Yace, "Allah ya kiyaye".

Be jira cewar ta ba, ya juya zai shiga ciki, yaji ana magana kamar ba zai juyo ba sai kuma ya juyo, har kau da kan sa ya kuma juyowa da sauri yana kallon sa.

"Mudansir?

Ya faɗa cike da mamaki, to me ya kawo shi nan wurin? Me ya zo yi? Da me kuma ya zo? Ganin sa na magana da Inna da alama gaida ta yake kuma cikin girmamawa yasa shi wucewa batare da ya kuma sanin me ake cewa ba.

"Ɗan samari naji bayanin ka, amma yanzu haka zan tafi Bauchi ne domin auren ita wacce kake so ɗin".

Sunkuyar da kan sa yayi, yana jin wani irin zafi da raɗaɗi a ran sa, shin daman wai haka so yake?  Ya tambaya a ran sa, ada shi idan aka ce zai yi so wata yarinya tsab zai iya yiwa mutum lahani amma a yanzu kam ya yarda ya kuma amince, ya kuma fara shiga jeren cikin sawon masu jarabawar so a rayuwar sa. Tabbas yasan a da baya san yarinya sai idan yasan auren jari zai yi bi ma'ana baban yarinyar na da kudi, amma banda a yanzu kuɗin be dame shi ba kawai yarinyar yake so, gashi kuma zai rasa ta.

Ji yayi an dafa bayan sa hakan yasa shi juyowa a hankali yana share ruwan da yaji a idan sa ashe hawaye ne be sani ba, Inna kuwa  ta jima da tafiya batare da ya sani ba. Kallan sa yake, kallo na kamar na taɓa ganin ka, kallo kuma na ina na san ka? Sajjad dake kallan sa ya ɗan sakar masa murmurshi tare da miƙa masa hannu.

"Sunana Ahmad Sajjad or Sajjad Ahmad".

Ɗan murmurshin shima yayi yana miƙa masa hannu.

"Mudansir Al-Hussain".

"Nace ko zamu ƙara sa ciki naji dame kake tafe".

Ya faɗa yana nuna masa hanya, babu musu yayi gaba alamar tafiya hakan yasa Sajjad shiga gaba ya wuce, part ɗin sa ya wuce da shi ya zauna sannan ya kawo masa ruwa da abin sha ya ajje masa tare da zuba masa a cup ya miƙa masa.

"Nagode".

"Zan iya sanin meke tafe da kai?

Riƙe abin hannun sa yayi yana sha ahankali kafin ya fara magana.

"Bansan ta ina zan fara ba".

Shiru ya ɗan yi.

"Ta cewa ni saurayin Bintu ne? Ko kuma ta cewa nine me san Bintu?

Ɗan murmurshi Sajjad yayi.

Yace, "Ina kuka haɗu da Bintu?

"A gidan radion da take aiki, anan muka haɗu".

Jinjina masa kai yayi alamar na gane.

"Mun fara soyayya da ita, duk har yanzu bani da tabbacin cewa tana so na ko kuwa bata so na, amma abinda nasani shine ina matuƙar san ta, koda bata mun magana ba, idan na gan ta ya wadatar, san da nake mata bana jin na taɓa jin irinsa akai na, ina jin zan iya sadaukar ga komai nawa wa ita".

"Sai jiya take sanar da ni cewa ita an rigada an mata miji a gida kuma baza ta iya cewa a'a ba".

Shiru yayi be ƙara cewa komai ba.

"Me yasa kake san ta?

Besan sanda yayi murmurshi ba.

Yace, "Wannan tambaya ce mai wahala, amma abu ɗaya zan iya ce maka ya ja hankalina gare ta shine fara'ar ta, da mai da komai ba komai ba".

Murmurshi Sajjad yayi.

Yace, "Bani da tabbacin kana san ta ko baka san ta, amma a yadda ka ce fara'ar ta, idan ka aure ɗin zaka ci gaba da sanya wannan fara'ar a fuskar ta har ƙarshen numfashin ka?

Kallan Mudansir yayi.

Yace, "Zan yi haka".

Wannan karan kasa riƙe murmurshin da Sajjad yayi, sai da ya yi murmurshi sosai.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now