1-2

717 19 5
                                    


20/11/2021- 21/7/1443AH

      *DEDICATED TO* ALL _ONLINE WTITERS, AL'KAIRIN ALLAH YA KAI MU, ALLAH YAY MAKU LIƊIFI DA KUMA JAGORA UBANGIJI YA KYAUTATA ƘARSHENKU YA YI RIƘO DA HANNAYENKU_

BOOK 1
PAGE 1-2

Edo/ Benin City state

Iska mai daɗi ce take Kaɗawa a garin, yayinda da samaniya tai wani kalar gwanin sha'awa, duk da cewa dare ne,Amma hakan bai hana ƙwantaccen hadarin dake ƙasan gajimare baiyana ba.
Yayinda gajimaran ke haske yana bada wani ƙara mai nuni da cewa hadarin gab yake da tashi.
Musamman yadda garin yay jajir baka jin sautin komai sai na tsuntsaye da kuma sassanyar iskar dake Kaɗawa a garin.
Yadda hadarin ke ƙara haɗi da wani bada kalar sauti mai rugugi yana ƙara shaidawa mutanan garin cewa Tabbas ruwan gab yake da sauka, sbd yadda gajimaran yake ta gudu yana haɗa kansa hakan ya data hankalin tsuntsayen dake saman bishiyoy da Flowers damar tashi domin samun mafaka.
Yayinda da a gefe guda ƙaramin Yaron wanda bai zai gaza shekara 15 yake tafe cikin sassarfa sbd samun damar shigewa makwancinsa,
Gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake sbd ruwan da yake jin ya fara sauka, sosai Allah ya ɗarsa masa tsoran saukar ruwan sama.
Fararan kayan baccin sa dake manne a farar fatar jikinsa suka ƙara mannewa.
Kasancewar su masu tsantsi da kuma sulɓi.
Tsayawa yay cak sbd sautin tafiyar da yaji a bayansa, gaba ɗaya a tsorace yeke, domin wannan shine karansa na farko daya fito cikin dare.
Juyawa yay yaci gaba da tafiya har ya samu damar  cimma shashin nasa yana gab da buɗe ƙofa.
Aka sakar masa wani doka a tsakiyar kansa.
Ƙara ya saki yana mai dafe da kansa nan da nan kuma jini ya fara gudana ta ƙasan kansa ya shiga sauka saman wuyansa zuwa kafaɗarsa,
yayinda idanunsa suke lumshewa, sabida tsananin azaba haɗi da zugi wanda yake ƙara hargitsa masa dukkan tunaninsa, Tabbas da gaske dokan ya shigesa har baya iya gane inda yake.
Maimakon ya shige part ɗin nasa sai kawai ya juya ya nufi wani sashin.
Gefe guda kuma, wani ƙyakƙyawan Yaro ne Shima wanda bazai wuce 15yrs ɗin ba.
Ƙyakƙyawa ne ajin farko, ɗan leƙawa yay yaga da gaske babu kowa duk da cewa bashi da tsoro amma shi ɗin Mutum ne mai son kare martabar sa, ga isa da kuma ikon gaske baya shayin kowa..
Da sauri yabar wajan sabida foot sounds da yaji.
Yana mai dafe da kansa dake ɗan zubar da jini ya ƙarasa inda take tsaye,
Ganinta a wajan ne kuma yasa gaba ɗaya ya nufi inda take gadan-gadan, ihu tasa amma duk da hakan bai hana shi rapping ɗin ta ba, sabida shi ɗin stubborn ne very stubborn bai ji sam, duk da cewa yana da tsoro.
Ganin abinda ya aikata
ne kuma yasa cikin sauri ya tashi yana mai naɗe wandonsa yabar wajan yana sakin tattausan Murmushi.

*SAHEL*
Wani yanki da cikin garin Sahel, San sanin Fulani ne wanda ya daɗe da kafuwa duk da kasancewar duk Fulanin wajan Makiyaya ne,
Masu tashi su sauya sheƙa a duk sanda suka so,
Gaba ɗaya cikin rugar bukkoki ne da ko wanne waje ga tarin garken shanu da ragona haɗi da raƙoma,
Amma gaba ɗaya shanun wajan sunfi ko wacce dabba yawa a cikin garken,
Dare ne mai cike da tsoro haɗi da tsantsar fargaba, gaba ɗaya Fulanin rugar sun hana idaniyar su bacci sabida tunanin abinda zai je ya dawo,
Gaba ɗaya basu da wata kwanciyar hankali kullum suna rayuwa cikin tsoro da tarin fargaba gaba ɗaya an hanasu kwanciyar hankali da farin ciki,
Basu da wata walwala ko kaɗan,
Misalin ƙarfe 2:30 ma daran yanar juma'ar kamar a mafarki Fulanin cikin rugar suka fara jiyo saukar bindiga da ƙarar fashewar abu kamar bom,
Cikin sauri ko wanne magidanci da kuma samarin rugar suka fara fitowa ɗauke da makamai yawanci kuma bawai makaman arziƙi bane,
Duk da yawanci jama'ar Duniya bawai gari ba sunawa Fulani kallan mugwayen mutane marasa tsoran ALLAH,
Amma a zahiri kuma ba haka bane, Fulani sam basu ƙaunar tashin hankali sabida sam basu sama da shi ba,
Kasancewar gaba ɗaya rayuwar daji suke rayuwa mara ƴanci,
Sosai hankalin Fulanin rugar ya tashi sabida kafin su yi wani tunani,
Tuni mugwayen mutanan sun ƙaraso cikin rugar suna harbin dukkan wanda suka yi katari da shi,
A can gefe guda kuma  Wani magidanci ne ya fito daga cikin bukkar sa yana riƙe da hannun matarsa,
Wacce take dafe da cikinta wanda ya cika wata 9 a duniya,
Cikin sauri yake mata magana suna tsaka da tafiya taji mijin nata ya saki ihu,
Da sauri ta juya taga ashe harbinsa akai baki ta buɗe zatai ihu,
Yay saurin sanya tafin hannunsa ya toshe mata baki dashi,
Cikin fitar rai ya cire wani (GURI) nasa ya damƙawa matar tasa,
Yana shirin yin mgn sai Numfashin sa ya ɗauke alamar dai rai yay halinsa,
Cikin sauri ta miƙe Idanunta na zubar da waye, a ranta take addu'ar tsira da abinda yake cikinta,
A haka ta kawo gaɓar wani kogi,
Sabida tashin hankali da yay mata yawa yasa naƙuda ta kamata, nan kuma take ta samu nasarar haifar farar jaririyar ta,
Wacce dunda tazo dubiya ta cilla yatsarta a baki, alamar haƙuri ya bayyana a tare da jaririyar, wacce aka haifa cikin tashin hankali,
Kuka ta fara hakan ya jawo hankalin mutanan da suke ta kaɗa shanun rugar suna gaba dasu cike da mugunta da kuma son zuciya,
Zanin Jikinta ta cire ta naɗe jaririyar da shi,
Kamar daga sama taji wani yace.
"Kawo ta nan"
Bata tsaya jiran abinda zaice ba tai saurin sauyawa yarinyar (GURI) wanda mijinta ya bata,
Da sauri kuma ta faki idanun mutanan wanda suke rufe da fuskokin su, kana tai azabar cillah jaririyar cijin ƙaton kogin dake gudana wanda babu wanda yasan inda ya tsaya,
Tana cillah Yarinyar suna sakar mata harbi.

ABU MALEEKOnde as histórias ganham vida. Descobre agora