Part 7-8

274 23 2
                                        

💞💞💞LAILAH💞💞💞

STORY AND WRITTEN BY

AISHA MA'ARUF

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITERS📚

page 7-8

______________________Washe gari ya kasan ce Wednesday,Husna tayi shirin school,7:15 ta bar gida driver ya kaita,Lailah ko batada lecture tana gida tana barci,ba ita ta tashi ba sai 10:00 na safe, tana tashi ta shiga wanka,bayan ta fito ta yi shafe shafen ta ta sa riga da skirt na less sky blue tayi daurin ture kaga tsiya,dama tayi sifa sannan tayi doughnut da gashin,Masha Allah,tayi kyau sossai dama Lailah ba dai kyau ba,kaman ita tayi kanta,fara ce doguwa amma ba sossai bahhh! tana da jiki kadan not slim not fat,tana da coca cola shape,gata da dogon gashi har baya,abin ka da jinin fulani gaba da baya,she's so cute, tana gamawa ta fita zuwa parlor ta share parlor tayi mop ta gyra TV stand da center table duk ta gogesu,tana gamawa ta shiga kitchen ta wanke kwano nin da ta gani a sink,bayan ta gama ta share kitchen tayi mopping ta fito ta kunna burner na turaren wuta,ko Ina ya dau kamshi,dakin ta ta wuce ta cire bed sheet din tasa wani ta share dakin ta tayi mopping ta wanke toilet,bayan ta gama tayi dakin mama taje ta share ta samata wani bed sheet ta yi mopping ta wanke mata toilet dama mama bata bari suyi na daddy ita keyi dakanta,12:45 ta gama komai taje dakinta ta tube ta daura towel ta shiga wanka 12:55 ta fito bayan tayi alwala ta shafa mai ta sa Ina wear ta sa plain gown da hijab ta tayar da sallah,tana idarwa ta yi adduo'i ta shafa ta tashi ta zauna a kujeran dressing mirror tayi light make up ta fesa turare ta tashi ta bude cabinet dinta ta ciro less dinta maroon color riga da skirt tayi daurin Aisha Buhari bayan ta gama sa kayan,drawer kayan dan kunnen ta ta bude ta dau wani mai adon stone maroon color,Mama na ganin ta tace "Masha Allah habibaty kinyi kyau,sai Ina wannan wankan haka dariya kawai Lailah tayi tace ba inda zani Mama,zama tayi kusa da mama bayan minti 5 Mama tace ta duba abincin dake wuta,da tohhh! Mama ta amsa tana mikewa dan taje ta duba ta samu ya nuna ta saukar ta juye a cooler ta aje gefe sannan ta bude fridge ta dauko pineapple da apple da banana duk tayi juice dinsu ta diba duka tasa a jug ta ajiye ma daddy nashi a fridge nasuma tasa kafun su ci abinci tana gamawa ta dauko abincin ta ajiye a dining ta dawo parlor ta ce na gama Mama ta kwanta ta daura kanta saman cinyan mama mama na shafa kanta suna hira.

