Chapter 11-12

20 2 0
                                    

*LADIDIN K'AUYE*

Follow me pls my lovely fans zaku sami complete na littafaina da kuma Ladidin ƙauye a wattpad 👇
https://www.wattpad.com/user/Momislam2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invit



*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Episode:* 11_12

_____washe gari ,inna Hauwa ta shirya malam Adamu ya aiko jalal ya kirawo ta dan bayason suyi tafiyar dare shigowa inna Hauwa tayi ta sami guri ta zauna dady ne shida malam Adamu suna hira dady ne yace ina Ladidin inna Hauwa ce ta kwalawa Ladidi kira segatanan da gudu ta k'araso dady ne yace sannu baiwar Allah ina kwana tace bayan ya amsa ne malam Adamu yadubi Ladidi kana yace yanzu ,zamu tafi amma inna tagaya miki anan zaki sauna ko ¿"Ladidi tana murna tace eh ta gayamin malam Adamu ne yafara yimata nasiha da fad'a akan tarbiya dakuma tayiwa su dady biyayya to tace musu daganan suka mik'e Humaid ne da Jalal suka shigo suka durk'usa suka gaida malam Adamu shida dadyn su ".

Mik'ewa sukayi sega momy nan d'auke da wata leda mekyau ta mik'awa inna Hauwa godiya inna Hauwa tayi mata daganan suka fito waje" Ladidi ce ,tace inna yaushe zaku dawo"ina Hauwa ce tadube ta da alamun tausayawa tace karki damu zamuzo dubaki Ladidi bata nuna 6acin raiba saboda tana son zaman birni "Humaid ne yatada mota suka shiga dady ,yaciro dubu goma yabawa malam Adamu godiya malam Adamu yadinga yiwa dady daga nan suka fice daga gidan suka zarce tasha suna zuwa suka shige mota se kano.

Ladidi ganin babu wanda tasani acikin gidan yasata yin sanyi gashi yunwa takeji tarasa inda zatasa kanta tagumi tayi seta fara tuno inna Hauwa da acan k'auyen,nne da ko tuwo ne taci sau biyu su nan idan aka bawa mutum shayi da burodi abincin rana se k'arfe d'aya na rana" dady ne yazo wucewa yaga Ladidi a kan dakalin wucewa palon tazuba uban tagumi "dadyne yadube ta kana yace Ladidi meke faruwa ne Ladidi da tarasa abinda satace seta k'ak'alo karya tace dama narasa d'akin dazan shiga ne dady ne yarik'e hannunta ya nuna mata d'akin da suka kwana jiya yace nanne d'akin ki ,kinji to tace mai shikuma yafice daga part d'in ,nata.

Tunda tashiga taji kamar an karo yunwar ne juyi tadingayi a katifa yar aikin gidan ce wato ummi tashigo da tiren abinci doya ce da miyar k'awai se lemon gora fanta da sauri Ladidi ta diro daga kan gadon ta kar6i abincin ita ko ummi mamakin ci ,irinna Ladidi takeyi " ko wanke hannu batayi ba tadinga tura doyar tana kur6ar ruwa seda taciye duka sanan takoma kan miyar kwan tana ta lasa tarasa miyar menene amma dai koba komai tayi dad'i tak'yar ta mik'e tanufi bayi kashine ya matseta seda tashiga ta tuna tunda suka zo batayi kashi ba seyau lek'a bayan gidan tadingayi kozataga masai "ina sewata kwalba fara mekamada kujera sekuma baho a gefe shima na kwalba .

Ihu ta kurma saboda kashi na neman zubo mata da gudu momy tashigo d'akinnanta taduba bata ganta ba k'wala mata kira tayi momy ce taji Ladidi takuma kurma ihu k'ofar toilet d'in ta ,tura ganin Ladidi a zaune tana ihu tayi" k'arasawa kusada ita tayi kana tace Ladidi meke faruwa tundaga room d'ina najiyo ihunki Ladidi batasan room ba sedai cewa tayi kashine ya matseni wlh na kusa yi a wando momy ce ta rik'o mata hannu ta mik'e nuna mata inda zata zauna tayi Ladidi gani takeyi kamar zata fad'a ciki se zaro ido takeyi kamar an tare kwarto.

Yau watan Ladidi daya a yaune dady ,ya samowa Ladidi makarantar primary a class 5 aka sata kasancewar sunje anyi mata interview tanada basira bazatayi wuyar d'aukar karatu ba "tunda tafara zuwa makarantar bata shiga sabgar kowa ,wata rana suna zaune a class teacher yashigo yace a fad'a mai masu ,surutu kowa a class d'in Ladidi yanuna kasancewar tunda tashigo school d'in ba,a ta6a kawo k'ararta ba ai kuwa malamin ya kamata yayimata duka sosai seda yafasa mata farcen baban dan yatsa" kuma tasha alwashi seta rama tunda yanaso tadawo Ladidin k'auye .

