Chapter 5-6

19 2 0
                                    

*LADIDIN ƘAUYE.*

_funny & love story._

      

_{MOM ISLAM}._

5-6

Humaid yasa shadda fara shi kuma jalal k'ana nan kaya ne a jikin shi Ladidi ce ta rik'e baki shagon da take kusa dashi ta shiga kana tace "dan Allah me manja samin a hannuna me manja ne ya dubeta kana yace "ke baki da hankali ko¿ LADIDI ce ta dubi me manjan kana tace "zaka ga aikin masu hankali roba ta hango a can waje zuwa ta yi ta d'auko robar shidai me manja yana kallon ta be ankara ba ta dumbula robar cikin manja .

Me manja da yaga barnar da LADIDI tayi mai  mik'ewa yai kana ya nufo ta da niyar kai mata mari.

Ya d'aga hanu ze mare ta yaji an wanke mai fuska da manja sakinta yai kana ya nemi gurin zama .

LADIDI kuwa ganin haka ta kuma dum bular manjan tayi gaba .

Hango su Humaid tayi a gindin wata bishiyar mangoro suna hutawa .

A hankali ta tako  kana ta zagaya ta bayan su inda bazasu ganta ba saboda bishiyar k'atuwa ce .

Juye manjan tayi a rigar Humaid ta baya sunata hira basusan abinda ke faruwa ba a jiye robar tayi a gefe .

Hango cinnaku tayi da yawa d'auko biyu tayi tasawa Humaid a dede gurin zaman shi kuma d'auko biyu tayi kana tasawa Jalal a daidai saitin da ya zauna.

Tashi tayi taje wani shagon da ake siyarda yar bebi jitayi anata ihu Humaid ta hango yanata tsalle shima jallal d'in tsalle yakeyi a tak'ai ce dai babu me temakon d'an uwansa.

Sun rasa inda za suyi aikuwa suka zuba a guje .

Kamar mahaukata Jalal ne yace "Humaid wlh bayanka manja .

Zaro ido Humaid yayi kana yace "kai k'yaleni bata manja nakeyi ba.

Mutane sa kallon su suke ta famanyi,  ita kuwa LADIDI barin gurin tayi dan karsu ganeta da k'yar suka gane hanyar gidan malam Adamu saboda zuwansu na biyu kenan .

Da gudu su ka shige cikin gidan inna hauwa tanajin an shigo gidan da gudu bata tsaya ganin kosu waye ba itama ta ruga d'akinta da gudu.

Su Humaid ne suka shige d'akin da malam ya basu wanan na ihu wancan na ihu se zuwa can anjima ya lafa musu .

Humaid ne ya hau tattaro kayansu yana had'awa guri d'aya jalal ne yace "Humaid me zakayi da kayannan .

Humaid ne ya kalli jalal kana yace "insha Allah gobe zamu bar wanan k'auyen .

Jalal ne ya tuna da gudu da suka dinga kwasa ya kyalkyle da dariya .

LADIDI ce ta fito d'auke da tiren tuwo da miya malam adamu ne da malam musa suna zaune suna hira kasa kunne tayi taji suna cewa ai bak'in gidana gobe zasu tafi .

Tsalle LADIDI ta buga kana ta je gurin kayan wasan ta kusa da bishiyar kuka .

Dakin YADIKKO ta nufa samun YADIKKON tayi tana sallahr isha I .

Fitilar d'akin ta d'auko kana ta koma gurin kayan wasan .

Farar k'asa ta d'auko taje kan dutse ta dan dak'ashi seda yayi laushi.

Ta kwashe shi a leda  d'akinta ta nufa mudubi ta samu .

Ta lakato mai me yawa ta shafa a fuskarta ta d'auko farar k'asar da tadaka shima ta goga a fuskarta, tunawa tayi ai batasa kwallin ba d'auko kwalkin tayi  ta zana baki a bakinta takuma zazzana a duka fuskarta  kayanta da suka yayyage ta d'auko .

Riga tasa me yagaggen hannu se wandon atamfa shima ta gwuiwa ya yage .

Dan k'aramin gyalenta ta d'auko ta kuma nan nad'ashi a kanta .

LADIDIN ƘAUYETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon