Yace, "Har yanzu baka canza ba kenan?

"Kamar ya?

"Taya za'ayi kace haka? Kasan yadda idan kunyi aure, auren naku zai kasance?

"Abinda zaka ce shine, zaka yi iya ƙoƙarin ka ganin cewa zakayi hakan, zakuyi faɗa kuma zaku yi shiryawa, zakuyi rikici zaku shirya, shin kasan da wannan?

Girgiza kan sa yayi alamar a'a, shima shiru yayi be kuma cewa komai ba.

Yace, "kamar baka gane ni ba".

"Na kasa sanin inda nasan fuskar".

"Taraba? Gassol? Hauwa'u Nilah? Aurenta?

"Tabbas kaine".

Ya faɗa yana ɗan murmurshi.

Yace, "Ina Nilah take? Ko har yanzu ba'a ganta ba?

Jinjina masa kai kawai yayi.

"Nine wanda za'a bawa Bintu. Amma zan yi iya ƙoƙarina na ga cewar ta dawo gare ka".

"Duk abinda nayi maka?

"Ai ita soyayya ba'a yi mata haka".

******

Sanda suka zo gida, Sajjad na ɗaki yaga dawowar Abba ta windown ɗakin sa, hakan yasa shi fitowa dan ya masa sannu da zuwa sai dai me, kafin ya fito daga ɗaki ya zo parlour Daada ya fito, be san da Daada ba sai da ya fito daga parlour kawai ya ja ya tsaya cak, yana kallan Daada.

"Daada?

Ya faɗa a hankali yana tafiya, yana yin wajen su, su kuma suna shiga ciki basu gan shi, sai ji yayi an rungume shi ta baya ya wani ƙanƙame shi gam, juyowa yayi shima ya rungume shi yana bubbuga bayan da alamar rarrashi. Sannan suka shiga ciki, Mama da Ummi har da Anty duk suna parlour, da kallo kowa ya bishi har ya zauna a kusa da Anty yarda take kallan shi da mamaki shima haka yake kallanta da mamaki. Taya hakan ya faru? Kowa yake tambaya a zuciyar sa, kafin ya kalle Abba ya kalli Baba sannan Sajjad.

"Kayi haƙuri".

Sajjad ya faɗa a hankali, jinjina kan sa kawai yayi.

Sajjad ne yayi ta kiran su, ba'a ɗaukan lokaci sai ga su sun zo. Kafin kace me, gidan ya cika maƙil kowa ya zo ganin Daada har ƴan Kano su Abdulmajid da Mustapha suma sun taho, haka ma su Al-ameen da Aliyu duk sun taho, murna de kam wannan familyn yau gani suke babu wanda ya kai su. Inna ce bata nan kuma ba'a sanar da ita ba, a cewar su zai je har Bauchin ta same ta.

*****

Nilah bata tashi sanin cewa tayi kewar yaranta ba sai da ta zo kwanciya ta kasa kwanciya ta kasa bacci, ta rasa ya zatayi, gashi de sunyi waya amma inaaa ta kasa baccin daga ta kwanta zata ji wani abu na mata yawo a jiki na kewar yaranta, basu taɓa raba koda makwanci ba bare kuma aje ga ɗakin kwana.  Yarda ta kasa bacci haka suma yaran suka kasa bacci, har da zazzaɓi sukayi babu abinda suke cewa sai akai su wajen Mammy, koda safe ma kasa cin abinci sukayi sun san bata nan ba kuma yau zata dawo ba. Itama da Ƙaramin zazzaɓin ta kwana haka da shi ta shi gashi babu wani baccin arziƙi da tayi, ga baƙon waje haka ta lallaɓa ta shirya suka fita ko break fast batayi ba, duk da jiyan an raba musu kayan abinci kafin su saba da gari su fara siyan nasu da kan su, anya kuwa ta taɓa ganin ko jin irin kirkin mutanen irin su?
Koda taje haka aka ce mata babu aiki sai ranar Monday da ta san haka ne da bata fito ba, tana juyowa shi kuma motocin sa na danno kai tasan shine saboda a cikin su shi kaɗai ne yake yawo da motoci biyu tasa ta uku.

Tana zuwa gida taga kiran shi dake wayar a silent take bata gani ba sai kiran Ruƙayya da Abdallah, su ta fara kira basu kira ba, ta ajje wayar ta shiga kitchen, jin ƙarar ta yasa ta zuwa kawai ta ɗaga wayar batare da ta duba ba, ta ɗauka ɗaya daga cikin su ne.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now