Chapter 15-16

22 1 0
                                    

*LADIDIN K'AUYE*




*Episode:* 15_16

_____gado tafad'a taci gaba da rera kukanta a yanzu ko san taga Humaid batayi "misalin k'arfe shida na yamma tafito zuwa ,kitchen tasamu momy tagama komai sedai jera abinci a dining, temaka mata Ladidi tayi suka k'arasa.

"Washe gari ammar yakirata a waya, yake gaya mata tazo tarakashi gidan su k'anwar momyn'shi " cewa tayi zatazo amma seta tambayi momyn ta ,cikin farinciki ammar ya sa aka ,gyara gidanshi aka feshe gidan da turaruka masu tsada.

Washe gari Ladidi takira Ammar a waya tacemai yazo ,misalin k'arfe sha biyu na rana yazo ya d'auketa ,jin haka ya buga tsalle yana murna" suna cikin haka ne yake tambayar ta ,wane colorn abinci tafiso?dariya tayi kana tace indomie "cikin jin dad'i yace to karki damu drinks fa ?kowanne tace ,sukayi sallama .

Washe gari misalin k'arfe sha d'aya na rana Ladidi tagama komai tasami momy take gaya mata zataje gurin wankin kai " momy ce tace kije ki tambayo dadynki tunda yana gida.

Da sallama tashiga parlour n dady ,samunshi tayi yana waya bayan yagama ne ta gaishe'shi cikin ladabi ya amsa "sekuma ta sunkuyar da kanta k'asa dady ne yace Khadija meyafaru?cikin jin nauyi tace dama inason zuwa gurin kitso ne" dady ne yace to gashi su Humaid basanan ,amma kisa driver ya kaiki" to tacewa kana tamik'e zata fita.
Kiranta yayi ,yabata kud'i ,godiya tayimai ta fice ."

Zuwa tayi parlourn momy tagaya mata dady 'ya barta kuma yabata kud'in kitson"nasiha momy tayi mata daganan ta d'auko hijab d'inta ta fice, taje tayiwa driver magana tafad'a mai 'inda ze kaita "

Bayan sunje suna hanyar dawowa suka ,hango motoci bak'ak'e sun zagaye su ,babu hanyar da zasu ,wuce "

Bude murfin motar tayi ,
baba driver ne yace"wallahi Khadija karki fita, Ladidi 'da hankalin ta ya tashi tace karka damu yanzu zan dawo ficewa tayi a motar, ta nufi gurin masu bak'ak'en motocin'nan bata hango kowaba acikin motar ,zata juya ta koma ,tasu motar "taji an janyota an turata mota,baba driver ne ya fito yana salati kafin yakai gurin masu motocin ,tuni suka wuce da gudu ,Baba megadi yara yazeyi ,mezeje ya fad'awa su Alhaji " driving yakeyi amma hankalin shi baya jikin shi ,haka ya iso gidan .
Momy ce dake shirin fita anguwa taji Horn d'in baba driver ,bayan yafito daga motar ne ya durk'usa kana yagaida momy'mom daketa lek'en ta ina Ladidi zata fito "baba driver ne yace hajiya wlh tsau'tsayine yafaru da Khadijan " momy da bata,gane inda yadosa ba tace mekake nufi "koba tare kuka fita da khadija ba ¿" shiru yayi cankuma yace wlhi Allah hajiya muna cikin tafiya mukaga wasu a wata bak'ar mota ,yabata labarin inda akayi har cemata da yayi karta fita.

"Cikin tashin hankali momy ta ,kalli baba driver tace kuma ka iya dawowa saboda ragon azanci baka bisu ba ko"

"Kana ganin kai rayuwar ka tafi ta kowa muhummanci .
Shiru drivern yayi kana yafara da ayi hak'uri hajiya ,momy cikin fushi tace ai wlh zakayi dana sani bari alhaji yadawo .
Waya sani ma koda sa hannunka a tafiyar da 'akayi da ita".

" cikin rud'ani driver yace ,wlhi hajiya babu sa hannun' na momy ce cikin fusata da 6acin rai tace shot up your mouth .

"Tace wlh idan kasake magana senayi report d'inka gurin police "zaro ido driver yayi kana yabar gurin ,momy da hankalin ta yagama tashi tarasa wace kalama zata ,fad'awa dady idan yadawo".

Shigewa part d'inta 'tayi ganin Humaid a ,zaune yasata ware ido tace" wato kai bakaji tashin' hankalin dake faruwa ba"Humaid da hankalin shi yatafi gurin TV a tsorace ya d'auki remote ya ,kashe kallon kana yamaida hankalinshi,gurin momy 'yace momy meke faruwa?"

Momy da idanuwan'ta suka ciko da hawaye ,tashare tadubi Humaid tace "tunda Khadija ta fita wlh ba,a gantaba a tsorace Humaid yace" bangane ba momy .
Momy na kuka tabashi labarin da 'driver yabata, a zabure Humaid ya mik'e ya'yi hanyar fita waje ,momy da keta kiranshi yak'i juyowa bare ya saurareta.

Kai tsaye gurin baba driver yanufa ,tunda baban ya hango shi ya fara salati,saboda dama basa shiri da Humaid ."

Cikin azama Humaid ya ,nufi gurinshi yana zuwa ya cakumo wuyar 'rigar baba driver yace gidan uban wa kakai marainiyar Allah "baba driver daya gama tsorata yace yaro " karka manta shekarata goma ina aiki a gidannan kuma ba,a ta6a samun matsala ba, seyanzu ne zance zan cutar da wani".
Humaid da bayajin ko mai da baba driver yake cewa yadinga ball dashi ,har seda momy tajiyo hayaniyar su tazo tana yiwa Humaid fad'a"

"Hak'uri tabawa drivern,ta ruk'o hannun Humaid suka shige ciki , tana cikin yimai fad'a sega Jalal nan ya k'araso ,ganin fuskar momy da Humaid babu fara'a yasashi k'arasowa da sauri yana momy meys faru " Humaid cikin k'unar zuciya yace Khadija cefa driver ya 6atar da ita "a zabure Jalal ya mik'e yace shine bro ka barshi? "Momy ce tadubi Jalal tabashi labarin da driver yabata Jalal yace wlh k'arya yakeyi" momy cikin d'aga murya tace zan sa6a muku "kubari dadynku yadawo ."

"Da daddare dady 'yashigo da fara,arsa ,rungumo momy ,yayi seyaga tak'i yin dariya alhalin ba haka tasaba yimai ba" duba fuskarta yayi kana yace hajiya meke faruwa naga kin sauya cikin tashin hankali da muryar da taci kuka ,tace Khadija .
Dady ne yace meyafaru da Khadijan¿ momy tace barin kirayo maka driver "mik'ewa tayi ,dady ganin momy tayi waje yasa'shi mik'ewa tare suka fita .

Tunda suka isa parking space d'in momy take ta k'awalawa driver kira ".
A hanzarce ya fito cikin ladabi ya gaida dady ' dady ne yace meyafaru ne da Khadija ?"
Cikin fad'uwar gaba driver yabawa dady labarin abinda yafaru dasu .
Kid'imewa dady 'yayi yahau fad'a ,yana cewa wlh baku kyauta minba meyasa ba'a kirani a wayaba "momy da kuka ya ku6uce mata ,takasa magana ,dady ne ya d'auki motarshi ya nufi police station yayi musu bayani ".

Tare dakawo photon Ladidin dakuma kalar kayan da tasa .

Bayan su momy sun dawo gida,suna zaune da safe ,suna kallo a TV sukaji ana cigiyr Ladidi momy jitayi hawaye sun zubo mata,dady kuwa hak'uri yake bata amma shima yanajin cikin zuciyarshi babu dad'i".

Tunda Ladidi ta 6ata momy tadena jin dad'in aiki sosai ,seda tasa aka d'auko mata yar aiki .

*WAYE YA SACE LADIDI*

Tunda suka sata a mota suka rufe mata fuska da bak'in wani abu, ihu takeyi 'iya k'arfinta amma babu wanda ya kulata, jitayi an d'auketa ana tafiya da ita ,daganan taji an sauketa an zaunar da ita an wurgo mata Jakarta .
Takai minti talatin a haka can kuma taji an bude mata ido,ganin ta a wani k'ayataccen parlor yasata sakin kuka tana, kiran momy " Ammar ne yafito d'auke da plate na abinci a wani farin trai me adon flowers masu kyau.
Ajiye mata yayi a gabanta ,nunashi tashiga yi da 'dasha shiyar muryar ta 'tace Ammar wanan ce soyayya ? ta k'ara dacewa wlh ka cuci kanka kuma tayarwa da iyayena hankali da kayi se Allah, yayimin sakayya .✍️✍️✍️

LADIDIN ƘAUYEOnde histórias criam vida. Descubra agora