17-18

220 9 4
                                    


BOOK 1
PAGE  17-18

Da wani irin sabon tashin hankali Oumuu-Ayman ta shiga girgiza kanta,
Abu Maleek ko a jikinsa ya shirya idan har Mahaifin nasa zai samu lafiya,
Ya rasa uwa mahaifiya dan haka ba zai yi saken da zai rasa mahaifin sa ba,
Oumuu-Ayman ce taka numfashi tare da kallon makamin gaba ɗaya hankalinta yaƙi kwanciya da wannan tafiyar da Jalaluldeen zaiyi,
Cikin damuwa tace.
"Jalaluldeen zai zauna da mahaifinsa, zan sanya ɗaya daga cikin fadawa suje nemu maganin"
Da sauri Makamin ya girgiza kansa yace.
"Hakan bamai yiwuwa bane, jinin King Tunde Muhammad Jalal ake buƙata yaje da kansa, idan ya shirya tafiyar zan faɗa masa ta ƙasashen da zaibi"
Kafin kowa yayi magana Abu Maleek dake zaune ya rungome King Tunde a hankali ya fesar da numfashi tare da sauke ajjiyar zuciya,
Cikin rashin damuwa da haɗarin da tafiyar take dashi yace.
"Gobe zan tafi, ka faɗi da komai na tafiyar"
Gaba ɗaya suka kallesa, sosai Abu Maleek ke ƙaunar iyayensa kamar yadda suke ƙaunar sa,
Cikin fahimtar maganar ta Abu Maleek Malamin yace.
"Ta kasashe biyu zaka shige ƙasar dake gaban Guinea itace Birnin Bera, zaka tsaya a wata rugar Fulani, wacce ake ce mata Rugar Mahinjo, daga nan zaka samu dukkan bayanan da zai sadaka da Birnin Bera"
Ya faɗa yana zaro wata peper daga cikin aljihunsa,
Kana ya ɗura da faɗin.
"Wannan taswirar wajance koda zaka ɓata a hanya, kana duba taswirar zaka Fahimci inda kake"
Abu Maleek bai ce komai, idanunsa akan fuskar King Tunde Muhammad Jalal wanda kawo yazo ko buɗe ido baya iyawa,
Hannunsa ya ƙanƙame a hannun Abu Maleek,
A cikin ransa ji yake inama zai iya buɗe baki yayi magana ko kuma zai iya rubutu,
Da babu abinda zai sanya yabar Abu Maleek ya yi wannan tafiyar,
Yayi imani abinda suke tunani sam ba haka bane,
Shi kaɗai yasan abinda ya samesa jiya bayan kowa ya tafi wajan bikin ODUN EGUN.
Oumuu-Ayman ce ta amshi taswirar idanunta ya ciccika da ƙwallar tausayin Abu Maleek da kuma halin da zai iya tsintar kansa a cikin tafiyar.
Sallama Malamin yayi masu kana yabar wajan Otun ne ya miƙe tare da mara masa baya saboda rakasa hanya.
A sanyaye Abu Maleek ya kwantar da king Tunde, kana ya gyara masa kwanciya, ba tare daya kula kowa na wajan ba, ya nufi sashinsa fuskarsa a ɗaure kamar hadari.

Yana miƙewa Kubraah ta miƙe tare da mara masa baya, yana tafe dafe da kansa Kubraah na bayansa, sarai yaji footsteps,
Amma bai kawo cewa Kubraah bace, shi harga Allah mantawa yake yana da wasu mata,
To ba dole ya manta ba, aure har biyu without his permission,
Babu wacce yana so daga ciki gwamma Auran Bola ƙaddara ta haɗa Auran,
Amma ko a yanzu da zai san gaskiyar dake ɓoye Tabbas itama da bazai zauna da ita ba,
Shi babu mace a sabgarsa, mantawa yake akwai wani abu dake shiga tsakanin ma'auratan,
To kuma ya sani ba sai yana da lafiyar yi ba, yana shiga Main Parlo nasa ya tsaya cak,
Sabida yana son yajin dalilin daya sanya Oumuu-Ayman take biyosa, idan ma tazo domin ta hanasa wannan tafiyar to tabbatas ta makara,
Yana nan tsaye yana sauke numfashi tare da taune leɓansa wanda sukai jajirr saboda yawan tsotse su da yake,
Bai an kara ba yaji Kubraah ta faɗa jikinsa ta baya tare da rungomesa.

      *Karatun ABU MALEEK yana buƙatar nutsuwa, daman na faɗa maku salonsa nada banne, zazzafar soyayya ce wacce tafi ƙarfin a haɗa ta data Laylerh da Majanun, balle kuma ta ROMOE DA JUILET, zata fi dacewa ka haɗa ta da Film ɗin TAITAINIK🥰💔*

Wani irin sarawa kansa yayi ransa ya ɓaci sabida tsabar raini, kamar shi wata zata haɗa jikinta da nasa,
Cikin sabon wani ɓacin ran, ya wani juya da sauri tare dasa hannunsa ya ɓanɓareta a jikinsa,
Kuka Kubraah ta sanya tare da ƙoƙarin ƙara rungomesa,
Da wani sauri yaja baya ya shiga nuna mata hanyar fita daga sashin nasa, cikin kuka tace.
"Why? Mene yasa Abu Maleek? Ni matar kace, tunda akai Aure na dakai babu taɓa magana ba, ban taɓa sanyaka a cikin idanuna ba, balle na zauna muyi magana dakai har naji ɗumin jikinka,
Nifa macace ina da rauni idan zaka iya zama ba tare da mace ba, ni sam ba zan iya zama babu namiji ba, da haƙurin mata dana maza ba iri ɗaya bane,
Ka tausaya min Abu Maleek ka sauke haƙƙin dake kanka kafin ka tafi, babu da tabbacin zaka dawo a raye ko kuma ajalinka zai riskeka a can ne, pls My dear try to understand my feelings"
Tunda ta fara magana ya kafeta da Manyan gajiyayyun idanunsa, so itace second wife ɗin da Salimerh tace King Tunde ya aura masa ita,
Why duk samarin gidan sai shi za'a aurawa mata har biya, matanma da babu wacce ya taɓa cewa yana so,
Ko kuma ɗan taure ya zama suna ganinsa yana bin mata a guje shiyasa sukai decided na aure mace ba tare da izininsa ba,
Shi gaba ɗaya baiga abinsu a jikinsu, ko wacce ƴar banza da nono bai fi tafin hannunsa ba,
Gajeran tsaki yaja tare da juya zai shige part ɗinsa yaji ta ƙara.

ABU MALEEKWhere stories live. Discover now