Har cikin saudat ya shiga watan haihuwa baza'a wayi gari a kai dare bata yiwa Muhammad maganan maida auren halima ba, ranar wata juma'a ta tashi da nakuda Almustapha da su Zainab suka kaita asibiti sbd Muhammad na kasuwa ta sha wahala sossai kan ta haifi santalelen yaronta na miji, se kiran Muhammad akayi aka sanar dashi ta haifi yaro namiji, farin ciki ba'a magana musamman yadda yaron ya kwaso kamannin ta sak, har hasken fatar sa'banin Muhammad dake wankan tarwad'a.

Ba irin 'barin kud'in da be yi ba a kan Yaron, danginta suma sun yi rawar gani kyaututtuka da ya samu ba'a magana sbd mai martaba na mugun ji da Saudat yasa duk makusancinshi seda ya san haihuwar, sarki kuwa da kanshi ya sanar da albishir ba'a bada tukuici me tsoka ba ai be yi ba, kan ranar suna yaro ya mallaki filaye da gidaje, a kano da Gombe.

Ranar suna kuwa Muhammad ya saka sunan babanta, baze ta'ba manta karamcinshi na bashi ershi alhalin shi ba kowan kowa ba bayan sarakuna da 'ya'yansu bila adadin sun nemi hannunta a aure ya hana yace se shi tunda shi take so, en uwanta ne suka mishi lakabi da Abrar. Ma'anar Abrar (me gaskiya, me tsoron Allah kuma nitsatse)

Bayan kwana biyu da suna malam Imam ya taho da kanshi don kallon jikan nashi me sunan babanshi dukda ba ainihin sunan yaci ba sede Muhammad dae Muhammad ne kuma gud'a d'aya jal d'in nan ake wa takwara wato fiyayyen hallitta, adu'a sossai ya mishi ya kasa d'auke idanunshi daga kan Abrar har Muhammad ya kasa shiru yace
"Malam na lura Abrar ya kwace duk wani matsayi na kowa a zuciyarka"

Murmushi yayi yace
"Ni kad'ai na san abinda na gani ga yaron nan, sede ba lallai in kai lokacin da abubuwan zasu bayyana ba, ina mishi fatar alkhairi kuma ina mishi adu'ar duk wani kaddara tashi ze yi kokari ya tsallaketa ba tare da yayi kuskure ba"

Da mamaki Muhammad ze kara magana malam ya mikawa Saudat dake zaune yace
"A kowani lokaci ki zama me fahimtar wannan aboki nawa, bakinki kuwa kar ya furta mummunar kalma zuwa gareshi duk tsanani Allah yayi muku albarka duka"

Suka amsa suna kallonshi, mikewa tayi ta fice ya dubi Muhammad yace
"Kayi hakuri babana ka dawo da Halima gidanka shekara d'aya yaci ace yanzu ka huce da mutuwar saudat, kuma halima nadama sossai ya bayyana a gareta kullum tana yawan samuna da in baka hakuri don haka ina Neman mata alfarma"

Shiru yayi kanshi a kasa shifa ta riga ta fice mishi a rai har ga Allah, sbd son kau da maganan yace
"Mustapha yayi maka maganan wacce yake so ya aura an ce ya turo kuwa a gidansu?"
Murmushi yayi yace
"Ka san Almustapha da kunya, ai yanzu kai matsayin uba kake a garesu har yayyunka mata ma, kayi duk abinda ya kamata mu namu zuwa mu tambayar mishi ne idan komai ya kamallu"

Duk yadda Muhammad yaso ya kwana yaki haka ya tafi, Muhammad na shirin tafiya massallaci sallar magriba kenan aka kirashi da mummunar labari Malam Imam yayi hatsari a hanyar komawanshi Allah ya kar'bi abunshi, iya rud'ewa familyn sun shige shi...

Har akayi bakwai d'in malam Muhammad be dawo daidai ba, da taimakon saudat ya warware ya kar'bi kaddara, bashi da masaniyar abinda saudat take fuskanta a zamansu na kwana bakwai d'in nan, ya de san ta ta'ba samun attack sau d'aya na asthma d'inta wadda ba don Allah ya taimaka Rumasa'u tayi gudun nemanshi ba da be san me ze faru ba har allurai ta sha, ita kuwa fuskantar matsalar mahaifiyarshi take tun bata gama jegon yaron ta ba ake sheganta mata shi ake jefarshi da maganganun da ba kowacce uwa bace zata juri ji.

Har cewa sukayi wa ya sani ko ribar asiri ne shiyasa daga zuwa ya d'auke mata malam, tunda da be je kallonshi a kano ba da be mutu ba, tayi kukan wannan magana sossai sede bata nunawa Muhammad komai ba, bayan kwana goma da rasuwar aka maida Aurensu da halima saboda alfarmar karshe kenan da ya nema daga gareshi, washegari suka koma Kano.

Wani irin zama sukayi marar daad'i Saudat hakuri ya mata yawa yayinda Halima take zazafa abu a ko yaushe tana cikin cutarta, hakan yasa tausayi da kauna kullum Muhammad ke karawa akan saudat tana bashi tausayi matuqa ya rabota da gidansu cikin gata da arziki ya kawo ta inda a kullum tana cikin kunci da damuwa in ba daga Almustapha ko gareshi ba babu inda take samun sauki, gwara goggonshi Asma'a tana sonta amma daga yayyunsu har mahaifiyarshi matarshi da 'ya'yan da yanzu mamansu ta gama hure musu kunne fitsara kala kala suke yiwa saudat d'in idan ba Mustapha ne ya gani ya zane su ba to fa sede ta kauda kai.

GAMON JINIWhere stories live. Discover now