Shafi Na Sha d'aya

427 10 2
                                    

⚡️*GAMON JINI*⚡️

     *NA FATIMA MOH'D GURIN*
               *GUREENJO*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

*LAST FREE PAGE*

*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*

*****

Rigingine yake kan doguwar kujera cikin haɗaɗɗun kujerun da suka ƙawata parlorn, ya tabbatar tun kan ya dawo masallaci ta zo ta ajiye mishi abinci ta tafi duk da baze ce basu taɓa samun saɓani a rayuwar auren su ba sede saɓanin kalilan ne kuma baya ɗaukar kwana ɗaya ba tare da sun shirya ba ya sani sarai yawan hakuri irin nata ke kwantar da zuciyar shi a duk sadda ya tafasa, runtse idanunshi yayi to Me yasa a yanzu ta kasa hakuri ta tankwara zuciyar ta?

Tunanin irin baƙar rayuwar da tayi da mahaifiyarshi da kuma Halima ya Lula, a hankali ya Mike zaune tabbas be yi mata adalci ba ya kamata a ce ya fahimce ta ko da kuwa ta mayarwa da hajiya babba magana ne sbd ta juri da yawa da yawan da baze iya lissafawa ba wani kam ya sani har abada baze sani ba tun da kullum a fita yake ya barsu cikin gida.

Da sauri ya mike tsaye tare da nufan kofar da ya sadashi da part ɗin ta ta cikin parlorn kaman yadda nayi bayani a baya, daidai ya sa kanshi cikin parlorn kenan yaji karajinta tana kiran sunan Abrar da sauri ya karasa ɗakin gabaɗaya ta fice hayyacinta tana shirin yowa waje da gudu ya riƙe ta yana furta
"saudat lafiya? Me ya faru ne? Me ya samu Abrar ɗin"

Hawaye wani na bin wani a fuskanta tana girgiza kai tace.
"Dan Allah Abbunsu ka kaini wurin ɗana in ga halin da yake ciki wallahi ba lafiya ba, wani abu ya samu Abrar dan Allah, inna lillahi wa inna ilaihi rajiun"

Gabaɗaya ta ruɗe ta ruɗa shi duk yadda ya so ta natsu tayi mai bayani ta kasa kawai maimaita Lamido baya cikin koshin lafiya da salati take, Khalid, Abdulkadir da jabir ne suka shigo da sallama ganin halin da take ciki se suma suka nemi ruɗewa, da sauri Abbu yace
"Abdulkadir kira min yayanku maza maza"

Da sauri ya fiddo waya ya fara kiran layinshi sede baya shiga Sam, kara ruɗewa Amah tayi Khalid da jabir duk gwada layin suke sede baya shiga Sam Sam.

A ta ɓangaren Amatullah tana jin hayaniya tana tsoron fitowa a ganinta family issue ne tsintar kanta tayi cikin tsananin hawaye tana addu'a Allah ubangiji ya kare shi kar ya sa wani mummunan Abu ya same shi.

Juya akalar Kiran Khalid yayi ga Daddy da kuma Uncle murtala cikin lokaci kalilan suka iso parlor suka fita, har lokacin Amah na kuka har numfashinta na yanke wa a jikin ta bata ji Abrar na lafiya ba duk cikin yaran ta babu wadda jikin ta ke saurin gaya mata yana cikin mummunan hali kaman Muhammad Abrar, Daddy ne ya bada shawarar Abbu ya kira headquarter ɗinsu aji ko akwai abin da ya faru don Amah bayanin yadda aka yi ta sani ma ta kasa.

Cikin hanzari kuwa ya kira su ba'a ɗaga ba, kaman an ce Jabir ya kalli TV dake aiki ya ga sunan Yayansu daga kasa da sauri ya ɗauki remote ya kara volume wadda ake maimaita kanun Labaran a nan suka ga Abinda ya kara ɗaga hankalinsu har yayi sanadiyar Suman Amah, Abin fashewa da ba'a tantance menene ba ya fashe a office ɗinsu na boarder ɗin Sokoto wadda yayi sanadiyar mutuwar sojoji biyu da ba'a tantance ba, me rahotonsu na chan ya tabbatar Brigadier General Muhammad Abrar Muhammad Magashi na cikin wanda abin ya ritsa da a sanadiyar ziyarar bazata da ya kaiwa rundunar shi don tabbatar da ayyukansu na tafiya cikin tsari da daidai.

Aisha, ruqayya, Aunty da matan daddy ne suka shigo a tare cikin ruɗewa basu zauna ba Aisha da Mufida yaran Hajiya Yaya tare da Nadra suma suka shigo gabaɗaya su a ruɗe sede ganin Khalid na kokarin ceto rayuwar Amah ya kara hautsina su yayin da Abbu ke ta kokarin reaching headquarter ɗinsu don yaji Abinda ke faruwa a ina kuma Abrar yake..

GAMON JINIWhere stories live. Discover now