Shafi Na Takwas

170 3 0
                                    

⚡️*GAMON JINI*⚡️

*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

*FREE PAGE EIGHT*

*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*

*****
Malam Imam Muhammad magashi shine asalin mahaifinsu, su biyu kachal iyayensu suka haifa da shi da kanwarshi Asma'u, mahaifinsu asalin shi limamin massallaci ne a nan garin magashi na jihar kano, sana'arshi kuwa saida kayan hatsi ne ba kuwa ta kirki ba sbd ko buhu d'add'aya na hatsi a lokacin be kai ba sana'ar tashi, kaman yadda ya tashi ya samu gidansu da karatu haka shima yake kokari sossai akan ilimin addini, mahaddaci ne hakan yasa ko hanya ake ganin kimarshi ana mamakin matashi irinshi da irin ilimin addini na ban mamaki.

Wata rana ya fita a hanyarshi ta zuwa kasuwa yabi ta wani lungu ya samu rikici ya kachame tsakanin wata me saida abinci da wani customer d'inta d'an garuwa ya ci yace karfinta ya kwatar mata, dukda yadda ake rirriketa haka take daddagewa ta watsar da kawayen nata dake talla tayi kan shi shima maza sun rirrikeshi, a natse ya karaso yayi mata sallama, murgud'a baki tayi gefe tare da juya mishi keya..

D'an murmushi yayi yace
"Baiwar Allah be kamata kina musulma kuma d'iya mace ki tsaya a tsakiyar unguwa kina rikici har dambe da namiji ba, muryarki alaura ce kaman yadda jikinki yake duba kiga..!"
Ya nuna ta sama har kasa Gyale na yashe a gefe, Dan kwali taci d'amara dashi, d'age kai gefe tayi tare da murgud'a baki cikin kunkuni tace
"To ni se aka ce ya ci kayan sana'ata yaki biya ai.."

Wani dattijo yace
"Ke Mairo, har yaushe zakiyi hankali ne? Yanzu aka barki da me Ruwan kina tunanin zaki iya dukanshi ne? Kuma ki duba wadda ke miki magana amma kike mishi kunkuni?"

Kuka ta fashe dashi tare da zubewa kasa tana ta zabga kuka, murmushi Imam yayi ya karasa ga me Ruwan yace
"Kaji tsoron Allah ka sani duk hakkin da kaci ba naka ba se ka ga ba daidai ba tun anan duniya kan aje lahira, wlh a duk lokacin da ka ce zaka sanya haram cikin jarinka kana juyawa bazaka ta'ba ganin riba ba, ina anfanin ciyar da iyalanka da haram? Ka sani duk fatar da haram ta gina ta to tabbas ta tabbata makamashin wutan jahannama"

Jikin kowa ne yayi sanyi shi karan kanshi me Ruwan yaji ya muzanta, kud'i ya cire ya karasa wurin Mairo dake ta jan hanci ya mika mata tare da karawa da
"Kiyi hakuri"
Kar'ba tayi tare da mikewa ta d'au gyalenta, kallon Imam me Ruwan yayi yace
"Na gode"
Dukda tabbas ze girme ma Imam ba na wasa ba sede ya san yaron Allah ya bashi abinda be bawa kowa ba.

Murmushi kawai yayi tare da wucewa kasuwa ya kar'bi mahaifinshi inda shi kuma ya koma gida, nan da nan jama'a suka fara tururuwa a gaban shagon, ana mugun son sayan abu a wurinsu Imam basu kasance masu tauye mudu ko sayar da abinda be da kyau ba sau dayawa sun gwammaci su yi asara da su sayar da abu marar kyau ba tare da sanin me ciniki ba, hakan yasa ake martaba su ake kuma sayan hatsi wurinsu, wadda hakan ke sawa sauran en kasuwan bakin ciki, dama haushin Imam d'in suke ji a duk sadda ya ga sun tauye mudu se yaje ya musu nasiha ba ruwanshi ga kwarjininshi ke hana su iya ta'buka komai ko da sun gama cikawa juna baki kuwa.

Wani abun mamaki tunda Imam ya raba fad'ar mairo da me ruwa ya kasance be da aiki se tunaninta a duk sadda ya tuna ta se yaa saki murmushi a hankali hankali ya maida hanyar da take saida abinci hanyar bi da kad'an kad'an ya fara sayan abinci kawai sbd ya ganta a duk lokacin da ze ci abinci ze tsinci kanshi da yawan kallonta ita kuwa se ta kasa natsuwa sbd kwarjininshi wasa wasa wani irin mugun shakuwa ya shiga tsakaninsu har ya juya ga soyayya daga nan se maganan aure.

Kaman ko wani aure sun fuskanci kalubale en uwanshi sun nuna basa sonta tana da rashin kunya sede abun nasu be yi wani tasiri ba sbd Malam Muhammad be d'aukeshi hujja ba, an yi aurensu inda suka tare a gidansu me d'akin ginin kasa guda biyu da kitchen da bayi, zamansu yayi kyau sossai sbd dama Allah ya san me ya had'a tana mugun son shi kuma duk masifarta bata iya mai sbd kwarjininshi da kimarshi da ake gani, a haka suka haifi yara mata hud'u Asma'u wadda yayiwa kanwarshi da yake mugun ji da ita, itama tayi aure a Magashi d'in se Aisha mahaifiyarshi..

GAMON JINIWhere stories live. Discover now