Shafi Na Daya

931 21 1
                                    

⚡️*GAMON JINI*⚡️

*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

*FREE PAGE ONE*
        
*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*

*****

Wata Arniyar bakar BMW 840 IX ce ke tsula uban gudu a hanyar dake tsakanin sokoto, zamfara da dukkan alamu mamallakin motar sauri yake ya cimma duk inda ya nufa, sanye yake da wata bakar riga wacce ta fito da duk wata kirarsa ta cikakken namiji me kwanji tare da wando ta khakin sojoji kafafunshi irin takalmansu ne, hannunsa na hagu dake d'aure da wata Rolex watch d'insa ya d'ago ya duba lokaci dukda karfe 11 na dare ya wuce sede hakan be sa ya ji kaman ya nemi masauki In ya shiga Gusau ya kwana ba, ya riga ya kudurta ba inda ze kwana yau se birnin kano, a jikinsa yake ji mahaifiyarsa ba lafiya kaman yadda shakuwarsu ta zarce misali though akwai wannan alkunyar ta en fari sede duk wani abinda ze faru dashi kaman gaya mata ake a jikinta take jinshi fiye da kowa da komai dukda ba shi kad'ai Allah ya bata ba, haka ta 'bangarensa idan yaji uneasiness da yake ji yanzu ya rasa natsuwa kwata kwata to tabbas ya san mahaifiyarsa ce bata da lafiya.
Had'add'iyar wayarsa kirar Samsung Ultra dake ajiye ya sa zara zaran fingers d'insa ya d'auko yana murza motar da hannun hagu ba tare da ya rage gudun da yake zabgawa ba ya fara latsa wayar har ya iso number d'in da yake nema ya danna kirar tare da maida wayar ya ajiye da yatsa d'aya ya latsa Bluetooth d'in dake jikin motar tare da maida duk hannunshi kan stirring ya kuma murza motar yana me kara mata speed, fuskarsa Bata ta'ba nuna expression d'insa a rayuwa kullum yana nan ba'a had'e ba ba kuma a sake ba he has a blank expression face tun tashinsa, ringing na karshe wadda ya kira d'in ya d'aga daga d'aya 'bangaren ya furta

"Am sorry Yayanmu"
Be kula hakurin ba yace
"Abdulkadir ya jikin Amah?"
Da tsantsar mamaki Abdulkadir yace
"Yayanmu wa ya fad'a maka bata da lafiya? After All gargad'in Abbu...."
Shiru yayi kaman yadda yayan nasu yayi shiru, jin be da niyyar magana kaman yadda yake idan har ya d'auki waya ya kiraka to abinda yake so yaji kawai daga gareka ze ji ba wai ya saurari tambayoyinka ko ra'ayinka ba.
"Da sauki yayanmu ya ma sauka karin ruwa ake mata"
Ajiyar zuciya ya sauke se da ya ja iska yace
"Usual hospital?"
"Eh, ba de kana hanya ba? You don't have to come da safe fah Khalid yace za'a sallameta..."
Kit ya katse wayar yana taune lip, yaushe mutanen gidan nan zasu bar mishi mahaifiya ta huta ne? Idan fa Har ta sarara aka rasa me d'aga mata hannu to fah yana cikin birnin kano ne shi d'inma ba wai don yana magana ba kawai shakkarsa da sukeyi ne yasa amma yana bada baya abubuwa daban daban dukda ba wani ke gaya masa ba sbd shi ba mutum bane me jin maganganun mutane, ba mutum bane me kallon mutanen ma gabad'aya idan kuwa ya kalleka ka kai kololuwa wurin kular dashi ne musamman mata, a ko yaushe kanshi na a kasa bakinshi na d'an motsawa, shi ba malami bane sede shi d'in mahaddacin qur'ani ne wadda da wuya kaga mahaddacin qur'ani na zaune baya tilawarta ko da a zuciya ne kalilan ke fitowa kan lips d'insu kad'an kad'an, tsaki yaja yana tuna yadda Amah Bata so suyi magana akan abubuwan da ake mata bama ta so ya sani alhalin bakin cikin ke tada Chronic asthma d'inta da 'bacin rai ke motsa shi ko ya yake.

A hankali sassayar ringing tone d'inshi marar hayaniya ya karad'e motar kasancewar shi baya son hayaniya hakan yasa komai nashi marar hayaniya ne, kallon wayan yayi se yaga Abbu, Bluetooth d'in motar ya danna tare da gyara murya yace
"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Amsawa Abbu yayi tare da d'aurawa da
"Abrar Kana Ina da tsakar daren nan?"
Kai tsaye yace
"Hanyar kano yanzu na kusa Gusau"
"Abrar lafiyanka kuwa? A yadda hanyoyinmu suke yanzun nan zaka kama hanya da wannan daren? Ko ita mahaifiyar taka aka ce maka zata so ka taho a yanzu me yasa bazaka hakura da safe ba?"

Cikin tsadaddiyar muryansa da jinta ma aiki ne yace "Just pray for me Abbu In Shaa Allahu lafiya zan iso"
Ajiyar zuciyar da har yaji daga 'bangarenshi Abbu ya sauke kan yace
"Allah ya kawo min kai lafiya" Da "Ameen" ya amsa kan Abbu ya katse wayan.
Yanayin garin ya kalla da alamu ruwa ke gab da sauka sbd iska da kuma chida da ake sakewa lokaci zuwa lokaci, ya bar kauyen Maru Abadan yana dab da shiga Bungudu kaman daga sama ya ga Ana shirin shan gaban motanshi cikin zafin nama ya taka wani wawan birki yana d'ago kanshi don ganin wani me kasadar ne wannan.

GAMON JINIWhere stories live. Discover now