Yace, "Wai ni za'a tozarta wai ni? Da girma na da kima ta?

Muddansir yace, "Baba sai dai kayi haƙuri amma duk abinda suka ce haka ne, da ace yau kai mutumin kirki ne, na tabbatar da za su yi maka magana mai daɗi amma zamantowarka ba mutumin kirki ba ya dagula komai. Ban taɓa jin inda aka ce mutum da kuɗin sa ka raba shi da shi lalle sai ya zama naka, kuma wai labarin sa kawai ka ji ya shahara shikenan sai ya zama naka? Gashi nan shi ya san ka kai baka san shi ba".

"Mudansir....

Irin tsabar mamakin nan, ya faɗa yana nuna kan sa, ya kuma nuna ɗan nasa. Samun waje yayi zauna kusa da shi yana dafe kan sa.

Yace, "Baba saboda ka reni da san kudi ne fa, nace ba zan auri kowa ba sai wacce Baban ta ke da kuɗi, nace auren jari zanyi. Kuma ka nuna hakan yayi, naje domin na auri ƴar abokin ka, wanda shima ka ƙudirin niyyar cutar sa duk da kana cutar tasa, sai Allah be yi ba, sai yanzu da na sami wacce a halinta suna da kuɗin da na tabbatar da ya fi na Mahaifin Nilah".

Dakatawa yayi da maganar da yake yi jin hawayen na zubawa a idan sa.

"Gashi ba zan same ta ba, kuma so ne nake mata na gaskiya da haƙiƙa amma..."

Kasa ci-gaba da yayi saboda kukan dake zuwar masa, kawai ya kife kan sa ya fara rerawa, ba za'a taɓa gane yadda yake ji ba, duk da yarda ya so yayi bayanin yadda yake ji akan ta, shikam yasan idan ya rasa to ya tabbatar da ya rasa rayuwar sa a yarda yake ji kenan.

"Fita!!!

Ya faɗa a tsawace babu musu ya tashi ya fice, ya tafi wurin Mahaifiyar shi.

"Subhanallah me ya faru?

Mahaifiyar tashi ta tambaye shi ganin yanayin da yake ciki, wanda bata taɓa ganin shi a irin wannan yanayin ba. Yana zuwa ya zauna a ƙafar ta kawai kifa kan sa a jikin kujera ya fara rera kuka, sosai hankalin ta ya tashi amma sai ta ɓoye duk wata damuwa da take ciki taƙi ta nuna hakan, sai ma ta haɗe ran ta, tamau.

"Zaka faɗa min ko kukan zaka cigaba da yi?

Sai dai yayi mai isar sa, sannan ya ɗago ya kwashe duk yarda aka ya sanar da ita.

Tace, "To meye zaka saka samuwa a ran ka?

Da mamaki ya ɗago kan sa ya kalle ta da jajayen idan sa. Jinjina mata kai tayi.

Tace, "Ehh! Kasan bahaushe yace alhaki kuikuyo ne".

"Amma Umma?

Dariya tayi ta su ta manya tana kada kai tace.

"Auren jari manya".

"Umma".

Ya faɗa badan yana so ya ce komai ba, sai dan be tsammaci haka daga gare ta ba.

"Na'am Muddansir".

"Shi daman Allah ai ba ruwan sa idan ya tashi kama mutum, yanzu wa gari ya waya? Akwai wacce kayi soyayya da ita kafin kuyi auren dan kawai Baffan ta sun kwashe gadon mahaifinta shikenan kace baza ka aure ta ba, yarinyar nan tana san ka, tana maka san da bata yiwa kan ta, wanda har yau har gobe tana nan tana kuma girmamani a matsayin na uwa".

Ɗan murmurshin takaici tayi.

Tace, "Samun irin wannan a yanzu yana da bala'in wahala. Na ɗaya baka ji tausayin ta ba, bare ka ji tausayin maraicin ta, ga san da take maka, ko da wannan Allah ba zai barka Mudan".

Sororo kawai ya tsaya yana kallon Umman nasa, kwata-kwata a tarihin ya manta da wata wai ita Safina sai yanzu. Ko tana ina? Ko wanne hali take? Ko tayi aure?

"Kalle ni dakyau ka kuma tunata idan ka manta ta".

"Umma tana tana..tana ina Ummma?

Ya faɗa hawaye na zuba a idan sa.

"Tana inda ka barta".

Ta faɗa tana gyara ƙafar ta dan ta ci abinci aka kawo mata.

"Yanzu Umma har samun damar cin wani abu zakiyi? Nida Baba muna a wannan hali?

"To Babana na ajje kar naci?

"Waya ce maka tension zai hana ni cin abinda nake so? Tension ma kuma ma na ka dana Baban ka. Ai shi Baban ka, na jima da sallama shi daman, duk da nasan duk tsiya ko ya ƙare rayuwar sa a prison ko kuma de ya ni na mutu na barshi ko shi ya mutu ya barni".

"To meye zai dame ni. Kai kuma daman sai addu'a'i".

"Lalle Umma".

"Kai ranar da Mahaifi na ya rasu na ci abinci ƙare wa ma kenan ko? Saboda mutuwa, ba ranar ake jinta ba, ita mutuwa har abada kullum sabuwa ce dal ga wanda ya san me yake yi".

Daga haka bata kuma ce masa komai ba, yayin da shi kuma jiri ya kwashe shi ya faɗi, tasa aka kai shi ɗaki tasa masa drip.


******


Tana zaune a office aka kawo mata wasu takardu ta kaiwa Ogan ta yasa hannu hakan yasa ta tashi domin kaiwa. Yana zaune yana aiki da system.

"Gashi ance ka sa hannu anan".

Ta faɗa tana ɗaura masa akan table ɗin sa, hannu ya miƙa mata alamar ta bashi biro, hannu tasa ta ɗauka a cikin pen stand ta bashi. Hakan da tayi sai yasa shi jin ƙamshin mayen turaren nan nata.

"Mtsww!

"Kai da wa?

Banza yayi mata, ita ma bata da mu ta cigaba da tsayuwa har ya gama tas sannan ya bata.

"Na mayar musu?

"Su wa?

"Wasu turawa ne, su biyu".

Jinjina mata kai kawai yayi. Ita kuma ta fita domin kaiwa. Tana cikin tafiya tana karantawa har ta iso elevator ta shiga, kawai karatun ido take yi musu idan tayi wannan sai tayi har ya fita ta zo zata shiga office ɗin Baturen bayan ta tambaya papern ƙarshe taga ta share ce mafi girma da suka bayar, abin ba bata mamaki bayan kuma tsohon sectary yace sun dena bada share, sun mayarwa da duk wanda suka bawa? To ya akayi haka kuma? Kuma ita kadai ce ta fita daban. Tana tsaye tana tunani taga Sagiru da Bashari sun fito daga office ɗin suna murna. Saurin laɓewa tayi ƙirjinta na mugun gudu.....













A SOYAYYAR MUDove le storie prendono vita. Scoprilo ora