Mai gadin ya faɗa yana zuwa ya buɗe musu, sai dai yana buɗewa kayo ball da shi sai ga shi a ƙasa warwar aka nuna masa bindiga bayan an caka masa wani abu a ƙafa aka rufe bakin sa gam yadda baza'aji ƙarar sa ba.

"Kana magana zan fasa kan ka".

Ɗaga kai ya fara yi kamar wani ƙadangare.

"Muje ka nuna mana inda aka ajje wannan yarinyar".

Babu musu ya fara nuna musu hanyar gidan, ta bayan gidan suka bi har suka hawo saman babban parlourn suka tarar da wannan shirgegen yana bacci suka shaƙa masa wani abu,jin motsi yasa wani fitowa kafin yayi magana an shaƙa masa sannan suka rabu cikin gidan shi kuma ya nuna musu ga ɗakin. Amma a rufe.

"A nan take?

Ɗaga kai ya fara yi, don a zaba ba zata bar shi yayi magana ba, ya gaskata da ake cewa sojoji mugaye wato dan kada yayi musu garda shine suka fara masa illah shida soja har abada daga yau kuma ya dena wannan aikin ko zai mutu yana neman kuɗi kuwa.

Sajjad ne ya fara kiran sunan ta, da gudu ta tashi ta ƙara kara kan ta a jikin ƙofar ya kuma kiran sunanta. Hakan yasa sata buɗewa kawai ta faɗa jikin sa, ta saki wani saban kukan tana cukuikuye shi, shima rungume ta yayi tsam a jikin sa yana taya ta kukan, Aliyu kuwa tsayawa yayi kawai yana kallan ikon Allah da tunanin anya kuwa kan su ƙalau yake? Sai dai babu yadda ya iya hakan yasa shi yin shiru ganin de eh ba ƙalau suke ba daga shi har ita, dan shi ya manta da wata Nilah.

"Ku muke jira".

Aliyu ta faɗa yana kallan su, ganin yanzu ya haɗe fuskar su a wuri ɗaya yana tambayar a by ɗaya. Jin anyi magana yasa ta ƙoƙarin zare jikin ta daga nashi amma yaƙi bata damar yin haka, sai kuma wata irin mashahuriyar kunya da ta kamata. Banda ajiyar zuciya da jan majina babu abinda take yi haka ma Sajjad haka suka fito tana jikin sa ya riƙe ta gam-gam wai kar a kuma sace ta, tana fitowa ta ɗaura idan ta a wanda ya sace ta a karo a farko yana nan be canza ba a kuma yarda yake, sosai gaban ta ya faɗi tana kallan Sajjad.

"Wannan ne ya sace ni na farko".

Ta faɗa tana sake nuna shi, sai kuma luuu ta tafi ta zube ya turo ta kayan sa. Tsuro-tsuro yayi yana tsilla ido shi kam ya shiga uku me kuma yayi? Aikuwa aka tisa ƙeyar sa aka sanƙama su a cikin motar su daban.

*****

Jiddah ce a zaune tayi shiru ta sa abinci a gaba, yau babu wanda take so sama da Mahaifiyar ta, ganin bata ci ba yada Abie shima be ci ba, babu yarda ba'ayi da su ba su ci akai su amma ƙememe sun ce su Mammyn su za su gani. Bintu babu wayon da bata musu ba amma sun ƙi. Abba da ya san komai saboda duk abinda ake ciki Senior na kiran sa, Allah yasa anganta da ba'a ganta ba shikenan ba su san ya za suyi da wannan yaran ba.

Abba yace, "Yanzu ba za ku ga Mammy ba, sai zuwa gobe idan Allah yasa mun koma can gida tunda daga can muka taho da ku ko?

Abba ya faɗa cike da lallami da kuma kwantar da murya.

"Sai gobe zamu koma?

"In Sha Allahu".

Inna tace, "Da baku dan yara ba kuyi ya kwaso su".

Abie ne ya haɗe rai, yana kallan Abba.

Yace, "Ni bana san wannan matal".

"Ai bance ka so ni ba daman, shegen yaro da rashin R ɗin ka".

Jiddah tace, "Nidai Yayana ba shege ne ba".

Ta faɗa tana turo baki gaba, tare da ɗaukan abinci ta fara ci.

"Kuna jin su ba baza kuyi musu magana ba suna zabga min rashin kunya?

Abba yace, "Kiyi haƙuri".

Sannan ya dawo kusa da ita murya ƙasa-ƙasa yarda ba za su ji ba.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now