ƳAR HIZBA(FREE PAGE 1)

123 4 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

        *🧕ƳAR HISBA🧕*
             (PAID BOOK)

                  NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486
BLOGSPOT@mumamnash.blogspot.com
*Watsapp link* https://chat.whatsapp.com/Gty1kpVjvrb2myAy87gOou
BISMILLAHIR-RAHMANIRRAHIM

WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE, KUMA MALLAKINA, SUNA, SUNAN GARI KO UNGUWANNI DUK ƘIRƘIRARRUNE. BAN YISHI DON CIN ZARAFIN WATA HUKUMA KO WANI MUTUM BA, IDAN HALI YA ZO ƊAYA TO ARASHI NE.

  *Assalamu Alaikum gareku masoyan littafan Mum Amnash, insha Allah idan anyi sallah babba da sati ɗaya zan fara wannan littafin na ƳAR HISBA  bazance komai ba akai, amma insha Allah zai ƙayatar. Littafin na kuɗi ne za'a biya kuɗin karatu naira #200 normal group, #300vip posting sau biyu a rana, Waɗanda ke son special kuma #400 a dinga tura musu ta pc. Masu buƙata su tuntuɓeni ta wannan number 07038826617*

9/7/2021

     FREE PAGE1️⃣

      Tana sauka daga Adaidaita sahu ta nufi ofishin Hizba na ƙaramar hukumar TSOKUMBO da ke jahar KADABO, Fuskarta lilliɓe take da niƙafi ko ƙwayar idanunta ba'a gani.

  Kai tsaye ta wuce ciki, mai gadi da hankalinsa baya wajen ya fara kiranta "Ke! Ke!!" Amma ko juyowa ba ta yi ba tayi gaba. Jin takun sahunsa a bayanta yasa ta cake, kafin ya furta komai ta ɗage niƙaf ɗin fuskarta, Suna haɗa ido ya haɗiyi wani busasshen yawu yace "Jeki"  Kai tsaye ta shige ciki, kan bencin da masu ƙara ko ƙorafi suke ta zauna, tana ƙara nazartar yanayin wajen a gabanta Shugaban ya shiga ofishinsa ya zauna.

Masinjansa ne ya shiga da sauri riƙe da wasu takardu, a ƙalla sai da ya kwashe kusan minti goma sannan ya fito, Matar da ke gefenta yace "Ku shiga" da sauri kuwa suka shige ciki ita da wata matashiyar yarinya mai goyo, basu wani jima ba suka fito, ɗan jim ta yi ko za a ce ta shiga ta ji shiru, kawai sai ta miƙe ta nufi bakin ofishin.

Cikin siririyar muryarta tayi sallama "Assalamu Alaikum" da sauri Kwamanda da ke waya ya juyo, da hannu ya nuna mata Kujerar zama, ta zauna sannan ta buɗe jakarta ta zaro wasu takardu ta ɗorasu a kan teburin da ke gaban Kwamanda, sannan ta koma inda ta taso ta zauna.

Hakan yayi daidai da kammala wayarshi, "Wa'alaikumussalam mene ne ya ke tafe dake?" Takardun gabansa ta nuna masa sannan tace "Allah ya gafarta Malam aiki na zo nema."

"Wa yace miki muna ɗaukar sababbon ma'aikata?"
Cikin sassanyar muryarta tace "Ba wanda ya faɗa min, na zo a ɗaukeni aikin sakai ne  bana buƙatar wani albashi ko wani tagomashi, zan yi domin Allah."

Fuskarshi ya ƙara ɗaurewa kamar ko yaushe sannan yace "To dama mu ai aikin Allah muke yi, ko ana bamu wani abu to ihsani ne, sannan  mudai ba mu da buƙata a  halin yanzu, sai ki tara gaba, ko ki nemi wani aikin ina ganin zaifi.

Niƙaf ɗinta ta ɗage fuskarta ta bayyana, kyakkyawace ajin farko kuma fara tas, tanada manyan ido mai ɗauke da dogon baƙin gashi, tana do dogon hanci mai tudu da ya dace da fuskarta mai matsakaicin faɗi.

  Ɗago idon da Kwamanda zai yi suka haɗa ido, bai son lokacin da wayar hannunshi ta zame ba, "Lahaula wala ƙuwwata illa billah" ya furta a fili, a zuciyarsa kuwa cewa ya ke ta yaya ma zan yarda mu ɗau wannan aiki anan, ai barin irin waɗannan matan a wuri haɗari ne mai girman gaske...

Miƙewa tsaye tayi ta tattara takardunta ta tura jaka, ssnnan tace "Akaramakallah zan wuce yanzu sai haɗuwa ta biyu, tunda na biyo ta ƙa'ida ban sami fa'ida ba Insha Allahu zan karya ƙa'idar kuma na sami fa'idar, mu haɗu a babban hedkwata."

Cikin sassarfa ta fice daga ofis ɗin, idanunta na tsiyayar da hawaye, da yake da niƙaf bata damu da share hawayenba, tana samun adaidaita sahu ta haye ba tare da ta faɗa masa inda za ta je ba. Allah ya gani ina son aikin HIZBAR nan ba don komai ba, sai don na bawa addinina gudummawa da ƙarfina da aljihuna, amma sai gashi ana neman yi min sakiyar da ba ruwa, a fili tace "Yaya Falmata" murmushi ta saki tunowa da ƴar uwarta mai ƙaunarta... Mai adaidaita ne ya katse mata tunani yace "Hajiya ina muka nufa ne?"  "Zoo road" kai tsaye ya juya kan babur ɗin suka ɗau hanya.

ƳAR HIZBA(PAID BOOK)Место, где живут истории. Откройте их для себя