Tace, "Duk abinda kaga ya samu bawa hakan Allah ya tsara daman hakan zai faru da shi. Kada ka tashi hankalin ka, ko ka ce zaka yi kuka, ko ka ce zaka nuna baƙin cikin ka ko makamancin wani abu. Nuna hakan ba zai sa abin ya dawo dai-dai ba, kuma nuna hakan ba za ka iya rewarding abun ba har ka gyara shi. Abinda ya fi shine muyi addu'a, mu dage da addu'a, mu cigaba da yin addu'a kada mu tsaya koda na rana ɗaya ne, addu'a ita ce makamin mumini, baya idan aka haɗa biyun, addu'a da kuma Ibada. Ba mune muke rubuta ƙaddarar mu ba, da ace mune muke rubuta ƙaddarar mu da mun zana ta yarda muke so, da mun zata daidai da abin da muke so, ba kuma zamu zana ta cewar zamu mutu ba, ko zamu rasa wanda muke so ba, ko mu sami baƙin ciki da takaici ko, ko ciwon kai ba zamu bari muyi ba, bare kuma muyi accident da makamantansu".

Numfasawa tayi kafin tayi shiru, yayin da  Sajjad kuwa kowacce kalma da take fita daga bakin tana shiga cikin kunnen sa yana ɗauka yana kuma fahimta tare da sata a wajen da ta dace da wurin. Komai nasa kuma ya tsaya jinta kawai yake yana fassara duk wata kalma nata, ga nutsuwar da take saukar masa kuma sai yake jin ta kamar Antyn sa, yarda take magana cike da lallami da kulawa, sai yaji har irin muryar ma ɗaya ce.

"Kayi haƙuri kada ka tashi hankalin ka. Idan har zaka yi amfani da maganar dana sanar da kai".

Sai ta kuma yin shiru.

Tace, "Aliyu yayi accident, a ranar da ka tafi Kano".

Duk da maganar ta dake shi sosai amma ga mamakin ta ko motsi beyi ba ga yarda yake, banda runtse ido babu abinda yayi.

"Ashe motar ka aka lalata domin idan ka tashi dawowa gida kayi accident, muna ta bincike nida Ƙarami sannan Abban ku ma yana yin nasa amma har yanzu babu wani labari".

Sai a lokacin ya buɗe idan sa ya ɗago da kan sa ya kalle ta.

Yace, "Akwai hanyar da za'a gane".

"Wacce kenan?

"Cameras ɗin dake companyn ɗin".

"Ai duka an duba".

"Ba wannan ba".

"Akwai wata ne?

Jinjina kai kawai yayi yana tashi tsaye ɗakin ta ya shiga ya ga mayafin ta da jaka a ajje da'alama dama fita zatayi kawai ya ɗauko mata yana danna kiran numbern Yaya Ƙarami. Miƙa mata yayi, yayi gaba abin sa. Burin sa a yanzu be wuce yaga mahalukin da ya ke yaga bayan Yayan sa ba.

"Mu haɗu a company".

Kawai ya faɗa yana wucewa. Sai da ya jira ta ta fito, wanda har sai da ya je ya ɗauko key ya dawo amma bata fito ba, haka itama Anty take indai za'a kai ta unguwa bata fitowa da wuri ita da Mama amma Ummi yanzu ne ya fito kun tafi. Can sai ga ta fito tana gyara mayafin girgiza kai kawai ya fito ya buɗe gidan baya ta shiga ya rufe sannan ya ja suka tafi.

Suna zuwa kuwa ya shiga ya buɗe musu suka fara ganin na ranar, ganin mota tayi parking a wajen motar sa yasa su maida hankali a wajen, ba'a ɗauki lokaci ba mutumin ciki ya fito fuskarsa a rufe  yayi kalle-kallen sa sannan ya faɗa ƙasan mota be wani jima ba ya fito, ya shiga mota ya cire abinda ya rufe fuskar sa da shi, ya ɗauki takardun sa ya fito, tsaida wa Ƙarami yayi tare da zooming fuskar shi.

Yace, "Waye wannan?

Sajjad yace, "Bansan shi ba".

Tsayawa Barrister tayi tana ƙare masa kallo dakyau, if she's not mistaken ƙanin tsohon mijin ta take gani. To me yake yi anan? Shi da ƴan gidan su suna Almaty? Me ma ya kawo shi Nigeria?

"Zancen banza, mutum yana aikin a companyn ka amma zaka ce baka san shi ba? Haka daman ake aikin?

"Yaya Ƙarami yanzu mutane dubuwa ne ke aiki a companyn nan. Taya za'ayi a san su".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now