Chapter 17-18

103 2 0
                                    

*LADIDIN K'AUYE*

Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*


*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Episode:* 17_18

_____Dariya ma tabashi ,seda yayi mai 'isarshi kana yace "kin mance da masoyinki ko ?kin kulashi tayi,sekuma taji hawaye na zubo mata .
Ammar ne yaturo mata abincin kana yace kici abinci " dama kince kinfison indomie ,kuma ita na dafa miki .
Kici kiji girkin Ammar d'inki "cikin masifa tace tirr !da hali 'irin 'naka ,tuno halinta na da lokacin da take k'auye tayi ,shirin mugunta take yimai .

" Tace to yanzu ka maidani gida" wani 'irin kallo yayi mata, ina wanan brother naki mara mutunci "cikin fusata tace bangane ba ¿" dariya yayi mata irin 'na y'an duniya yace manta.
Jiyo k'arar wayarta tayi dake hand bag d'inta ,zata d'auka Ammar ya kwace wayar ,cikin masifa tace wlh koka bani wayata kokuma kayi nadama"yayi receive din kiran kenan , zeyi magana da alamu han,kalinshi na kan wayar yana shirya iskancin daze fad'a musu .
Ficewa yayi a parlor yana tunanin ai bazata fice ba".

Bud'e k'ofar tayi a hankali tayi waje babu hijab a jikinta babu takalmi, lek'awa tayi taga babu megadi ,ta bud'e k'ofar da gudu ta ruga tanata gudu ,tarasa inda zata nufa .
A wata anguwa mesuna rikos ta tsaya tana jiran mutane ,hango wani yaro tayi ze shiga wani gida."

Azama tayi ta isa gurin yaron kana tafara tambayar shi ,dan Allah yaro daga nan zuwa 6ukur park G.R.A dan Allah nawa ne ? yaron yace" masu napep zasu kaiki a d'ari biyu ,godiya tayi mai tacigaba da tafiya.
Tana cikin tafiya ne ta hango wani me adai,daita yace hajiya ina zuwa "anguwar ta fad'amai, yace " tashiga su tafi ."

Sunyi tafiya me nisa sanan suka iso anguwar ,a lokacinne tafara gane anguwar tasu,nuni tayi mai da ga'gidan can "barinje in kar6o maka kud'inka ."

Me napep ne yashiga yimata masifa yana cewa dama kinsan bakida kud'i kika shiga to wlh inan a nan kishiga ki fito ".
Tana shiga taci karo da Jalal ,yana ganinta yahau tuhumarta" Ladidi cikin jin tsoron abinda ze biyo baya tace dan Allah brother dari biyu zaka bani 'inbawa me napep "Jalal ne yace gashi mik'a mai ".
Fita tayi tabashi ya tafi,tadawo cikin gidan.
Bata sami Jalal din waje ba ,tashige cikin gidan ,tana shiga tayi sallama ta hango momy da Humaid da Jalal da ,dady saboda baije aiki ba.
Tunda dady'ya hangota yafara yimata wani kallo tana shigowa ,Humaid ya mik'e ya wanka mata tagwayen maruka har biyu,babu wanda yayi 'yink'urin hanashi .
Cikin 6acin rai Humaid yace gidan ubanwa kikaje" banza mara tunani" Ladidi da tarasa mai zatace tadubi dady da tun shigowar'ta yake kallon ta 'taje har gabanshi tana kuka tace wlh dady ba wani guri naje ba "ya d'aga hannu zekai mata mari momy ta rik'e hannun tace katsaya muji abinda zatace" ai alamun mai gaskiya ya fita da ban .
Dady ne ya saurara,yana jiran mezatace cikin murya mai ban tausayi Ladidi tace wlh dady dama cemaka nayi zani gurin kitso ,to bayan an yimin muna cikin dawowa da driver mukaga wasu ,bak'ak'en motoci sun zagayemu "shine na fita inyi musu magana ,naji anturani cikin mota an rufemin fuskata ,an kawoni wani gida kuma bansan inda jakata take ba " momy ce tadubi Ladidi tace to d'azu da Jalal yakira a wayarki waye ya d'auka? cikin she' shek'ar kuka Ladidi tace lokacin da aka shigo dani cikin wani gidan shine naga babu kowa a gidan ,cankuma naji motsin,fitowar mutum.
Bayan mutumin ya fito shine , naji alamun ana kira a wayata ,ashe wayar na gefena "nazo d'auka naji an kwace wayar" da mutumin yashige ciki nikuma na gudo ".

Dady ne ya jinjina lamarin yace " amma kinsman shine ?atsorace tace wlh dady bansan shiba ,su Jalal da Hunaid 'da suka zuba mata ido suna kallon ta ,momy tace Allah sarki daughter Allah yadad'a tsareki "kowa ya amsa da amin.

Washe gari dady 'yakira nalam Adamu ,suna cikin wayar ne naji dady yace" yaya so, nakeyi muhad'a Khadija da Humaid aure ,cikin farinciki malam Adamu yace" wanan ai abin murna ne, amma naji dad'i sosai .
Dady ne yace"abinda yasa nakawo wanan shawarar saboda muk'ara k'arfafa zumunci ,malam Adamu yace"karfa kadamu ,sukayi sallama.

"Bayan dady 'yakoma gida yasamu momy da maganar ,itama tayi farinciki sosai sedai tana ganin ,anya Humaid baze wulak'anta Khadija ba ? ".

Saurin kawarda tunanin tayi ,dady da yalura momy tunani takeyi yace" tunanin mekuma kikeyi ,fara'ar dole momy ta k'ir' k'iro tace" duk acikin farinciki ne ".

Yau kawanansu dady biyu da yin maganar auran su Humaid, dady ne yatarasu a parlor'nshi saboda ya gaya musu,halin da 'ake ciki ".

Tunda Humaid yaji wanan kyakyawan albishir ,yadinga farinciki .
Ladidi dajin hakan taji tsoro ya shigeta, saboda tana tunanin,halin da zata shiga ".

Washe gari dady ,yace" ansa biki sati biyu,momy ce tazaro ido tace"sati biyu fa alhaji? dady cikin tuhuma yace "kina nufin yayi kad'an ko¿" eh momy tace.

Dady ne yace"muyi fatan Allah ya kaimu kawai , Ladidi ce kwance a d'aki tana tunanin halin da tashiga, Allah ma yatemaketa Ammar d'in beyi mata komai ba,tunowa da wayarta tayi kukane ya k'wace mata ,tadinga cewa"wlh nayi nadamar saninka Ammar ".
Bayan sati d'aya ,yau biki saura sati biyu ,momy ce take ta shirya Ladidi musamman takira wata k'awarta daga Maiduguri".

Tunda tazo aka fara yiwa Ladidi dilka dasu magunguna ,tun Ladidi nashan 'na marmari har tadawo k'in maganin,se momy tayi da gaske take sha .
Tadena fita ko da harabar gidan'ne , daga d'aki se sallah ,wani haske Ladidi tayi ,dama fara ce gashi kuma ankuma gyarata.
Tunda akasa biki ango Humaid ya dena zama ,shikuwa Jalal kulum cikin siyayya yake".

Yau biki saura sati d'aya, bak'i ne suka fara zuwa na kusa dana nesa ,Inna hauwa ma ta iso itada malam Adamu ,se dangin momy da suka iso saboda shirye shiryen biki".

A yaune lahadi wata k'awar Ladidi tazo tayi mata make up saboda tanada shago, kwaliyar hausa day akayi mata ,duka k'awayen sunsa" farar riga dakuma zanin atamfa da suka fitar anko ,DJ' Jalal ya d'auko musu ,kasancewa gidan yanada fili ".

Bayan Amarya da ango sun fito ne DJ yace " ga Amarya nan itada angon ta ,please kutafa musu "bayan angama tafinne D J ,ya sake wakar da akayi musu ,Humaid 'da baki yak'i rufuwa ya ruk'o hannun Ladidi suna rawa ,sauya wak'ar akayi suka nemi guri suka zauna .
DJ ne yace munason muga nera biyar a gurinnan Jalal yaje yasa dubu d'aya, ana cikin haka ne momy ta fito taja Ladidi tace asa musu wak'ar da 'akayi musu ,Ladidi kanta a sunkuye suke rawa da momy ba k'aramin kud'i momy ta zuba ba.

Ana cikin rawa y'an uwan momy suka fitoda ,su goruba magarya taura aduwa se fate wanda yaji kashi a takeaway dakuma dambu ,kai kowa ya yaba wanan shiri da akayi ,anyi taro lpy an tashi .
Washe gari kuma za,ayi ,kumbo day fans kuzo kuga k'ayatuwa da gurin yayi ,tunda aka fara kumbo ake jiran amarya ,tana can anayimata kwaliya material ne a jikinta me tsada sekuma head d'in data d'aura kasancewar milk ne material d'in ,ta d'aura pink head sekuma takalmi shima pink and milk ,woo gaskiya 'amarya tafito sosai ga k'afar tasha lalle ".
Humaid ne yashigo yasa shadda pink hula milk wow shimafa 'angon ya had'u .
Momy da takejin farinciki tashigo da turare a hannunta ta fesawa Ladidi takuma fesawa Humaid sega y'an uwan momy nan sun shigo suna gud'a.....✍️✍️

Mom Islam

Você leu todos os capítulos publicados.

⏰ Última atualização: Oct 09, 2023 ⏰

Adicione esta história à sua Biblioteca e seja notificado quando novos capítulos chegarem!

LADIDIN ƘAUYEOnde histórias criam vida. Descubra agora