2:00 Husna ta dawo daga school tatadda su Mama a parlor rungume Mama tayi ta gaishe ta da Anty Lailah,Lailah tace ni dai kar akaryamin uwa wannan irin rungumar,Allah yasa dai baki gautar mata da kashi ba,ta karasa maganar ta tana dariya,Mama na tayata,turo biki Husna tayi tace Mama kinga Aunty Lailah kohhhh! kullun sai ta nemi tsokana na,dariya Mama tayi tace kyaleta auta na,zamu fasa zuwa outing din da ita,da tsauri Lailah ta rungume Mama tana bata hakuri tace ayya mama na,farin ciki na,first love dina,my happiness,my world,my everything,haba mama na ayi hakuri,ba zan sake ba,dariya Mama tayi tace"I dama k awurin dadin baki A1 ce,tuni sai ki chuci mutun da dadin baki,dariya Lailah tayi tace ayi hakuri Mama aje dani,Mama tace tohhhh! naji uwar zance da dadin baki,yauwa Mama na,tana ma Husna gwalo Mama,kinga aunty Lailah ko, Mama tace ni kam ban iyawa da fitinar ku,tashi tayi tana tafiya tace kuyi ku shirya karfe uku (3) zamu tafi,da tohhh! Mama duk suka amsa,dakin su duk suka nufa,Husna na shiga ta cire uniform din ta ta daura towel ta shiga wanka,bayan ta fito ta shafa lotion dinta ta fesa turare tayi light make up,tayi kyau sossai Masha Allah,drawer ta bude ta ciro material mai kyau gaske da kudin shi zai kai kimanin dubu 50,kayan kalan pink ne,saka kayan tayi,sannan tayi dauri mai kyau na zamani, gyale da takalmi da jaka ta dauka duk kalan pink,bayan ta gama shiri ta kara fesa duka jikin ta da turare,sossai autan Mama tayi kyau Masha Allah,a ban garen Lailah bayan ta shiga daki wanka ta shiga,bayan ta fito ta zauna ta shafa lotion,tana gama shafawa mai ta hau make up,tana kammalawa ta tashi ta bude drawer ta ciro gezna kalan sky blue,an mai dinkin dogon riga ya sha aiki daga sama har kasa,akan gado a jiye kayan,bangaran inner wears ta bude ta chiro leggis da bra kalan sky blue tasa kafin ta saka gown din ta,bayan ta kammala shiryawa ta kwance gashin ta data kitsa,combing gashin tayi ta shafa mai ta kama gashin da ribbon sannan ta saki jelan gashin a bayan ta,dankwalin kayan ta daura,tayi kyau sossai kaman ka sace ta ka gudu,tana gamawa ta dauko jaka,takalmi,gyale duk kalan kayanta tana kammalawa ta fito hannun ta rike da gyale,a corridor ta hadu da Husna itama ta fito,"wow antyna kinyi kyau sossai ta fada tana blowing mata kiss,murmushi Lailah tayi tana jan kumatun ta "tace ke ma kinyi kyau Auta",wayyyyoooo! Aunty na zaki bata min kwalliya na,"dungure mata kai Lailah tayi tace ja'ira kawai",muyi hoto Anty kar wannan kwallian yayi waste,selfie su kayi kusan guda goma,zata kara daukan wani Lailah tace"wlh baki isa ba,na gaji,ke ko gajiya baki yi,parlor suka sauko,after 5min Lailah tace ma Husna ta duba ko Mama ta gama,da toh ta amsa ta haura sama,dakin Mama ta bude ta shiga bakin ta dauke da sallama,a zaune ta sami Mama ta gama shiri tana waya,tsayawa tayi ta gama wayan,Mama mun gama,girgiza mata kai mama tayi tace tana zuwa,da toh Mama ta amsa sannan ta fice daga dakin,bayan saukan Husna da minti goma Mama ta sauko,Masha Allah kunyi kyau yan matan mama,Husna ce tace Mama muyi selfie,tsayawa Mama tayi Lailah ta dauke su hoto sannan tayi da Lailah kafin su kayi dika,Mama tace to muje tunda angama,da toh Lailah ta amsa sannan ta kashe TV,Mama da Husna suka fita,bayan Lailah ta gama kashe komai ta fito ta kulle kofan ta same su a mota,shiga motan driver yaja suka bar gidan direct shop rite suka nufa,suna kai wa driver yasa mu wuri yayi parking suka fito suka shiga ciki,basket duk suka dauka,suka fara daukan abin da suke so,bayan minti 30 suka kammala wurin lissafin kudi suka nufa inda ya kama 500,000,ATM Mama ta bada aka cira kudin,akayi packaging duk abin da suka siya a laida,daukan laidodin workers su kayi zuwa gurin mota driver ya bude musu suka shirya laidodin a ciki,kulla booth din motar yayi sannan ya zagaya ya shiga driver seat ya tayar da motar suka bar harabar wurin,daganan wurin wani shakatawa suka tafi,basu suka bar wurin ba sai biyar da minti sha biyar 5:15 suka kama hanyyan gida,a hanyyan su ta komawa suka tsaya a wani shago suka siya ice cream da shawarma,burgher,doughnut, chin-chin da chocolate,bills din suka biya wurin counter kafin suka fice daga shagon,suna shiga driver ya ja mota,suna cikin tafiya suka ga mai sai da fruit Mama tace a tsaya,fita tayi ta siya orange,pineapple,Apple,Watermelon,da banana,aka hada mata komai a Leda ta biya kudi ta sa driver ya bude booth tasa a ciki ya kulle,mota ta shiga shima ya shiga ya tayar suka tafi gida basu suka kai ba sai karfe shida da minti arba'in da biyar suna kaiwa gida duk suka sauka a gajiye,driver ya bude booth suka fara kwasan kayan shima ya taya su,bayan sun gama ya kulle booth din da motan ya kama hayyan masallaci su Mama suka shiga ciki aka aje kowanni a mazaunin shi suka je sukayi sallah bayan sun idar Lailah da Husna suka shiga kitchen suka girka jellof din spaghetti yaji bushashen kifi,sai tayi pepper soup,a cikin 1 hour suka kammala komai Husna ta wanke kwanonin da suka bata Lailah kuma ta goge kitchen,banyan sun kimsa kitchen suka kai abincin dining table,Lailah ta bude fridge ta ciro juices din da tayi dazu ta aje bisa dining,sallah su kayi,bayan sun idar suka sauko a parlor suka tadda Daddy har ya dawo yayi wanka duk suka rankaya zuwa dining,Lailah tayi serving din su,bayan sun kammala Daddy yace ya shopping din,mai aka siyo min,Mama tace fruit ne Alhaji sai su kayan flour,amma sauran kayan kwalliya ne,Daddy yace toh ni ina nawa kayan kwalliyan,dariya su Mama da Lailah su kayi,"mai zaka yi da kayan kwalliya Alhaji cewar Mama",mai kuke yi da shi,"dariya su Lailah kawai suke",toh gobe zanje na siyo maka insha Allah,yace a'a na yafe,ni mai zan yi dashi,i sai ku,ni yanzu akawo mun su fruit din,da toh Mama ta amsa,Lailah da Husna suka tashi suka dauko laidojin fruit din dana doughnut suka kawo dining,kitchen Lailah ta shiga ta dauko plate da ruwa a roba ta wanke kankanan ta yanka a plate,Husna na taya ta,bayan ta gama yankawa ta miyarda sauran da ya rage da ruwan da ta wanke kankanan dashi ta zubar da ruwan ta dauriye roban da wuka sai tasa sauran fruit din a fridge ta fito ta ja kujeran dining ta zauna ta fara cin fruit,bayan sun gama suka hau kan kayan flour,akaci naci akabar na bari,suna gamawa Daddy da Mama suka nufi parlor,Lailah da Husna suka kwashe kwanonin suka Kai kitchen,Husna ta fara wanke kwanonin Lailah kuma ta share dining,bayan sun gama aikin suka dawo,parlor Suka zauna suna hira sai wurin 10:00 duk su kaje suka kwanta,Asuba ta gari......................................

Kubiyoni dan karanta cigaban labarin.

Comment
and
Share

💝💝💝.

💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE) Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang