Mahmud yace, "Amma kamar ƙafan naka naga kana tafiya".

"Amma ai ciwo take min".

"To hannun fa?

"Hannu kaɗan ne yake min".

"Ko targaɗe ne to?

"Nifa ban sani ba".

Tashi yayi suka shiga ciki yaje ya haɗo allurar dake da za'a sa masa drip da suka je siyowa har allurar ya siyo shiyasa ma aka samu.

"Ka ci abinci?

"Ban ci ba".

"Kasan amai zaka yi ai?

"Dan Allah kamin baka san me nake ji ba ne".

"Babu yadda za'ayi nayi maka allura baka ci abinci Sajjad".

Ya faɗa yana mayar da allurar ya rufe.

"Ka kamata bari naje na siyo maka masa".

Flask ya ɗauka ya fita yaje ya siyo masa duka be jima dake a kusan su ake yi wani lokacin ita yaje siyo musu su ci har da rana ma idan sun rage, shayi ya haɗo masa ya kawo tare da plate yasa shi a gaba sai da ya ci, ba laifi ya ci dayawa ba kamar yadda yake musu a gida ba, sai da ya ƙoshi dam sannan yayi masa allurar.

"Me kake ganin zata buƙata?

Mahmud yace, "Wa?

Duk da sarai ya gane abinda yake nufi.

"Ita".

"Wace ita?

"Mahmud bana san wulaƙanci matata".

Sai da ya faɗa yaji wani iri a baki wai matar sa. Dariya Mahmud yayi.

"Masu mata".

Banza yayi masa.

Yace, "Sajjad tunda ga yadda auren ku ya kasance ba lalle a ce tana san ka ba".

Kallan Sajjad yayi.

Yace, "A shawarce Sajjad kaine ya kamata ace ka nema ta kun zauna kun tsara rayuwar ku, me take so meye bata so, meke ɓata rai and so on".

"Uhmm".

Kawai yace masa dan shi yasan wacece ita da har zata tsaya tana masa dogon lissafi, yadda ya bi da shi haka shima zai bi da ita sai ya ga ta tsiyar rashin magana.

"Kana ji na?

"Inaji mana".

"Yanzu me ka yanke?

"Zan duba na gani, amma nidai yanzu ka fara siyo mana abinda kake ganin zata buƙata".

"Nida ba mace ba? Taya zan sa abinda take buƙata?

"Kayan amfanin mu na ci".

"Ayyahh sai ka min gwari-gwari ma zaci lefe zaka haɗa".

"Uban me na tara da zan haɗa lefe? Ɗan da me iyayi".

"Allah ya baka haƙuri".

"Mtswwwww! Kuma ka tabbatar da ka siyo mana komai wallahi".

Ya faɗa yana ɗaukan flask ɗin wainar yayi gaba. Girgiza kan sa Mahmud yayi gaba ɗaya ganin abokin nasa yake wani iri ya canza ya rage magana ya dawo wani iri da shi, kamar ba shi ba daga dare ɗaya kawai? Ko dan baya da lafiya? Shi ɗaya yake tunanin sa kafin ya ture ya fita ya cigaba da wankin sa.

Da sallama ya shigo tashi tayi tana amsa masa sallamar tasa tayi wanka tasa atampa riga da skirt bata iya dauri ba kuma ɗan kwallin babba ne hakan yasa bata wahalar da kanta ba kawai ta zura hular ta ta yafa mayafi.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now