K'arfe hud'u na yamma dady ,yakirawo Humaid yana gurin aiki akan yaje ya d'auko Ladidi a school ranshi ba k'aramin 6aci yayi ba amma babu inda ya iya dole ya ajiye abinda yakeyi yaje d'aukarta babu kowa a school d'in kowa yatafi gida se teachers dasuke office suna ta ttaunawa tana hango motar Humaid gabata yashiga bugawa shigewa baya tayi seda yatada motar ya daka mata tsawa yace ubanwaye drivernki fitowa tayi saboda yunwa takeji dukda anbata kudin break amma ,a banza.

Tun kafin takoma gida take ciwon ciki sosai tarasa inda zatasa rayuwarta Humaid ,da yalura da halin da take ciki seya rud'e ko magana bata iya yi hospital d'inshi ya wuce da ita wani d'aki ya kaita da babu kowa aciki se karar Ac daketa bada iska yaje siyo mata abincin turo k'ofa yayi yaga jini yana zuba zaro,ido yayi yadubi Ladidi da ko motsi batayi seda ya,yayyafa mata ruwa kana ya murd'e bakin ,nata ko kulashi batayi ba dan ita kad'ai tasan wahalar da takesha alura yayi mata daganan yafice d'auko mata magani wayarshi ce take ringing dady yagani d'agawa yayi dadyne yace ina Ladidi Humaid cikin jin nauyin maganar da zegayawa dady yace gatanan a hospital zaro ido dady ,yayi kana yace meke faruwa da ita Humaid ne yakasa yiwa dady bayani yace am dady in momy na kusa please kabata wayar dady ne yahau banbamin fad'a kana yace ubanme kayi mata dabazaka fad'amin ba itako Ladidi hatta jinin da yazuba a jikinta duk bata sani ba tunda tana farfad'owa daga suman datayi yayi mata allurar bacci .

Dadyne rai a 6ace yamik'awa momy Humaid ne yace momy zakizo hospital d'innne¿" eh momy tace gamunan nida dadynka"hijab momy ta d'auko zuka nufi hospital d'in Humaid itada dady da isarsu direct office d'inshi suka wuce dady ne ya nannad'e malun malun din'shi yace to gamu maunzo nace uban me kayiwa yar mutane momy ce ,tace katsaya a tambayeshi mana kanata fad'a Humaid dai yakasa magana dan yana ganin kamar inya cewa iyayenshi Ladidi tafara period zasuce bashida kunya" sunkuyar da kai k'asa yayi kana yace 6atan wata tafara kuma yau d'inan momy ce tadubi Humaid tace to wanan shine abin 6oyewa dady ne yanemi guri ya zauna yace to yanzu tana ina Humaid ne ya mik'e yace kuzo muje d'akin "suna zuwa suka samu haryanzu tana bacci momy ce takalli fuskarta hak'ik'a tayi rama sosai Allah sarki.

Momy ce ta ,tambayi Humaid kasiyo mata pad kuwa eh yace kana yabawa momy ledar harda sababin pants yasiyo mata dady bece komai ba yana tsaye yazuba hannu cikin aljihu.

Farkawa tayi taga su momy a kanta tuno ciwon cikin datayi ne a mota sekuma taga jini a zaninta zaro ido tayi tafara kuka dady ne suka fice shida Humaid momy ta k'arasa gurinta tayi mata bayani dakuma inda zatayi ta gyara kanta momy tayi mata fad'an sallah akan lokaci " bayan ta gama shiryawa ne momy takira Humaid a waya tace yasiyowa ladidi riga ko doguwa ce "be jima ba segashi da rigar "dayake basuda nisa da masu saida kayayyaki".

Ruwan zafi yasa akawomata bayan tafito daga wankan ta kintsa kanta suka nufi gida momy a motar dady suka tafi shikuma Humaid da Ladidi suka tafi tunda suka fara tafiya talura da kallon da humaid yake yimata amma seta basar".

*BAYAN SHEKARA DAYA*

Ladidi na hango takuma kyau tayi haske tayi k'iba sosai gashi tafara jin turanci kuma tadena wauta irinta yan k'auye " samarine da ita sunkai biyar amma Humaid na ganinsu seyace anyi mata miji "itadai Ladidi batasan hujjar yin hakanba " tagama primary yanzu tana jss 2 komai nata yak'ara baiyana ".

Batada abokin shawara inba jalal ba duk wata damuwa tata yasani basa shiri da jalal " wata rana tana cikin tafiya zataje gidan wata k'awarta ta had'u da wani saurayi kya kyawa yana cikin mota ita kuma tana tafiya a k'afa"baya yayi da motarshi yace ya ,yammata ina magana kink'i kulani cigaba tayi da tafiya jitayi ya rik'o hannunta a zabure ta juye dan tunda take babu namijin da yata6a gigin rik'e koda gefen mayafinta ne..

LADIDIN ƘAUYEWhere stories live. Discover now