A GURGUJE
Haka kwanaki suka cigaba da gangarawa har ya rage yau saura kwanaki biyu kacal daurin auren. Baƙi kuwa zuwa yanzu kowa ya gama hallara na nesa da na kusa duk sun iso kowa na jiran ranar da aka taru domin shi. Hibba ma dai ba'a barta a baya ba dan tun jiya ta dawo gidan da zama a cewar ta Noor na bukatar ta a kusa da ita kasancewar ta aminiyar ta kuma gashi dama hutun makaranta suke.
A yau ne kuma aka shirya walimah da za'a gabatar a harabar gidan inda Ammiey da kanta ta gayyato wata hafizar Malama mai matsanancin ilimi da zata gabatar da taron.
Zuwa yamma kuwa babu bata lokaci aka fara gabatar da taron inda tayi wa'azi mai matuƙar ratsa zuciya da kuma zamantakewar aure. Cikin nasihohin da tayi ne ta dinga nanata kalmar hakuri da kowacce mace take yi a gidan auren ta inda ta ja hankalin amarya akan sai ta yi hakuri a gidan ta kafin taci ribar aure.
Ita dai Noor na zaune ne kawai a wurin ba dan tana fahimtar abun da malamar ke cewa ba. Cikin kaso dari ta dai fahimci talatin. Haka taro ya watse aka tabawa mutane souvenirs wasu suka samu Alqur'ani yayin da wasu kuma suka samu dadduma.

Koda suka shiga ciki an fara kirayen kirayen sallar magrib hakan yasa gaba dayansu suka dauro alwala suka gabatar da Sallah. Suna gamawa kuma aka shigo musu da abinci dan dama an riga an gama tun tuni. Da kyar Hibba ta samu Noor din ta ci kadan dan sam bata da nutsuwar cin abincin.
Bayan sallar isha kamar kowacce rana wayar Noor ta bada karar notification sound wanda ko bata duba ba tasan sako ne daga Junaid reminding her of the hell that is awaiting her a gidan shi. Sanin da tayi cewa daga shi dinne kuma yasa bata ko duba ba ta share message ɗin ta hau gado ta kwanta ba wai dan zatayi baccin ba. Tana nan kwance har Hibba ta shigo ta rufa mata bargo dan a tunanin ta Noor din tayi bacci ne sannan itama ta wuce ta kwanta bata fi mintuna ashirin ba kuma bacci yayi gaba da ita. Noor dai tana kwance tunani fal ranta ta saƙa wannan ta kunce wannan. Bata san iya adadin awoyin da ta dauka a haka ba har bacci ya dauke ta bayan kiran sallar farko.
Washegari haka ta wuni sukuku har zuwa lokacin da aka fara gudanar da henna dan Ammiey tayi hayar kwararrun masu lalle wanda zasu zana wa kowa sannan musamman aka dauko wacce ta ƙware sannan ta shahara wajen zanen lalle don tayi wa amarya. Cikin lokaci kankani aka fara zana wa kowa kuma tabbas babu karya na kowa yayi kyau amma na amarya ya ɗare na kowa kyau a wurin kasancewar combination din baki da jaa aka mata sai ya zama ya bada kala sosai kamar daura shi akayi akan hannun nata.
Zuwa dare an gama wa kowa nata gida dai ya kara kacamewa biki ya kankama. Amarya dai in banda fargaba, tsoro, firgici gami da tashin hankali babu abinda take ciki. Gaba daya rayuwar ta ta juya upside down. Bata taɓa kawowa kanta wani abu makamancin haka ba a rayuwarta. Aure at her age? That too a forced one? To whom she didn't even know? Ya Allah! Wannan wacce irin kaddara ce haka a hagunce? Kuma wai gobe ne daurin auren. Abun kamar a mafarki take ganin shi. Gani take kamar za'a zo a tashe ta daga baccin da take yi. Hakan kuma take fatan ya kasance.
A ranar dai idan akwai waɗanda suka yi bacci a gidan to kadan ne dan kamar rana haka ko ina ya kasance da jama'a kowa na harkar gabansa. Amarya Noor kuwa dama bata kawo bacci cikin jerin agendan ta ba don abun duniya sun taru sun mata yawa. Hibba cema take ta kokarin karasa mata last minute preparation dinta.

