Shafi Na Tara

188 3 0
                                    

⚡️*GAMON JINI*⚡️

     *NA FATIMA MOH'D GURIN*
               *GUREENJO*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

*FREE PAGE NINE*

*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*

*****

Baya manta watarana ya shigo cikin garin magashi da misalin karfe shidda na yamma a gajiye yake be da wani buri se na ya ga yayi salla ya kwanta ya huta, yana saka kanshi cikin gidan yaga Zainab er shi ta fari da Rumasa'u ta biyu suna rike da saudat d'iyar da bata fi shekara da wata biyar ba se kuka take muryarta ko fita baya yi da alamu ta jima tana kuka, suma duk se hawaye suke yi.

Da sauri ya karasa kansu yana cewa
"Zainab me ya same ta? Ina mamarku?"
Cikin kuka Rumasa'u tace
"Bamu sani ba Abbu ta fita tun da safe, gashi tun azahar saudat ke kuka har yanzu bamu san me ke damunta ba"
Surar Saudat d'in yayi yace
"Ku zo mu je"

Mota suka shiga a rud'e yake jin yadda jikin yarinyar yayi wani irin zafi be yi tunanin yunwa bane, kano suka koma dayake ba wani Nisan kirki bane, asibiti da suke da NHIS ya kai saudat a take aka kar'beta sede lokacin ma ta fara convulsion a rud'e ya kira Almustapha ba'a jima ba se gashi, shine ma ya iya sake tambayar su Rumasa'u dake kuka me ya sameta?

Rumasa'u tace
"Tun jiya kaman bata da lafiya dama tunda Mama suka fara fad'a da Abbu kullum in baya nan se ta fita ta barmu da saudat sede muyi ta bata ruwa har ta dawo da dare, to jiya duk yadda mukayi tayi shiru taki da mama ta dawo muka gayamata tace ta mutu ma in ta so, uban da yasa sunan buduruwashi yazo ya bata mama..."

Hanci ta ja tana shesheka er shekara biyar ce ke musu wannan bayanin yayinda muniba dake da bakwai bata ce komai ba se kuka, seda Almustapha yace
"Ehem se me ya faru yau kuma?"
Ta cigaba
"Se yau zata fita nace Dan Allah tayi hakuri ta fita da saudat bata da lafiya tace in ban rufe mata baki ba zata ci ubana, kuma daga ni har Zainab muka kuskura muka fad'a maka in ka dawo zata yanka wuyanmu"
Sossai ranshi ya 'baci jikinshi har tsuma yake me yasa wasu mata kishinsu ke zama hauka akwai wadda ya haifa mata yarinyar ne? Ta cire tausayi da imani ta ajiye gefe sbd banza kishi..

Be gama tunaninshi ba likitan ya fito jikinshi a sanyaye yace
"I'm sorry we lost the baby, ciwon ciki da zuwa yanzu bamu san musabbabi ba shi yayi ajalinta"

A firgice ya mike yana ambaton sunan Allah hawaye na zuba a idanunshi yace
"Dr. Kisa ne please kuyi filing case, call the police immediately..."
Jiri ne ya d'ibeshi a take ya nemi zubewa se Almustapha ne ya tareshi a take ya suma...

Ba karamin rikici akayi ba kwananshi biyu a asibiti, ya dankara ma halima saki biyu kuma ya rantse da Allah se sun yi shari'ah, da kyar Malam Imam ya sauko dashi itama halimar kwananta d'aya asibiti sbd rud'ewa bata ta'ba tunanin zata rasa yarinyar ba a tunaninta idan uban ya gaji da halin da take yi ya fasa auren, maidata kam duk yadda malam Imam yayi Muhammad yaki yace ba yanzu ba...

A tsakankanin ya karasa ginin gidan da yake a cikin kano wadda Almustapha ne kawai ya sani a lokacin ne kuma suka rasa kaninsu Murtala d'an shekara bakwai sanadiyar Amai da gudawa me tsanani, Muhammad ya nuna it's high time su bar magashi sbd rashin ingantaccen ruwa ne yayi sanadiyar Murtala, Malam Imam ya nuna baze iya barin magashi ba, ba yadda Muhammad ya iya haka aka yi aurensu da Saudat be bari sun zauna magashi na kwana biyu ba suka koma cikin kano, da Almustapha da muniba da kuma Aisha waenda saudat ta maidasu en d'aki kuma abokan hirarta sossai take sonsu..

Bayan watanni uku Mairo ta sake haihuwa aka maida murtala a lokacin Saudat na da cikin wata biyu, ba fa wai Mairo ta saduda da tsanar da tayiwa Saudat bane se ma karuwa da yayi, a ganinta bakin jininta ya janyo mutuwar jikarta da kuma raba auren Muhammad da Halima, hakan yasa ko kallon saudat batayi idan ba bakar magana zata ya'ba mata ba, gashi Muhammad baya iya 'boye son ta hakan ke kara kona mata rai ta tabbatar asirin da ake maganar en Gombe da iyashi shi tayi ma d'anta.

GAMON JINIWhere stories live. Discover now