"Sir! Ance na kawo maka kasa hannu".

"Waye ne yace ki kawo min?

"Rabi'u messenger ne".

"Ohh! Anyi haka jiya yace idan nasa hannun daman ke yake kawo wa ko?

Ɗaga tayi.

"Shine yace zaki kawo nasa hannu. Wallahi sam na manta yi hakuri zauna mana".

Ya faɗa yana ƙara nuna mata wurin zama, looking so innocent ta sami waje ta zauna, a ɗan ɗosane ma ta zauna irin ta nuna tana da tarbiyyar nan, tana kallan ƙasa shi kuma yana sa hannu yana satar kallan ta, yarda ta wani nuna tana da tarbiyya ba ƙaramin burge shi tayi ba. Abu ta fara nema a jakar ta, kamar tana neman wani abu, be san kuwa kakan flash din take nema ba, wanda zai yi dai-dai da wanda aka bashi, aikuwa ta samu, har kala da size sak iri ɗaya babu wani banbanci. Ta zaro ta riƙe gam a hannun ta, ganin kamar ya dena satar kallan yasa ta yasa hannu zata ture takardun dake kan desk ɗin su faɗi aka kira shi a waya, ganin mai kiran nasa yasa shi ɗauka yana barin wajen, batare da wani  jinkirtawa ba kuwa tayi wuf ta sake ta sauya wanda ko sallamae da yake yi a waya be gama bere ya juyo yana kallon ta hakan ta faru, aikuwa yana amsawa ya juyo yana kallan ta, sai wasa take da hannun ta.  Yana gamawa ya zo ya ƙara sa sa mata hannun ya bata, harda ɗan durƙusawa ta amsa tana godiya sannan ta fita, ya jinjinawa kamalar ta tarbiyyarta ko ƴar waye ta fito daga gidan mutunci haka ma mijin ta yayi dace da ya same ta a matsayin mata.

Tana fita ta sauke wata irin ajiyar zuciya kafin tayi sauri ta maida komai a wurin sa, sannan ta hau system tayi copy guda uku, ita bata ga komai ma da aka tattauna ɗin ba, kodan ita ba ganewa na zatayi ai, har ake wani neman sa da muhimmanci, taɓe baki tayi kafin tayi masu shaidar da ita kaɗai zata gane sannan ta watsa biyu a jakarta ɗayan kuma tayi masa kyakkyawan tanadi a office, yayin da ta fara tunanin yarda za'ayi ta maida masa ɗayan batare da ansani ba.

~~~~

Jiddah ta shigo cikin companyn tana wani irin ware ido ganin wuri mai kyau, sai kalle-kalle take abun ta, batare da yi la'akari da ina take jefa ƙafar ta ba, sai ji tayi karo da mutum ta ɗago kai mana taga basamuden mutum na kallan ta, ai tuni idan ta ya ciko da ruwa tana ƙara ware ido tana kallan shi, kafin ta kai kallan da sauran sojojin da suke kallan ta, ƙara damƙe jakar ta tayi idan ta nayi ƙwale-ƙwale. Ɗaya daga cikin sojojin ne, yace.

"Ke! Me kike anan?

Jin wani irin mashahurin fitsari tayi ya zo mata, tuni ta fara matse ƙafa, tsawar da suka daka mata ne yaja hankalin Sajjad ya juyo yana kallan yarinyar da ta kafe Sojan da yayi mata magana da ido tana kallan shi, wayar da yake yi ya kashe tare da dawowa kusa da ita, ya durƙuwa a gaban ta, haɗa idan da sukayi yasa shi wani irin lumshe ido da be shirya ba, ta ƙure da kallo tana kallan sa haka kawai taji kamar ta san shi.

"Me kike yi anan?

"Fitsagi nake ji".

Ta faɗa hawaye na zubo mata, hannun ta ya kama, ganin kamar basa sauri yasa shi ɗaukan ta ya riƙe, yayin da ita kuma ta saƙolo da hannunta tana cigaba da kallan sa shima ita yake kallo yana kallan hanya, har suka hau Elevator zuwa hawan ƙarshe ya shiga office ɗin da aka gyara masa, ya kai ta toilet ya ajje. Shi kuma ya fito ya zauna a kujera, shiru shiru bata fito ba, shi kuma be shiga ya duba ba, sai ji yayi tana cewa.

"Na gama".

Da irin ƙarfin nan, to be rufe ƙofar ba, hakan yasa shi jin abinda ta faɗa, ko ya rufe ma wannan ihun da tayi yasan ai zai ji, da mamaki ya tashi yana mamakin to me tayi? Karde kashi tayi? Yana shiga kuwa ya tarar kashin tayi, girgiza kan sa yayi za wanke mata.

Tace, "Mammy sai ta faga wanke hannun ta take wanke min".

Kallan yarinyar yayi sosai yana so yaga no wani abu daga jikin ta amma ya rasa ganewar, wanke hannun nasa yayi kamar yadda ta buƙata sannan ya wanke mata yayi flushing.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now