Chapter9-10

22 1 0
                                    

*LADIDIN K'AUYE*

*MOM ISLAM*

*ZAINAB HABIB*

*MARUBUCIYAR:*




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Episode:* 9_10

______malam Adamu ne yakira dadyn su Humaid a waya akan cewar Ladidi zata dawo gurinshi saboda tasami ,ilimi sosai"beyi musuba yace ranar lahadi se su Humaid suzo su d'auketa malam adamu ne yace da muna shirin kawota gobe nida Hauwa dady ne yace to ai babu damuwa duk d'aya ne sekun so Allah yakawoku lpy daganan sukayi sallama".

Inna hauwa ce ta ,tattaro wa Ladidi kayanta had'i da bata kud'in sabulu akan tayi wanki gobe zasu wuce birni aikuwa Ladidi jin haka ta fara murna tana tsalle ta kar6i kudin tafice siyo sabulu tana cikin tafiya ,ta had'u da k'awarta tana siyarda d'anwake gashi Ladidi najin yunwa k'awar ce tace Ladidi barin zuba miki d'an waken saboda tasan inta wuce Ladidi zata iya 6aro da robar d'an waken".

Fara zubawa tayi Ladidi tace ke barshi haka yarinya gobe zamu tafi birni mushi kayan d'ad'i kawar Ladidi ce ,tace nima inason zuwa birni sedai bamuda y'an uwa a birni .

Bayan ta siyo sabulun tafara wanki seda tagama duka sannan ta zauna tana jira su bushe ta ninke ".

Washe gari bayan sunyi sallahr asbh malam adamu yashigo yace su shirya da wuri saboda wuyar mota.

K'arfe goma suka tafi tasha sunyi sa,a wata mota bata cikaba suka shige malam adamu yabiya kud'in motar suka d'auki hanya zuwa jos".

Tunda suka shiga mota Ladidi ta hango wani k'aton arne yana cin Apple lek'enshi takeyi tana lashe baki had'a ido sukayi ta sunkuyar da kai a karo na biyu takuma d'ago kai tayi sa,a shima yad'go suka had'a ido ita kuma Ladidi ganin yanata kallon ta mugud'a mai baki shikuwa yana ganin haka ya bige bakin inna Hauwa ce ta ce kaikuma metayi maka dazaka bigi yar marainiyar Allah .

Da hausar da bata game bakinshi ba yace wanna yariya batada hakali Ladidi ce ta ,tuntsire da ,dariya shikuwa yaji haushin wanan dariya ana zuwa gurin sojoji ya bawa Ladidi 6awon gyad'a yace tazubar mai Ladidi bata ta6a shiga motar da zatayi tafiya me nisaba aikuwa ta watsa 6awon gyd'ar kusada wani k'aton soja suna ganin haka suka tare motar su Ladidi suka ce kowa ya fito da kuma wacce ta watso 6awon gyad'a ".

Ladidi ce tahau zaro ido saboda tana tsoron masu bakin kaya malam Adamu ne yace mekuma mukayi arnen ne yace daughtern kuce ta zubo bawon gyada malam Adamu ya bud'e baki yace ba ita bace".

Koda zamu fito bataci gyad'a ba kuma babu komai a hannun ta Ladidi ce ta nuna arnen tace wlh shine yabani yace in wurgar sukuwa sojoji sun rasa wazasu kama sukace Ladidi itada Arnen su fito suyi tsalen kwad'o .

Sojanne ya k'araso kusada su kana yace ku za6a ko tsallen kwad'o ko ayi muku bulala Ladidi ce ,tace wlh gara ayimin bulala tunda wanan k'aton arnen yajamin bulala biyar sukayi mata lafiyayyu malam Adamu bashida ta cewa kar a had'a dashi yaja baki yayi shiru direban motar sune yaketa masifa .

Ladidi ce tashige mota tanata kuka shikuwa arnen yak'i zuwa ayimai d'ayan sojan ne ya nuno arnen da bindiga da gudu yazo ganin sun saita kanshi.

Tunda aka fara bulalar yafara kuka yana basu hakuri ,ita kuwa Ladidi se dariya takeyi.

Malam Adamu ne yace wlh da tuni mun isa bayan an gama bulalar suka shige mota kowane fasinja yana fad'ar albarkacin bakinci har suka iso well come to plateau .

Kowa ya sauka a mota Ladidi tak'i fitowa seda ta ciro wata allura a kanta lokacin su malam Adamu sun tari adaidaita sahu zasu shiga ta sokawa arnen ta shige da gudu ".

Sun isa 6ukur park G.R.A anan ne anguwar su dadyn Humaid take wato alhaji abdullahi tsaya sukayi a bakin get d'in megadi ne ya lek'o kana yace daga ina kuke malam Adamu ne yace daga kano muke ni yayan mai gidannan ne seda megadi yakira a waya tukun yabarsu suka shige".

