39

63 1 0
                                    

Sun  dawo daga sallahr Isha kenan lokacin likitan na fitowa inda aka kwantar da ita, kafin sauran nurses ɗin harma da wasu doctors suka fito suma kowa jikin sa a sanyaye, yayin da matan suke a zaune fitowar su yasa su tashi tsaye sai dai kuma ganin irin expression ma fuskokin su yasa kowa jikin sa yayi wani irin sanyi ƙalau dashi dan shi Daada faɗuwa ya so yi Abba da Baba sukayi saurin taro shi. Dakyar ɗaya daga cikin doctors ɗin dan sauran suna fitowa daga ya kalle su sai kawai yayi saurin barin wajen, shi kaɗai ya iya ƙarfin halin jira dan sanar da su. ya iya faɗar"we lost her". Shima da sauri ya raɓa ta gefen su ya wuce ƙwalla na cika idan sa, shima kenan. Bare kuma familyn.

Kowa tsayawa yayi a inda yake babu wanda ya iya koda motsi ne a cikin su bare kuma wanda za'a iya samu ya yayi magana. Baba ne ya fara sakin kuka, wanda hakan yayi sanadiyar da yasa duka a halin sakin kuka, yayin da Daada da suka zaunar da shi yake kallan gefe guda kawai, shi de gashi nan kamar be ji me aka ce ba, kafin ya ɗago ya kalle su, hatta Abba shima goge hawayen yake a fakaice. Ɗaya bayan ɗaya take bin su da kallo har idan sa ya sauka akan Barrister ya ƙura mata ido yana tuno kalaman Anty, ba yau ta fara masa huɗubar da ya aure ta ba. Kusan kullum sai tayi masa wannan huɗubar tana yawan cewa. "Tana da kirki" "halin ƙwarai ne da ita" "bata da damuwar komai" "ta kasance tana ƙaunata a yarda nake ɗin nan" ire-iren maganar nan da take masa ne suke dawo masa tamkar yanzu ne take faɗar su, har sanda aka kawo yau da tace ya aure ta. Ajiyar zuciya ya sauke kafin wani irin hawaye mai zafin gaske ya zubo a fuskar sa, wanda hakan yasa shi jin nutsuwa da kuma salama ta ziyarce shi. Yasan ba yanzu zai yi kuka ba. Yasan kukan sa ba zai taɓa ƙare wa ba har abadan abada, yasan da cewa a yanzu kawai zai ke rayuwa ne ba tare ta san me yake yi ba. Sai dai ba zai bari a yanzu hakan yayi tasiri a zuciyar sa ba,bare suke masa kallan abin tausayi daga shi har Sajjad, ba zai taɓa bari ayi musu kallan abin tausayawaba.

Hakan yasa shi tashi cike da dauriya gami da jarunta ya nufi ɗakin da take ciki. Tana kwance kamar mai bacci, haka suma sauran suka shigo suka same shi, suka cika dakin kafin ya juya ta barsu a dakin ya fita domin a sallame su, su tafi gida. Ba ƙaramin jarumta da dauriya ya aro ba wajen kama kan sa da lallashin su daƙyar ya samu suka dena kuka. Yasan da Baba be fara kuka ba, da wuya a samu mazan sun yi kuka amma ganin Baba na kuka yasa gaba ɗayan su suma suka sa kuka.

****

Bata samu ta koma baccin ba, kawai kallan shi tayi ta yi yana baccin sa hankali kwance daga ta motsa zai sake riƙe ta gam, ganin lokacin magriba yayi yasa ta dole tashin sa, suka wanka sannan sukayi sallah, kayan sa ya zura.

Yace, "Bari na fita".

Hannun sa ta riƙe, hakan yasa shi juyowa yana kallan ta.

"Me ya faru?

Yana dawowa da zama kusa da ita.

"Kai zan yiwa wannan tambayar ai".

Ɗan murmurshi yayi yana pecking hannun ta.

Yace, "Wani iri kawai nakeji na gani nan de".

"Ba abinda yake damun ka?

Ta faɗa cike da kulawa. Ɗan hararan ta yayi.

Yace, "Bansani ba".

Murmurshi tayi masa sannan ya tashi ya fita ita kuma tana nan zaune kafin ta tashi itama domin fita, suka yi kiciɓus da su Aisha da ita da yaran sa Sadiya.

"Amarya Amarya".

Sadiya ta faɗa suna wuce ta tare da shiga parlourn. Ɗan murmurshi kawai tayi kawai tana girgiza kan ta.

Tace, "Sadiya wallahi bansan yaushe kika ɓaci da magana ba haka".

"Na ɓaci da magana ko kika ɓaci".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now