ƳAR HIZBA FREE PAGE 4

27 1 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

  *🧕ƳAR HIZBA🧕*
       (PAID BOOK)
                  NA
MARYAM M. SANI (MUM AMNASH)
*WATTPAD:@mumamnas2486*

WANNAN LITTAFIN ƘIRƘIRARRE NE, KUMA MALLAKINA.  BAN YI SHI DON CON ZARAFIN WANI/WATA KO HAƊAKAR WASU MUTANE BA, IDAN SUNA KO HALI YA ZO ƊAYA ARASHI NE.

NORMAL GROUP #200 VIP #300
ACCOUNT: Abubakar Abdullahi Zenith Bank 2083460164
SHAIDAR BIYA, TURA KATIN MTN KO ƘARIN BAYANI : 07038826617

20/R-Auwal/1443 - 26/10/2021

FREE PAGE 4️⃣

Duk yanda ta yi ƙoƙarin guje masa, sai da ya risketa. Fuskarta a turɓune tace "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Ƴar Hizba."
  Murmushi ta saki jin sunan da ya kirata da shi, za ta wuce yace "Don Allah Malama Zainab, ki daure ki cigaba da aikinki kamar yanda ki ka ɗauko..." Cike da tsananin mamaki ta ɗago ta kalleshi. Kanshi na gefe tamkar ba da ita yake ba ya ɗora "Amma kar ki yarda ki yi ƙarkon kifi, kar ki yarda ki zo a gyara ki koma a alakoro. A taƙaice ina nufin ki guji bin rajin ƴan kare haƙƙin mata, don wasu na zurfafawa har su fara kaucewa faɗar Allah da Ma'aiki."

Kafin tace komai, ya yi tafiyarshi. Sai da ta gyara zaman tabaran idonta sannan ta ƙarasa ofishin Malama Sauda jikinta a sanyaye.

Sai da ta ɗan russuna sannan tace "Malama ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Malama Zainab. An ƙaraso?"
"Eh" ta amsa kanta a ƙasa, don sosai Malama take mata kwarjini.

Kasancewar ba a taɓa rasa aiki a hukumar ya sa ta bawa Baby, wasu takardu ta fara duba mata. Ba ta ɗauki lokaci mai tsaho ba ta gama.

Yanayin yanda take sarrafa na'ura mai ƙwaƙwalwa abin sai ya dinga bawa Malama Sauda sha'awa. Duban Baby ta yi tace " Malama Zainab  ina tunanin zuwa sati na gaba, zan yi tafiya  Saudiyya. Wata ƙila na ɗau kusan wata ɗaya a can, da son samu ne ina son na ƙarƙare ayyuka masu yawa kafin na tafi. Da Kwamanda zai yarda ma, da ke zan bari a kujerata zuwa na je na dawo.

Cike da farin ciki Zee tace "Allah ya kaimu da rai  da lafiya, amma Malama akwai manya a gabana."

Murmushi Malama Sauda ta yi tace "Ilimi shi ne ya ke mayar da yaro ya zamto babba, ya zamo abin girmamawa a wurin al'umma. Malama Zainab, haƙiƙa Allah ne ya turo mana ke cikin wannan hukumar domin ki yaƙi abubuwan da mu manya masu aure ba za mu iya yaƙa ba. Amma a matsayinki na mai ƙuruciya za ki yi abunda mu muka gaza. Allah ya yi riƙo da hannunki."
"Ameen" ta amsa kanta na ƙasa.

BAYAN SATI ƊAYA

Sosai Baby Zee ta ware a cikin hukumar Hizba, duk wani aiki da ya taso ta kan shiga ko da ba a sakata a ciki ba.

Wasu na jin daɗin aiki da ita, wasu kuwa tamkar su shaƙe ta suke ji don tsabar tsanar da suke yi mata.

Tun safe da ta zo ta tarar da hukumar a hargitse, danƙar da mata masu yawon dare (Karuwai) da a ka kamo a tsakankanin Kasuwanni da ƙananun otel. Waɗanda ba su saba ba kuka suke yi, waɗanda kuwa suka saba suka zama ƙwanƙwararru babu abinda ya dame su.

Kayan jikinsu kawai ya Isa ya sa zuciyar Musulmin ƙwarai ta raurawa.

Cike da takaici Zee take ƙare musu kallo, suma suna kallonta.

"Assalamu Alaikum" Wani ɗan Hizba ya furta. Da sauri Zee ta juya tace "Wa'alaikumussalam, yaya a ka yi?"
"Bayanan waɗanda a ka kamo jiya za a ɗauka."
"Da kyau, amma bana son ka ƙara dawowa tanan ɓangaren. Su ɗin mata ne, kuma wajibi ne a kanmu mu yi iyakar ƙoƙarinmu wajen kare martabarsu. Kallonsu da shigar da ke jikinsu kawai haramun ne a gareku. Don haka ka koma ka ce, za a kawo in ji Zainab."

Jikin ɗan Hizbar a sanyaye ya bar wajen, duk da bai ji daɗin yanda ta yi masa magana ba, amma ya san gaskiya ta faɗa.

Kai tsaye ya koma ya sanar da Kwamanda, sannan ya koma bakin aikinshi.

ƳAR HIZBA(PAID BOOK)Where stories live. Discover now