Tun daga k'ofar gidan Ladidi ke kallon tsarin gidan tunda tazo duniya bata ta6a kallon kyau da tsarin gida irin wanan ba sekace baza,a mutu ba inna Hauwa ce ta janyo mata hannu suka shige domin malam Adamu yarigasu shigewa.

Da sallama suka shigo itada inna Hauwa k'asa Ladidi ta zauna ina Hauwa a kujera malam Adamu shima yana kujera suna jiran mutanen gidan wata wata mata ce fara sol da ak'alla zatakai shekara arba,in a duniya sanye take da wani dakakken leshi me duwatsu tafiya takeyi kamar wata sarauniya ta iso gurin su inna Hauwa ta nemi kujera ta zauna .

Inna Hauwa ce ta fara gaida hajiya amina hajiya amina batasan inna Hauwa ba amma ganin malam Adamu yasa tagane matar shice bayan sun gaisa hajiya amina ta gaida malam Adamu Ladidi kuwa ta ,tafi a kallon palon dan batasan me akeyi ba seda inna Hauwa tace Ladidi baki iya gaisuwa bane ¿".

Ladidi ce,tace ina wuni hajiya amina tace lpy daughter ya kike shiru Ladidi tayi taci gaba da kalle kallen ta .

Hajiya amina ce ta k'walawa yar aikinta me suna ummi kira dagudu ummi ta k'araso ta durk'usa a gaban hajiya amina.

Cewa tayi kikawowa su malam abinci amsawa tayi da to hajiya ta mik'e ta nufi kitchen jollof d'in taliya ce wace taji kayan lambu sai k'amshi take zubawa da hollondia yogurt me sanyi ta d'oro akan turai ta kawo musu mik'awa malam Adamu tayi takuma mik'awa inna Hauwa nata ta d'auko wani ta mik'awa Ladidi nata da rawar jiki Ladidi ta k'ar6e abincin ta cire cokalin hajiya amina ce ,tace daughter kisa cokalin mana Ladidi ce tace a a wlh da hannu ma ya nak'are bare nasa cokalin.

Bayan dare yayi suyi sallah hajiya amina ta nunawa inna Hauwa d'akin da zasu kwanta suna shiga d'akin Ladidi ta d'are gado tanata tsalle tana cewa wanan aba kamar burodi mu agarinmu babu wanan aba me laushi haka inna Hauwa tana jinta bata kulataba.

Inna Hauwa ce takira sunan Ladidi tsayawa tayi da tsallen tace na,am inna kinsan me nakeso dake Ladidi tace a a".

Kinga kindawo birni da zama tsalle Ladidi tayi tana murna inna Hauwa ce ,tace kirik'e mutuncin ki dan Allah kinga ke marainiya ce kar ,rud'in duniya yasa ki zubda tarbiyarki to Ladidi tace".

Washe gari su Humaid sun shigo part d'in momy take gaya musu suje su gaida matar malam Adamu jalal ne yace ai tun jiya muka gaisa da malam Adamu sedai ,inna bari muje momy ce tace musu amma zaku shigo kafin kutafi ko Humaid ne yace eh insha Allah momy.

Direct dakin da momy tace musu inna Hauwa na can suka nufa sallama sukayi ,inna tana kan sallahya tana lazimi suka shigo gyaran murya tayi musu ,bayan ta shafa adu,ar ne suka fara gaisawa inna tace jiya tunda mukazo bamu had'u dakuba Humaid ne yace wlh inna aiyuka ne sukayimana yawa shiyasa inna ce ta sanya musu albarka suna cikin hira sega Ladidi nan tafito daga toilet da gudu batama lura dasu Jalal ba tahau jikin inna tana ihu Humaid ne yace inna a ina kika samo wanan yarinyar Jalal ne ya zaro ido ganin kamar yarinyar da tabige k'afar Humaid ce ,a zabure Jalal ya mik'e yadubi Humaid kana yace wlh brother wanan yarinyar ce da ta addabi mutanen k'auyen su d'ago kai Ladidi tayi suka had'a ido da Humaid .

Humaid ne yazaro ido yace yaushe zaku tafi ne inna¿" inna Hauwa ce ta washe baki ,kana tace ni da malam yau zamu wuce ita kuma Ladidi anan zamu barta .

Kwata ,kwata Ladidi batasan gidan su Humaid suka zoba sai yanzu ,

Humaid ne ce munshiga uku "inna Hauwa ce ta dubi Jalal da yakasa cewa komai se Humaid ne da keta salati duban su tayi kana tace wanan yarinyar yar uwar kuce dan Allah ku, kula da ita sosai duk cikin su babu me magana suka mik'e suka wuce d'akinsu .

Dayake d'akinnasu a had'e yake Jalal ne yadubi Humaid yace wlh brother ankawo mana bala,i cikin gidan mu.....✍️✍️✍️




Mom Islam ce ✍️✍️

LADIDIN ƘAUYEWhere stories live. Discover now