3-2

372 10 8
                                    


BOOK 1
PAGE  3-4

"Jikin King Tunde Muhammad Jalal ya tsananta, babban tashin hankalin yadda yake ta kiran sunan Queen Roomana"
Dam dam dammm zuciyar Mai Babban ɗaki ta bada sauti,
Cikin tashin hankali da kuma tsoro haɗi da zullumin daya gama ratsa zuciyar mai Babban ɗaki,
Ta sanya tafin hannunta tare da dafe gishintuta shiga sharfe zufar da yake karyo mata,
Baya tayi kaɗan tare da fesar da numfashi haɗi da kallon,
Hadima Zubaida cikin jarumta tace.
"Kije ki kira Oumuu-Ayman ta sameni a tirakar King Tunde,
Sannan ki kiramin OTUN (Galadima), shima ya sameni a tirakar King Tunde"
Cikin ladami da girmamawa Hadima Zubaida ta sunkuya har ƙasa tace.
"Faɗe taki cikawa tawa,Mai Babban ɗaki"
Kai kawai Mai Babban ɗaki ta jinjina,
Shekarunta sun ja, amma komai na rashin tsoran Allah da kuma son zuciya ƙara bayyana yake,
A cikin Alaafin (Masarauta).
Hadima Zubaida na shirin fita Mai Babban ɗaki tai saurin faɗin.
"A tsananta tsaro a shashin, ki tabbatar babu wanda ya san da maganar ciwon na King Tunde,
Hatta matarsa kada ki faɗa mata, sannan ko sirikan gidan nan kada suji wannan labarin mai tarwatsa zuciya,
Ki sani fitar wannan al'amarin yana nufin rushewar Wannan Masarauta wacce ta kafu shekara da shekaru,
Ki kiyaye da wannan Hadima Zubaida, duk abinda yaje ya dawo kiyi kuka da kanki"
Ƙara sunkuyar da kai Hadima Zubaida tayi cikin son bawa Mai Babban ɗaki girmanta na mahaifiyar King Tunde tace.
"Ubangijin Al'arshi yana kallon komai,
Kuma yana ji yana gani, idan har maganar ta fita dukkan hukunci daya dace aimin ni Hadima Zubaida na aminci"
Tana faɗin hakan ya juya da sauri domin zuwa sashin Oumuu-Ayman.

Ajjiyar zuciya a karo na barkatai Mai Babban ɗaki ta ƙara saukewa,
Zuwa yanzu abubuwa sun fara mata yawa,
Tana son samun mataimaki Tabbas,
Amma yaushe? Ta ina? Wace zata zama hasken da zai yaye duhun dake cikin Alaafin?
Shine abinda har yanzu bata sani ba,
Yadda shekarunta suka ja hakama Oumuu-Ayman ba komai zata iya ba,
Jigon gidan biyu ne, gashi an wayi gari babu Queen Roomana,
Ɗaya ɓangaren wanda ya kasance haske da kuma tauraron gida ƙaddarar sa kaɗai da ishesa,
Ƙaddarar kuma da ita ce sanadiyyar faruwar dukkan wani mugun tuggu dake cikin Alaafin,
Miƙewa tsaye tayi tana runtse ƙafarta wacce take mata,
Tsananin zafi da kuma zugi domin kwana biyu,
Ciwon ƙafar ya dawo mata sabo fill har bata iya taka ƙafafuwan ta,
Tana dogara sandar zallar azurfa ta mai sheƙi ta nufi Parlo idan Kuyanginta suke jiranta.

A can tirakar King Tunde kowa Oumuu-Ayman ce zaune a gefe guda, sai Otun da kuma Hadima Zubaida.
Gaba ɗaya Babban shashin wanda ya kasance shine sashin Oba watu sarki ya cika da masu tsaro ko alamun fara'a babu a fuskarsu bare ka tabbatar cewa idan kazo zasu barka ka shiga,
Mai Babban ɗaki ce ta ƙarasa shiga ciki yayinda kuma,
Kuyangunta suka tsaya can nesa da Babbar ƙofar shiga tirakar ta King Tunde,
Tana shiga Oumuu-Ayman ta Miƙe tsaye sabida nuna girmamawa,
Cikin sabon tashin Hankalin daya samesu bayan wanda suke ciki,
Mai Babban ɗaki taja Jikinta can gefe kusa da King Tunde tana faɗin.
"Kiloshèle?" (Meke faruwa)
Cikin jan wahala da kuma tsananin a zabar da King ya keji a cikin zuciyarsa ya sanya tafin hannunsa,
Dake ɗigar da gumi yace.
"A nemu Queen Roomana duk inda take,
Kada a bari a rasata, Tabbas jikina yana bani akwai wani abu,
Ban san mene shi ba, ban kuma san yaushe ya faru ba,
Amma Queen Roomana itace hasken Alaafin"
Ɗauke kai Oumuu-Ayman tayi sabida hawayen daya sakko daga cikin idanunta,
Babu abinda yake tayar mata da hankali irin rashin Queen Roomana,
Babban abin fargabar har kawo yazo babu wanda ya faɗawa,
Jalaluldeen sabida tsoran abinda zai yi,
Tana tsananin son Jalaluldeen so mai yawa musamman idan ta duban mummunar ƙaddarar data hau kansa,
Gyara zama Mai Babban ɗaki tayi tace.
"Babu abinda zai faru da Queen Roomana, ka kwantar da hankalinka, na tabbatar ko babu Queen Roomana akwai hasken da zai zo cikin Alaafin yay fatali da duhun da yake cikinta,
Tabbas nayi imani da hakan lokaci kawai muke jira"
Ta ƙare maganar tana tasbihi a ranta,
King Tunde kallon mahaifiyar tasa yay yace.
"Wanne haske ne wannan wanda ya wuce na Queen Roomana?,
Bana jin akwai wani haske da zai yi iya yaye wannan duhun dake cikin Alaafin"
Murmushi Mai Babban ɗaki tayi tace.
"Da kasan zaka samu Queen Roomana? Ko kuma kasan zaka samu MALEEK yaro mai fikira da hikimar gaske, to mafarki na bazai taɓa gayan ƙarya ba,
Sai dai bansan lokacin da mafarkin zai zama gaskiya ba"

ABU MALEEKWhere stories live. Discover now