Sarauniya Mundila tayi dariya tace "Yanzu da wannan ne yasa ka ki kwana a gida har tsawon kwana biyar ina ta neman ka, ka gaza zuwa ka sanar dani halin da kake ciki ina matsayin mahaifiyarka har, har akwai abinda zaka boye min?"

      Yayi shiru ya sunkuyar da kai kasa kamar mai yin wani tunani da ya gaza samo mafita.

      Sai Sarauniya Mundila tace "To gobe kaje ka same su ka gaya musu abinda yake zuciyarka, kada ka boye musu komai kuma duk yadda kukayi sai kazo ka gaya min sai a san yadda za'ayi"

     Yarima Harzik yace "To aini ban san abinda zance mata bane!"

      Sarauniya Mundila cikin matukar mamakin kalamansa tace "Yanzu saurayi kamar a ce bai san abinda zai ce da budurwa ba? kaine fa yariman kasar Dizhwar baka da kani ko yaya ko wata 'yar'uwa, gaka saurayi kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, babu abinda ka rasa a duniya kuma duk wani abu da mace take nema ga namiji kana dashi, gaka kyakkyawa ga jarumta ga mulki ga dukiya, amma a ce wai wata mace ta gagare ka tsarawa, haba yarima!"

      "Gaskiya ne ranki ya dade! na kasa yin wani abu da jawo hankalinta zuwa gareni, saboda ni babu wani abu da ya taba hadani da wata mace ba in ba ke mahaifiyarta ba sai dai ko bayinmu da kuyanginmu"

    "Wai da gaske kake"

    "Shakka babu"

    "To kaga ka kwantar da hankalinka je ka kayi wanka kaci abinci sai kazo zan gaya maka abinda zaka gaya mata har ta yarda da kai da soyayyarka"

     "Da gaske Ummina?"

     "Karka ji wai"

     "To shikenan"

     Ya tashi ya sauri ya tafi yaje yayi wanka ya dawo aka kawo masa abinci yaci ya koshi sannan ya dawo gurin mahaifiyarsa ya zauna.

     "To ranki ya dade na gama komai sai ki sanar dani"

      "To kawo kunnenka in rada maka kada ma wani yaji irin wannan salon bare har ya satar maka fasaha"

      "To ga kunnena Ummina ki sanar dani"

      Sai ta fada masa wata magana a kunne cikin rada, bayan ta gama rada masa sai tace dashi a fili "Gobe da hantsi sai ka shirya kaje ka fada mata kamar yadda na sanar da kai"

      Ya tashi yana murna ya tafi dakinsa ya kwanta amma sai barci ya gagara yayi ta juyi yana tunani har gari ya waye, ai kuwa da duku duku ya fito ya shiga wurin mahaifiyarsa ko tashi daga barci bata yi ba.

      "Ni fa zan tafi sai kuma na dawo"

      "Haba! Harzik ka bari mana rana ta dan fito ko zuwa hantsi ne sai ka tafi tunda kace suma basa zuwa wucewa da wuri"

      "Kai Ummina! jinkiri fa shi yake kawo rabon wani"

       "To shikenan je ka ina fatan alheri ganeka"

       Harzik ya fita ya kama ingarman dokinsa ya hau ya fice daga wannan gidan sarauta nasu, da ya isa inda yake ganin yaran nan sai ya tsaya zuwa daf da la'asar sai ga su nan sun zo zasu wuce su debo ruwa sai yace musu "Sannunku"

     "Yauwa sannu" suma suka amsa masa.

      Har sun wuce sun tafi inda yake sai ya kira babbar gefe guda, da kyar ta tsaya ta saurare shi.

      "Abinda yasa na kira nan kusan kullum sai nazo nan saboda in ganki raina yayi fari, hakika ni dai tun randa na fara ganinki na tsinci kaina a kogin begenki tsamo tsamo kuma tun daga wannan rana har zuwa yau kullum da sonki nake kwana kuma dashi nake tashi ina kaunarki kuma ina so ki zama mata ta uwar 'ya'yana da fatan ba zaki kushe soyayya da nazo miki da ita ba"

Je hebt het einde van de gepubliceerde delen bereikt.

⏰ Laatst bijgewerkt: Apr 01, 2023 ⏰

Voeg dit verhaal toe aan je bibliotheek om op de hoogte gebracht te worden van nieuwe delen!

WATA ALKARYA Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu