Shafi Na Sha d'aya

Start from the beginning
                                    

A takaice familyn sun shiga tashin hankali ba kaɗan ba kan su samu labarin Abrar, yayin da wasu ke farin ciki kaman Hajiya Yaya ji take dama ace yana cikin waenda suka mutu taga karshen tsiya da soyayya da suke mai yayin da hajiya babba take jin daaɗin Shima daga karshe ya mutu kaman yadda yayi mata sanadiyar miji daga zuwan shi duniya, Nadra bazaka ce ga halin da take ciki ba ita bata farin ciki saboda bata so ya mutu cikin sauki haka be bi baabin azaba da wahalar da ta shirya mai ba, ta wani ɓangaren kuma tana farin ciki sbd bata da tabbacin haƙan ta ze cimma ruwa sbd taurin rai da sa'a irin na Abrar.

Sede jin cewa baya cikin waenda suka mutu sede yaji rauni kuma an ɗauko shi a Jirgin su na sojoji yanzu haka ma suna shirin sauka Kano yasa hankalin da yawa ya kwanta a take Khalid ya kira hospital ɗinsu a tura Ambulance su haɗu a airport don shi kam be yarda da asibitinsu na sojojin ba ya za'ayi ace a sa abin tashi a cikin wurin aiki ba tare da ma karkashiya ba idan boko haram ko bandits ne ai sede hari gar da gar.

Sanin baza'a taɓa shi ba ko da sun kai shi asibiti se da sa hannun family ɗin shi yasa ya karawa motar shi speed, shi da Abdulkadir ne yayin da Abbu da su Daddy suka yi asibitin su Khalid ɗin a lokacin karfe ɗaya saura na dare....

Likitoci sun fi biyar kanshi ana kokarin ceto rayuwar shi da ikon Allah da rahamar shi suka samu suka ceto shi, ya samu tsagewar ƙashi a hannu se kafan shi da ya ji ciwo sossai, Amah da farfaɗowanta kenan taji an samu an ceci rayuwar shi da ikon Allah se ta ɗauro alwala ta fara sallah, Su kansu su Uncle maraq se lokacin suka samu kansu duk da basu ganshi ba sede Khalid ya tabbatar musu yana cikin koshin lafiya yanzu sauki ze samu ne a hankali..

Duba time daddy yayi 3 ya gota na dare, Liuetenant General Sani Idris tare da Major General Habeeb ghali ne suka shigo asibitin da rundunar sojoji fuskokinsu ba fara'a ko ɗigo sojojin dake zube a kofar ɗakin ne suka kakkame yayin da su Abbu suka kara so suka gaggaisa, Duba shi suka yi tare da kwantar wa da su Abbu hankali akan in shaa Allahu za'a bashi tsaron da ya dace sbd shi ɗin ɗan gatan Field Marshal Muhammad Attahir shugaban sojojin Nigeria gabaɗaya ne yanzu ma shi ya turo su kuma in shaa Allah se an bi diddigin komai baza'a bar komai a rufe ba. Sun ɗan jima a tattaunawar kan suka tafi.

A ɓangaren Amatullah kuwa tunda karfe ɗaya ya buga ta mike daga zaune da take kaman gunki ta shiga toilet Alwala tayo ta zo ta hau kan sallaya ta fara nafila tana jero mishi aduoin samun lafiya sbd taji fitansu kuma taji wasu tattaunawar tasu, addu'a take tana kuka tana rokon Allah ya bashi lafiya ya tashi kafaɗunshi kaman yadda yake me tausayi da kuma taimako Allah ya taimake shi a sadda yake tsananin bukatar taimakon da tausayi daga wurin mahallicin duk duniya.

Nadra ke kai kawo yayin da hajiya Yaya ke binta da idanu tace
"wannan zirga-zirgar babu inda zata kai ki fa, kin kasa ajiye zuciyarki wuri guda anya ba sonshi kike ba?".

Wani dariya tayi tace.
"So? Ko ɗaya babu soyayyar Abrar a raina ƙinshi dake raina yafi duniya da Abinda yake cikinta en uwa biyu da nake dasu jal a duniya fa ya ɗauke min su ya raba su da rayuwar su, kawai bana so ya mutu cikin sauki haka ne I want his death to be painful and slowly bayan na bubbuɗe mishi fejukan tashin hankali da damuwa da na tanadar mishi a littafin kaidina"

Dariya sossai Hajiya Yaya tayi tare da cewa "Allah ya bada nasara yanzu na kara tabbatar da idan har haƙan ki ya cimma ruwa ba gawa ɗaya ne ze tafi ba sede gawarwaki"

Da sauri tace
"amma ina ga wannan good opportunity ne muka samu akan Wannan baƙar munafukar Amatullah ne ko waye?"
Nadra tace
"me shawararki? Ban taɓa ji nayi mugun tsanar mutum farar ɗaya bayan Abrar a rayuwa ta irin yarinyar nan ba"

"Auntynsu sun tafi da Saudat Asibiti, mazan duka basa nan Hajiya babba na san tayi nisa a bacci haka Mufida da Aisha, me ze hana mu ɗauko ta ta karfi mu sata a mota ki ja ki kai ta nesa da nan gidan ki wullar da ita yadda ko hanya bazata gane ba?"