*****
Sannu sannu baya hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba. Sannan rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya.
Yau ta kama asabar kuma ita ce ranar da duk wani bako da bakuwa, babba da yaro, matashi da tsofaffi suka taru domin shi; wato ranar auren Noorul Janna da Junaid.
Tun sassafe aka kammala komai kasancewar karfe sha daya na safe za'a daura auren.
Bangaren ango kaff sun gama shiri dan har wasu sun kamo hanyar tahowa venue din. Ango kuwa na tare da abokansa wanda kaff dinsu babu wanda ya gayyata amma baiyi mamaki ba dan yasan hakan baya rasa nasaba da mahaifin sa da ya sanar da amininsa, wato Amin. Sannan Amin kuma ya gayyaci duk sauran abokansu. Shakiyanci kala kala babu wanda sruka manta basu masa ba duk da sunyi matuƙar mamaki jin ba da present girlfriend dinsa bane auren don su shaida ne na irin son da yake mata. Amma koma menene, nasu ido tunda bai basu wani hint akan auren nashi ba. Sun gama shirin su tsaff inda suka fito sak wayayyun angwaye masu ji da kansu ga ilimi da dukiya duk sun tara. Kallo daya zakayi musu ka gane their everything is screaming money. Irin kyan da sukayi ko makiyin su ya gansu sai ya yaba don sun hadu iya haduwa most especially angon da ya fita daban a cikin su. Tare suka jero inda suka sanya angon a tsakiya suka taho har wurin da aka jera motocin su kowa ya shiga driver sit suka dau hanyar gidan su amaryar kasancewar nan ne venue din.
Sun isa daidai lokaci saura mintuna biyar kacal nan kallo ya koma kansu dan tamkar taurari haka suka zamo.
Cikin gida kuwa kowa yaci kwalliya an cakare ana jiran a kammala komai a wuce reception. Mata iyayen biki kenan.
Bangaren amarya kuwa saida aka kai ruwa rana kafin ta yadda ta shirya cikin tsadadden bridal wear ɗin da Ammiey ta kawo. Kyau kam da yana magana da yayi a ranar dan fadar irin kyan da Noor tayi ɓata lokaci ne. Duk wanda ya ganta kuwa sai ya so sake kallon ta don kallo daya yayi kadan. Mai makeup ma da tazo da kyar aka samu aka mata dan hawaye ne kaɗai ke fita a idanun ta kuma sunki tsayawa.
Shelan da ya karade ko'ina da kuma guɗar da suka jiyo ne ya sanar dasu komai ya kammala and everything is official. Noor is now officially and legally married. A wife. Legal one. Wacce aka hada gemu da gemu aka daura. Wani irin hantsilawa hantar ta tayi sannan ƙirjin ta ya buga da karfi sannan ta mike tsaye cikin fitar hayyaci wanda hakan har sai da ya haifar mata da sarawa a tsakar kanta. Dafe kan tayi da hannun ta na hagu na daman kuma na saitin zuciyarta akan ƙirjin ta. Wani mahaukacin faduwa gabanta yake yi. Shikenan. Mafarkin ta ya rushe. All her fantasies is erased. Her dream of getting married to a loved one has now become a mirage. What has she done to deserve such? Me ƙaddara ta tanadar mata a wannan kaddararren auren? Menene makomar rayuwar ta? Shin zatayi rayuwar 'yanci kamar kowacce mace ko kuma uƙuba zata fuskanta kamar yadda take gani a mafarkin ta a kullum ta kwanta bacci? Wadannan sune tambayoyin da ke yawo a kwakwalwar ta wanda ya haddasawa sarawar kanta tsananta har tsayuwar ta gagare ta sakamakon jirin da ya fara deban ta tayi luuu zata fadi. Hibba dake ankare da ita ne kuma tun da taji an fara shelan tayi hanzarin isowa ta tare ta dan tuni numfashin ta ya katse ma'ana dai ta suma.

Wlh na gaji sosai. Ku manage. So far this is my longest chapter I guess. 2.1k words. Ai nayi dan kokari koh? Typing dinne akwai wahala.
Not edited.
Love You😘

Fateedau.

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now