A wannan dare tsakanin Noor da Ammiey babu wanda ya samu damar runtsawa. Ammiey tunanin 'yar ta da kuma neman mafita ya sa bacci kaurace mata. Noor kuma tunanin makomar rayuwar ta ya hana bacci ziyartar ta.

Washegari da safe kowa ya hallara a dining table don yin breakfast amma banda Noor da bata ko fito daga dakin ta ba. Dad ne ya ajiye mug din hannunsa sannan yayi gyaran murya yace:
"Ammiey ban ga Janna tafito ba hope dai lafiya?"
"Same here. Let me check on her." Ta faɗa tana mikewa tayi hanyar dakin Noor din.
Koda ta shiga ta same ta ne kwance cikin bargo ta takure sannan ta riga har kanta. Ammiey ta bude bargon tana kiran sunan ta amma shiru ba amsa. Zama tayi a bakin gadon tare da tapping kumatun ta. Zafi taji sosai jikin Noor din yayi wanda har sai da ta firgita. Sai a sannan kuma ta lura da karkarwan da jikin 'yar yake. Sosai take kiran ta tana jijjiga ta amma shiru hakan yasa ta kidime. Cikin tashin hankali ta koma dining area din tana kwala wa dad kira. Shima mikewa yayi da sauri dan wannan kiran da Ammiey take masa ba an lafiya bane. Isowar ta inda yake ta kamo hannun sa da sauri tayi hanyar dakin with him trailing behind her.
Ganin halin da take ciki yasa dad cikin sauri ya dauke ta zuwa mota yana kwada wa driver kira da mugun karfi. Da gudu ya figi motar yayi waje da ita bayan mai gadi ya wangale gate din.
Koda Ammiey ta fiti rike da hannun Jawad dad ya riga ya tafi. Hakan yasa ta wuce direct wurin da take ajiye motar ta suka nufi asibitin da take kyautata zaton dad zai je.
Bayan sun isa ta tsaya a reception ta and tambaye su ko nan aka kawo Noor nan suka amsa sannan ta wuce ciki inda ta hango dad tsaye sai safa da marwa yake ya kasa zama.
"Ya jikin Noor din me kuma likitoci suka ce yana damun ta?" Ta tambaye shi hawaye na kawowa idon ta. Bata damu da ta share ba ko ta tsayar da su ba ganin bai ce komai ba ta sake jefo masa wasu tambayoyin.
"Haba Juwairiya ki nutsu ki kwantar da hankalin ki mana. Har yanzu babu abun da suka ce sun dai shiga da ita kuma basu fito ba har yanzu."  Cikin daga murya yayi maganar.
"Shikenan." Iyakar abin da tace kenan ta juya a sanyaye ta zauna a daya daga kujerun da aka tanadar don zama. Ganin bata ji dadin tsawar da yayi mata bane yasa ya bita shima ya zauna daga gefen hagun ta don har yanzu tana riƙe da Jawad da hannun daman ta. Daura kanta yayi bisa kafadar sa ya shiga lallashin ta.
Sosai bata ji dadin abin da yayi ba amma tsakanin mata da miji sai Allah. Nan take ta hakura. Nan suka cigaba da zama kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa. Bayan kusan mintina ashirin lokacin suka fito inda suka bukaci ganawa da su dad.

Office din doctorn ya tsaru iya tsaruwa ga wani sanyi na daban a ciki yayin da ya gaurayu da sassanyar air freshener mai daɗin gaske inda ya bada wani homely atmosphere. Zama sukayi kan kujerun da suke facing juna a gaban babban mahogany table din mai dauke da abubuwan aikin sa da kuma name tag wanda sunan DR. MUHAMMAD ADEL ke jiki da manyan harufa.
Cikin nutsuwa da tarin kamala ya cire farin spec din idonshi ya ajiye a ma'ajiyar sa sannan ya daga ido ya kalli dad sannan ya mayar da duban shi zuwa ga Ammiey. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fara magana cikin nutsuwarsa.
"Mun samu ganin ta dawo hayyacin ta I mean she has gained consciousness and everything is normal now."
Sai a sannan suka sauke numfashin da basu ma san suna rike da shi ba. Da sauri kuma Ammiey tace
"Dr zamu iya ganin ta?" Kallon ta yayi kadan ya kau da kanshi sannan yace
"Zaku iya when you're done here." Gyara zama yayi ya fuskance su da kyau ya cigaba da faɗin
"Yar ku nada damuwa wanda hakan yana neman jefa rayuwar ta a matsala dan gab take da kamuwa da hawan jini sakamakon damuwar da ya taru ya mata yawa which is very bad ace at her age har ta fara samun irin wannan matsalar."
Idanu Ammiey ta kafe maigidan ta dashi dan tayi imani koma meya samu 'yar ta shine sila kuma dalilin wannan kaddararren auren ne.
Nisawa dad yayi sannan yace
"Inshaallah Dr zamu nemo damuwar kuma mu magance mata matsalar ta. Mun gode." Daga haka ya mike ya fita. Ganin haka Ammiey ma ta mike ta fita bayan tayiwa matashin likitan godiya. Shi dai binsu kawai yayi da ido yana nazarin irin sakacin wasu iyayen. Taya kana zaune da ɗaukan amma baka san yana da damuwa ba. Whatever it is ma ai su ya shafa. Tane baki yayi ya janyo wani file yana dubawa.

A can dakin da Noor take Ammiey ce tsaye gaban dad tana kallon shi. Ganin bai da niyyar cewa komai yasa ta share hawayen ta tace:
"Ka dai ji abinda likita yace. Idan ba so muke mu rasa 'yar mu ba na roke ka dan Allah kayi hakuri ka janye zancen auren nan wlh na tabbatar shine ya jefa ta cikin wannan halin da take ciki." Ta ƙarasa wasu zafafan hawaye na gangarowa.
"Juwairiya wai ke meyasa ba'a faɗa miki magana daya kiji ne? Yarinta ce ke damun ta ba wani abu ba. Da zarar anyi auren shikenan an wuce wurin. Kwana nawa ne zata manta da duk wani abu ta rungumi mijin ta? Mutane nawa aka wa aure basa so da fari amma daga karshe su zama masoya? Ki faɗa mun lokacin auren mu ni da ke waye yake so a cikin mu? Babu. Amma yanzu fa? Wa yake jin kan mu? Saboda haka daga yau karki sake mun maganar nan inba haka ba zaki ga ɓacin rai na wlh." Tun da ya fara magana take kallon shi baki sake har sai da ya kai aya amma kan tace wani abu har ya fice daga dakin. Zama tayi a kujerar dake gaban gadon tana hawayen tausayin 'yar ta. Wannan wani irin rayuwa ce haka?
Ji tayi ana share mata hawayen ta daga ido taga autan ta ne Jawad. Murmushi ta sakar masa tare da rungume sa.
"Why are you crying mom?"
"I'm not crying dear. Abu ne ya shiga idon Ammiey shiyasa take hawaye." Ta faɗa plastering a fake smile on her face.
"Ok." Ya fada innocently.
Komawa yayi ya zauna a gefen Noor da har lokacin take kwance idanu rufe alamar bacci take har wannan lokacin.
Sai da drip din da suka sa mata ya kare ta tashi daga baccin. Ganin ta samu karfin jikinta yasa suka rubuta mata sallama tare da magunguna da zata na sha. Har lokacin kuma dad bai sake dawowa ba.

___________
Fateedau.

Please vote and comment. It means a lot.

Not edited.

NOORUL JANNANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