"Kai baka da lafiya ne?

Cewar Yusuf.

"Ni bana san sa ido, ina ruwan ka da ni".

Hafiz yace, "To fa, yau kuma kai ke haka?

Banza yayi musu ya yi hanyar shiga cikin gida, yayin da ta gaida su suka amsa mata cikin kulawa.

Hafiz yace, "Basa nan suna Bauchi".

"Abba yace yau za su dawo".

Ya basu masa yana juyowa da basu amsa yana zabga musu hararar da ba su san ta menene ba. Part ɗin Anty ya nufa da ita ya zauna ita kuma ta nemi waje ta tsaya tana ƙare wa parlourn kallo yayi kyau sosai.

"Soja kika zama ne?

"Banji ance na zauna ba".

"Sai kinji nace ki zauna?

Shiru kawai tayi masa bata ce komai ba. Ƙwafa yayi.

Yace, "Cigaba da tsayuwa to".

Daga haka ya tashi ya shiga kitchen, ita kuma ta sami waje ta zauna, jin wani irin bacci bacci na fizgarta yasa ta jingina da jikin kujerar da ta zauna sai bacci. Noodles ya dafa musu ya soya kwai ita kuma ya dafa mata ya haɗa musu tea ya fito da shi ganin ta tana bacci yasa shi ajjewa a kusa da ita sannan ya tashe ta.

"Tashi mu ci abinci".

"Kuma da kai zan ci?

"Kuturu ne ni?

Taɓe baki tayi tana shirin saukowa.

"Da wa kike?

"Dana ce me?

Ƙwafa ya yi ya sa hannu ya fara ci yana ci yana haɗawa da kwai, yana kurɓar shayin sa, haka ita ma.

"Dena cimin kwai na, ga na ki nan".

"To me yasa baka soya duka ba?

"Kinyi employee ɗina ne?

Bata ce komai ba ta cigaba da ci, dan ta lura neman magana ne kawai irin nashi da san neman faɗa ita kuma yanzu bata shirya wannan zaman da sukayi a baya ba, da Nilahn da, da ta yanzu ba ɗaya bace.

Ɗayan ɗakin Anty ya nuna mata yace taje ta yi Sallah ganin suna cin abinci lokacin sallah yayi, daga nan za su shiga companyn zuwa yamma kafin nan sun dawo. Shine ya tattara wurin ya wanke komai da sukayi amfani da shi sannan ya fito.

"Baki shiga ba?

"Dan Allah jaka ta".

"Ohh sorry".

Ya faɗa yana nufar waje da ɗan saurin sa. Be jima ba ya dawo ya bata jakar har ƙaramar jakar ta. Tunani ta fara yi, ita de daga zuwa gidan mutane ai bata yi wanka ba kuma a gidan surukai, sannan basa nan? Sai taga kamar be kamata ba, hakan yasa ta kawai yin alwala ta ɗan gyara fuskar ta da sauya kaya kawai tayi Sallah ta fito.

~~~~

Babu abinda yake yi sai Safa da marwa a cikin tamfatsetsen parlour wanda ya ji kayan more rayuwa ya haɗu ta ko ina. Sheshshekar kukan Muddansir ce ke tashi a parlourn. Gajiya yayi da jin sautin kukan nasa haka yasa ce tsawatar masa ya dena amma inaa sai na ma ƙara tunzura shi da yayi kamar wanda yace masa ci-gaba da kuka.

"Wai ba zaka min shiru ba?

"Ba magana nake ma ba?

Daƙyar ya samu ya dena kuka mai sauti batare da ya dena hawaye ba.

"Shi hawayen shanye maka shi zan yi?

Hannu yasa ya fara gogewa yana jan majina, wani wawan tsaki yaja.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now