CHAPTER 2

917 84 4
                                    

TAMBARIN SHAHARA..🌹(FREE BOOK)
  
          CHAPTER 002
Mai_Dambu
#undertheinfluence
    
   Babu abin da yake bashi mamaki kamar duk abin da yake kewaye da shi, baya fada yana so sai dai a bashi, shi bai da zab'in kan shi, kome da aka san zai so kawo mishi ake, yawan damuwa da shiga kadaici yasa shi fara shan taba, a boye ba tare da kowa ya sani ba, sai dai kash wacce irin duniya ce yake rayuwa da komi kashin motsinsa akan idanun su yake, domin ya fara da idan su Abraham suka sha suka kashe zai dauka ya shiga ban daki ya kunna ya shaki hayakin sai ya fahimci ai yana bukatar sha domin samu abokin hira.  Abu ne da an rigada an shirya, shi kuma taba wani banzan abu ne idan kasha sai ta bayyana kanta. Da haka aka fara kawo mishi Davidoff grand Cigar, wanda a kalla kudin shi nera dubu arba'in ne, Por larranga Galanes Cigar, wanda shi kudin shi ya haura 114k, domin sigari ce da matukar ba jan wuya bane kai baka isa shansa ba. Balle shi da yake King Ajwaad.

        Wata biyu da rasuwar mahaifinsa, aka fara shirin su fara exam wanda a lokacin har jarabawar kawo mishi aka yi, domin ba a son ya bawa kan shi wahala, amma da yake yana da burin zama likita a rayuwar shi yaki yarda da haka, da kansa yayi jarabawar shi. Bayan sun gama suka dawo gida.
   Swan town.
Unguwa ce da take bakin teku, sannan an kawata unguwar da wasu agwagin swan da kullum suke shawagi a saman tekun,
Da safe da kuma maraici, mansion din shi tana kallon tekun, duk wani jin dadi da farantawa an bawa Ajwaad, sai dai ya kasance cikin rashin farin ciki, kullum fuksar shi kamar ta shanuwa, koda yake basu da wani zuri'a domin babu me zuwa wurin shi as family uwa ko na Uba, shi daya yake rayuwar shi bai da kowa sai Allah, kadaici yasa shi tashi da wani irin kangararren hali, haka yasa members na tambarin shahara suke tsammanin ai dan yana under control din su ne, watan su uku a gida sakamakon ya fito, da farko sun so tura shi ya karanci kasuwanci ne, sai yaron nan ya kafe lallai shi likitanci yake son karantawa, abin ya basu haushi. Amma babu halin fusata kuma babu yadda suka iya da shi.
    Da wannan abin suka fara tunanin nima mishi makaranta anan Mafia City. Amma dan banza yayi tsalle yace shi kasar waje zai tafi karatu. A lokacin da maganar ya isa gaban members na tambarin shahara, shiru suka yi suna kallon Mr Paul.
Mr Charles ya ce.
"Yanzu yaron nan shi yake juyawa mu fa, uban shi mun sha dakyar a hannun shi, ace shima juya mu yake?"
     Mr Barraq yayi kwafa yana kallon Mr Gayu, da Allah bai saka mishi takurawa kan shi akan Ajwaad ba ya ce.
"Gayu meye nufinka? Kasan da Yarona Adil kuka bawa matsayin nan."
"Ai kuwa da kome ya rushe, kai bari kaji ko mutuwa da zata yi shawara dani na rantse da Allah ba zan barta ta dauki Rayuwar Ajwaad Imran Nasara ba, ka fahimta? Tow wannan Yaron al'amarinsa sai shi. Matukar zai tsaya a side din mu, I don't care da duk abin da ya zab'awa akan shi, burina TAMBARIN SHAHARA ta shahara a Duniya baki daya don Allah Yaro ya ce abin da yake so a bar shi yayi yadda yake so, dukkan ku waye bai kawo project an saka mishi hannu ba, ko wanen ku an mishi yadda yake su, sai me?" Mr Paul ya faɗa.
"Ka dai san halin sa, da Uban shi daya."
"Yes like Father like Son, so kar na kuma jin wani abu daga baya idan ba haka ba, zan dauki mataki."
        Da wannan suka kashe bakin al'amarin, bayan wasu kwanaki aka tura Ajwaad da abokan shi biyu Harved University, United State, su kuma suka cigaba da ruined din kungiyar su kamar yadda suke su.
         Amma duk inda yake ana tura mishi sakon saka hannu, domin cigabar ƙungiyar su. Kuma yana saka musu kawai dai sai dai idan bai samu sakon ba. A hankali yake karatun shi, gashi shekaru na kara zuwa gogewa da nutsuwa tare da wayewa yana kara shigar shi ta kowani side, yaki yarda ya zauna da kudin da kungiyar take spent din shi akan shi, tsabar kokarin niman na kansa. A lokacin da ya cika dan shekaru ashirin da biyar a duniya, ya goge fatar shi tayi kyau dama gashi uwar shi yar asalin ƙasar algeria ce, mahaifin shi ne dan kasar jamhuriyyar arewacin Afirka,  sai fatar shi ta zama wata irin vibes, shi ba fari can ba kuma shi ba baki ba. Amma duk inda ya shiga yana hada yan mata, domin fada ake a kansa,  babu abin da yake kara firgita yan mata suke fadawa kansa kamar fitanannen idanun sa, da matukar ya kalli mace sai ta kusan haukacewa.
              Apartment din su daga shi sai abokan shi, har yau ba zasu ce ga abin da yafi so a rayuwar shi ba, yana da shekaru ashirin da shida ya haɗa master din shi, a lokacin sunyi tunanin zasu koma gida, sai suka fahimci shi batun gidan ne fa bai da wani damuwa a kai.
   Yau ya kasance Laraba. Yana kwance a saman restchair, yana sanye da bathtube. Domin tunda ya fito wanka yake kwance a wurin, shigowa Abraham yayi yana shirin fita wurin party, ya ce mishi.
"Boy yau ne fa Birthday din Anna" ware idanu shi yayi akan Abraham, kafin ya mika zara zaran yatsun shi ya ja wata yar karamar drower ya ciro wani kwali da aka rufe shi leda mai kyalkyali, ya ajiye a kasa.
"Boy gift dinka ke nan?" Lumshe idanun shi yayi yana kara kwanciyar shi a wurin.
"Kai amma ta gode" Abraham ya dauka yana jijjigawa. "Boy" hannun sa ya saka a baki yaja kamar zip, dariya Abraham yayi ya fito ya bar shi a dakin hutun.  Shi dai bai cika son yawo ba, karatu yake sai kuma babban asibitin Harved din da suka dauke shi aiki, shi likitan ƙwaƙwalwa ne, matukar bai tafi aiki ba ko makaranta tow fa, zaka same shi wurin bawa kwalkwalar shi hutu,.baya son hayani ko kaɗan.

TAMBARIN SHAHARA....🌹Where stories live. Discover now