce musu ita kam. Tun bata sakewa idan sun kirata da Yaya Nilah har ta zo ta saba, dan kullum suna gidan, yaran ma idan an ɗauko daga makaranta nan ake kawo su, Mama ce daman sarkin faɗan gidan ita ke saita yaran idan suna rashin ji.  Ranar da ta cika sati biyu kuwa sai ga su Ruƙayya sun zo suma, ba karamin daɗi abin yayi mata, suma sun koma gida amma kuma Baban Abdallah ya sai musu gida a Kano dan haka yace babu inda zai je, shima sana'ar sa ta kafu, yana so ya gina kan sa ne. Bayan korar da aka musu daga gida ma ta ishe su. Abdallah a ranar ya koma ita kuwa Ruƙayya sai da tayi kwana biyu ta koma tare da Sultan, wanda yayi matuƙar sabo da dukan yaran gidan.

*****

"Ni gaskiya nagaji a bani Matata na tafi da ita, wata nawa dan Allah?

Al-ameen yace, "Wacce matar za'a baka? Da bata da lafiya?

Sajjad yace, "Ta warke, wata uku fa".

Al-ameen yace, "Nima nagaji wallahi, abu yaƙi ci yaƙi cinyewa wata uku fa, wallahi Sajjad mun yi ƙoƙari".

Sajjad yace, "Kokari ɗaya ma, ni Abba zan je na samu".

"Kai da kake da Abban kenan".

"Kai ba zaka iya ba?

"Ba zan iya ba, ranar da ta ga ya dace ta dawo. Nagaji da zuwa weekend ɗin nan kuma. Daman ga mai gayyato ni nan".

Al-ameen ya faɗa yana nuna Aliyu dake danna system ɗin shi, kamar baya jin su.

Sajjad yace, "Zuwa zakayi wajen Baban ta".

"Haba Sajjad, ai ba zan iya ba".

"Toh".

Sajjad yace ya tashi ya fice, be zar ce ko ina ba sai gidan su Unaisa dake weekend ne, Baban su yana nan be fita ba a compound ɗin gidan ma ya gan shi, suka gaisa sosai, dan Baba yasan Sajjad a wajen Abba tun kafin ya gan shi, tun kafin su haɗu. Sajjad kuwa kan sa tsaye babu wata nuƙu-nuƙu tunda shi ba sirikin sa bane ba.

Yace, "Har yanzu Anty Unaisa fa Baba bata koma ba ɗakin ta ba". 

Baba yace, "Yau yau ɗin nan zata koma in Sha Allah. Kaji ko? Ina Al-ameen ɗin".

"Yana can Abuja, nima jiya na dawo, naga ashe bata koma ba".

"Allah sarki. In Sha Allah zata koma".

"Zan koma Baba sai anjima a huta lafiya".

"Ka gaida Abban naka".

"In Sha Allah zai ji".

Daga haka ya fita daga gidan, daman a waje yayi parking motar sa ya koma. Gidan su ya wuce da tunda abin nan ya faru be ƙara zuwa ba sai yanzu. Gyara gidan yayi sosai  ya fesa fresheners masu ƙamshi da ya tsaya ya siyo. Sannan yayi wanka a gurguje ganin magriba tayi, ya wuce Masallaci.....



A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now