Bata da me bata amsar nan hakan yasa ta ci gaba da aikin, sai dai kuma kuzarin ta ya ragu sosai da sosai sakamakon sunan sa da tagani duk da cewar komai zatayi tana maƙale da shi a  zuciyar ta, bata taɓa cire shi ba har yau kuwa, sai dai ita bata sani ba, ko yana nan? Koma ya manta da ita? Wannan tambayar kawai yake yiwa kanta wanda take bawa kan ta amsa a take cewar daman ba san ta yake ba ƙila ya manta da ita, da wannan take samun damar cire tunanin sa, more especially idan ta tuna irin zaman da sukayi.

Hannu ta gani an miƙo mata tissue hannun tabi da kallo har ta sauke shi kam Mustapha dake kallon ta, da ace kamar su ɗaya wannan ai bazata gane su ba, saboda kayan su iri ɗaya ne bata ga banbancin dake jikin su ba, duk da cewa kuwa suit ce suka sha amma kalar iri ɗaya ce haka ma design ɗin iri ɗaya ne hatta ƙamshin turaren nasu iri ɗaya ne".

"Uhmm?

Yayi gyaran murya, a hankali tasa hannu ta karɓa, ashe wai kuka take oho bata san tana yi ba.

"Idan kina tunani haka taya zaki gudanar da abinda ke gabanki?

"Uhmm?

Ya faɗa da alamar tambaya, sunkuyar  da kanta ƙasa tayi, bata da abinda zata faɗa ita kam, ɗazu ɗayan ya tarar ta tana bacci yanzu kuma wannan ya tarar ta tana kuka ita bama wannan ba duk haɗuwar su sai ta ji gaban na wani irin faɗuwa gudun zuciyar ta ya ƙaru, ko rashin sabo ne oho. Bata san ya fice ba sai da taji ƙamshi ya ragu a office ɗin sannan ta lura da baya nan. Ajiyar ta sauke sannan ta ture tunanin a ranta tayi abinda zata yi.

*

"Mammy jiya baki je ɗauko mu ba yau ma kika manta da mu".

"Jiddah kiyi haƙuri mana aiki ne ya min yawa shiyasa".

"Mammy aiki kika samu?

Abie ya tambaya. Ɗaga masa kai tayi tana cigaba da naɗe musu kaya.

"Mammy ni kuwa kinsan me?

Girgiza kai tayi alamar a'a.

"Soja nake so na zama".

Jiddah tace, "Wanne soja? Salan kike hagbe ni?

Yace, "Ke bazan halbe kiba".

"Taab ni kuwa mai bada labarai zan zama, yagda zan ke zuwa ana nuna ni a TV".

Ta faɗa tana wani washe wawulan ta. Ita abin nan nasu dariya yake bata, dukan su ba R ɗin kirki ba, shi L ita kuma G, bata ga ranar da za su dena wannan R ɗin ba, idan ba sabawa kayi da su ba lalle ka gane zancen su ba idan suna yi da R a ciki, kuma baza'a gyara musu ba. Idan suna wasa ko suna zance takan zauna tayi ta kallan su, ada sanda suna jirirai sai Sajjad da suka fara girma kuma sai suka biyo ta yanzu da suka girma sai suka biyo wasu kammanin da bata sani ba, Ita dai anata Family ɗin babu wasu masu kamar su.

"Mammy mu sai yaushe ne Abban mu zai dawo?

"Nima Mammy ina so naga Abban mu".

Jiddah ta fara magana kafin Abie.b

Tace, "In Sha Allah zaku ga Abbanku".

"Kuma dani yake kama?

"Dalla dani yake kama..."

Bata gama rufe baki ba aka ɗalle bakin nata, ta ɗaura da yi mata, daga nan tayi fushi aka je bayan ƙofa aka raɓe a haka bacci ya ɗauke ta. Basu cigaba da maganar ba, ganin sunyi bacci su duka yasa ta zuwa ta ɗauko ta tayi musu addu'a sai da ta gama naɗin kayan ta fito da kayan da zasu gobe da komai sannan ta tanadi abinda zata dafa da safe gudun kar azo a makara.

~~~~~~

Kyakkyawar mata ce wacce ta amsa sunanta na mace, mai ji da kuɗi da kuma wadata. Tafiya take cike da nutsuwa gefen ta kuma yarinya ce da bazata wuce shekara goma ba, kallo ɗaya zaka yi wa yarinyar kasan bata da lafiya saboda yarda Mahaifiyarta ta riƙe mata hannu ta ja ta jikin ta suke tafiya.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now