Haɗa yatsunta tayi ta buga ya bada Kass tace
"brazo! Sam hankalina be kai ga wannan Tunanin ba muje"

Fita suka yi zuwa sashen Amah tana zaune kan sallaya har zuwa lokacin sede yanzu karatu Al Qurani me girma take yi, Hajiya Yaya na isa ta fisgota ta tsinkawa fuskanta marin da ya kusa kurman tata tace
"shegiya tsintacciya wannan marin na miki shi ne sbd sanadiyar zuwan ki gidan nan Saudat ta fara maida mana magana cikin isa to duk abun da kika kullo kika zo dashi yau ya ƙare"

Fincikota Nadra ma tayi ta watsa mata mari a ɗaya gefen tace
"wannan kuma sakamakon shiga harkar Abrar da kika yi ne, gargaɗi ne me sauki in kina sha'awar ganin girma da faɗinshi ki dawo cikin gidan nan zaki gani"
Jan ta tayo suka yi waje fuuuuu zuwa parking space motar ta ta buɗe ta wullata baya, alamu ma kaman ta suma ne ko ciwonta ya tashi wani irin rawa jikin ta yake...

Nadra da Hajiya Yaya basu damu ba Sam Nadra taja mota tayi horn me gadi ya buɗe ta fice da gudu yayin da hajiya Yaya ta koma sashenta cikin halin ko in kula kaman ba mutum bane suke kokarin tozarta wa cikin talatainin dare.

Seda Nadra tayi tafiya me nisa ta isa cikin wani unguwa me tsananin duhu kuma ghetto area ta fito ta buɗe back seat ta Fincikota ta wullar da ita har Seda goshinta ya bugu da wani Dutse a take ya fara zub da jini, bata ko kula ba ta shige motar ta ta fige shi tana jin daaɗi, yadda ta samu nasara akan wannan tsintacciyar da ta so kawo musu cikas a plans ɗinsu haka zata gama da Abrar da yardar Allah..

Duhun wurin ya kara tsorata Amatullah hakan yasa ko tashi ta kasa yi duk da yadda jini ke wanke fuskanta jikin ta in banda rawa ba abunda yake yi, ko ambaton sunan Allah bakinta ya kasa fasalta mummunan halin da take ciki a wannan lokaci baze yiwu ba, wasu Matasa da suka shawu suka yi Nak su biyu ne suka yo inda take se surutai suke, ɗaya ne yayi tuntuɓe da kafarta yayi taga taga ze faɗi ya samu ya tsaya daidai yace

"kan..... Wani me karar kwanan ne ya sa min kafa na kusa faɗuwa?"

Ɗayan ne ya haska touch duka baki suka buɗe suna kallonta na farko yace.
"Baaba kana ganin Abinda nake gani kuwa ko gizau ne? Ko de aljana ce?"

Wadda ya kira da Baaba yace
"ba aljana bace kai banza, kana ganin kafafunta na mutane sannan ga jini na fita a goshinta mutum ce, tsuntsu daga sama gasashe dama banda kuɗin biyawa wanchan gida na bayan layi a ɗayar kuma nayi na bashi Reza se nema na take ta ci min mutunci"

Dariya suka yi a tare na farkon ya duko kanta yace
"kai yarinya ga kyau ga diri yau muna aljanna kace hahaha haha"

Belt ɗin wandonshi ya hau since wa yana furta
"kai kauce in fara don na san yau zamu kwashi romo"
ba tare da wani nazari ko tausayin halin da take ciki ba ya nufe ta gadan gadan.....

*Tou Fah ana wata ga wata, Anan Dae Littafin Gamon Jini ya kawo karshen Free pages ɗin shi me ke shirin faruwa nan gaba? Shin Waennan Marasa tsoron Allahn za su samu galabar aikata nufinsu wa Amatullah? Idan hakan ta faru wani irin hali Abrar dake kwance cikin fitan hankali ze shiga? Shikenan Nadra ta fara samun nasara kenan a cikin baabin rayuwar Abrar?*

*Shi kuwa tafiyar bazata yayi taya har aka samu aka kai mishi wannan mummunan harin da ba don Allah ya kare ba sede gawar shi? Kenan bayan colonel Nura bukar akwai da yawa masu farautar rayuwan shi a cikin sojojin? Anya Amah zata bari ya cigaba da wannan aikin? Shin Abbu ze samu nasarar lankwasata a ko da yaushe kaman yadda ya saba ta amince da Auren Nadra da Abrar don samun kwanciyar hankalin mahaifiyar shi?*

*Duka wannan zasu kasance cikin saukin fahimta ne da zarar kin biya Naira ɗari Uku kachal kin mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, akwai tufka me matukar sarkakiya a wannan labari karki bari a baki labari ƴar uwa*

****

*Ko kin shirya mallakar Wad'annan TAURARI Guda biyu😉 Da Naira Dari biyar kachal zaki mallaki gawurtattun littatafan nan guda biyu...

*GAMON JINI Na Fatima Muhammad Gureen (Gureenjo)*

*Da Kuma*

*SABABI Na Amina Ibrahim (Oum Ameer)*

*Akan Naira D'ari uku kuma zaki mallaki Guda d'aya cikin biyun, karku manta mun shirya tsab domin Nishad'antar daku, fad'akar daku da kuma Nishad'antar da ku masoya, Mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali er uwa👌*

Zaku iya biya ta account number kamar haka
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
    Se a turo shedar biya ta wannan layin
09039206763
Note: Banda Recharge card.

🖤Gureenjoh🖤

GAMON JINIWhere stories live. Discover now