5-6

220 10 1
                                    


BOOK 1
PAGE 5-6

Robar ta faɗi ƙasa, cikin sauri kuma ta ɗauka tare da mayarwa saman fuskarta tana sauke ajjiyar zuciya.
A hankali kuma cikin son tunanin abinda zai faru gaba shiga yawo cikin kwanyar kanta.
Tabbas rashin lafiyar King Tunde tai matuƙar faranta ranta sosai fiye da sosai ma.
Kawo lokacin harshashen kasancewar ta Sarauniyar Kanzaf take.
Cike da farin ciki da kuma jin daɗin,
Sabuwar nasarar dake shirin tunkaro ta, ta tsirawa mirror'n idanu tana hango zallar kyau da kuma tarin haibar dake saman fuskarta,
Lallai Tabbas Hadima Zubaida tana da amana da kuma riƙo da gaskiya wannan dalilin ya sanya ta zama Amintacciyar Hadimar King Tunde.
Baya tayi kaɗan tana watsa hannayenta sama cikin dakakkiyar murya ta mai cike da isa da kuma gadara tace.

"Easy! Easy! Wannan lokacin tunani ne bawai shirme ba, wanne dalili ya sanya Oumuu-Ayman da Mai Babban ɗaki suke son ɓoye MALEEK? Har suke laƙaba masa kalmar mutuwa kalmar da ita a rayuwa ma mancewa take da ita, idan har ba gani tayi wani ya faɗi ya mutu ba"
Shiru tayi da zan can,
Ta shiga kewaye cikin ma dai-dai cin Parlon nata,
Murmushi tayi kana ta ɗura hannayenta duk biyun ta bugi tsakiyar kanta tace.
"Perfect idea, dole Tabbas ya kamata MALEEK yayi mutuwar gaskiya, domin shi kaɗai zai hanani zama sarauniyar Kanzaf"
Ta faɗi hakan tana mai faɗawa saman kujera 3seater tare da sauke gwauron numfashi.

Misalin 11:30 na safe Salimerh ta fito sanye da wani tattausan farin voyal na mata.
Wanda yake ɗauke da red torches, masu kyau da kuma walwali suna ɗaukan idanu,
A ƙalla voyal ɗin Jikinta zai kai adadin kuɗi kimanin 1500k (dubu ɗari da hamsin).
Sai milk ɗin Alƙyabba data sanya a saman voyal ɗin,
Wanda ta haddasa fitowar a salin kyanta kuma ta ƙara shaidawa jama'a Tabbas, ita ɗin jinin Alaafi ce,
Salimerh tana da sanyayyan kyau bata sa jiki sosai sai tsayi da take da shi,
Ga kuma fara'a da kyautatawa, amma tana son nuna cewa iya ɗin da gaske jinin sarauta ce,
Wanda ko da ace bata nuna ba to zallar jin kanta da kuma isarta haɗi da Izzarta ka ɗai zai shaidawa mutane cewa ita ɗin jinin King Tunde Muhammad Jalal ce.
Hannunta riƙe da wayarta mai ƙirar Iphone 12pro max,
Kanta a ƙasa take taka Fararan sahunta wanda suke sanye cikin wani takalmin fata,
Mai tsananin kyau ga wani gashi gashi dake a jikinsa,
Daga bayanta kuma Hadimanta ne suke riƙe da school bag ɗinta da kuma Iphone system ɗinta,
Duk inda ta gilma bayi ne ke zubewa suna gaida ta, duk da cewa abinda take dubawa yana da matuƙar muhimmanci amma haka take daurewa tana ɗaga masu hannu,
Sabida wulaƙanci bana ta bane, infact ma bata iya sa ba.

Wani babban dogari ne ya ƙara su da sauri ya buɗe mata back seat na motar mai ƙirar  Mahindra XUV7000 ash color!
Da sauri ta faɗa mota tana mai gyara zaman farin iphone bluetooth ɗin ta,
Driver na ƙoƙarin jan motar, taji an buɗe ƙofar left hand side ɗin ta an shigo,
A hankali ta saki numfashi tana mai ɗan taune laɓɓanta, tuni ƙamshin perfume ɗinsa ya shaida mata ko wanene,
Ba tare kuma da tayi magana ba taci gaba da searching ɗin dake na *Criminology*
Kasancewar yau ne First time da zata halarci *Dean Of Law* (University of Benin) a hankali kuma ta shiga typing ɗin “Define Criminology¿”

Cikin abinda bazai wuce wasu daƙiƙo ba goggle ɗin suka watso mata amsar.

_Criminology is a_ _multidisciplinary science that studies a diverse set of information related to criminal activities such as individual and group criminal activities, perpetrator psychology and effective means of rehabilitation._ _Criminology degrees examine social reaction to crime, methods and procedures to prevent and combat crime and social protection from crime. Criminology combines theories from other disciplines like psychology, sociology and law_

Anya zata iya wannan karatun mai wahalar gaske da kuma tarin hatsari,
Wata zuciyar ta bata amsa da.
"Dole za kiyi, kada ki mata wannan karatun shi ne hope ɗin ki, kuma shine abinda kike so kiyi Achieving a rayuwa, kuma yin wannan karatun shi ne zai baki damar tsare jama'ar Alaafi da kuma al'ummar Kanzaf,
Wannan karatun shine zai baki damar fahimtar mugwaye kuma azzaluman da suka jima suna zuluntar ɗan uwanki, wanda har kawo yazo babu wanda yasan ko suwane bare yasan plan ɗinsu na gaba"

ABU MALEEKWhere stories live. Discover now