"Ɗauka mana! Ko sirikin nawa ne kike jin kunya"
Dariyan yaƙe nayi nace "A'ah fah, wata ce ki bari kawai zan kira ta daga baya idan na koma gida"

"A kan me? Idan kuma wanj babban uzuri ne fah?"
Miƙewa nayi na nufi hanyar fita da ƙarfi ta jawo ni na dawo na zuba saman kujera,

"Munafuka, babu inda zaki je ki ɗauka a nan naji waye tunda nace kina da saurayi kin ƙaryata ni"

Bani da zaɓin da ya wuce nayi picking na ƙara a kunne tare da sallam ina ƙifi_ƙifi da ido,

Daga yanda naji muryan zayyad nayi sensing akwai wata matsala don banji shi cikin fara'a da dariya kaman ko yaushe ba, gaida shi nayi cikin ladabi bai amsa ni ba sai cewa

"Babes I'm very sorry lallai na zamo miki ɗawainiya har yanzu abinda nake son bai samu ba"

Kallon aunty Aisha nayi wanda ta ƙura min idanu na sake sauƙe kaina sannan cikin ƙasa da murya nace "wani abu ne ya faru hamma zayd?"

"Bani so kiyi tunanin yaudaran ki nake yi Saudat, har cikin jini na nake son ki amman kiyi min alfarma ki jira ni nan gaba kaɗan, for the maximum of 2 years zan saita komai ya zamo dai_dai yanda za'a bani auren ki indai ina da rai, kada ki amince da wani Please wait for me"

Shiru nayi na kasa amsa shi saboda nauyin amsan da nake son bashi da kuma idon aunty Aisha amman shi yayi tunanin request ɗinshi bai karbu bane yasa yaci gaba da roƙo na,
"Please, Please ki taimaki rayuwata baby, zuwa lokacin na zamo mai ƴanci na tashi daga ƙarƙashin kulawar iyaye na da babban yaya kuma zan iya kula dake harma da yaran da zamu aifa nan gaba but please wait for me"

Tashi daga zaune Aisha tayi da nufin bani wuri ganin hawaye na zuba a idona nayi saurin riƙo hannunta ta dawo ta zauna domin ina matsanancin buƙatar shawara a yanzu sannan na katse kiran ina fashewa da marayan kuka,

"Meye haka saudat? Waye ya kira ki? Me ya saka ki kuka?" Ta faɗa tana share hawayen idona da ya kasa yankewa,

"Kiyi magana mana saudat, zan ɓata miki rai fa bani son sakarci"

"Aunty ban san yaya zanyi ba dan Allah ki bani shawara..... ni ba mayaudariya bace amman garin rufe sirri na nayi masa ƙarya kuma na barshi cikin rashin fahimta, bai san ni wacece ba, bai san matsayi na ba bai san asali na ba gashi yayi nisa a sona, na kasa faɗa mishi gaskiya aunty Aysha"

"Kinyi kuskure babba Saudat da kika ɓoye masa ke wacece, don ba'a taba ɗaura soyayya a kan ƙarya, abinda ya fara cutar da auntyn ki yusrah kenan rashin cikakkiyar sani a kan wanda take zaune dashi..."

"Duk abinda zan faɗa mishi a yanzu ba zai saka ya aminta cewa bani da niyyan yaudaran shi ba aunty.... bai taɓa ɓoyemun komai ba harta rashin lafiya da yake fama dashi na jinnu da ake ɓoyewa duniya ya bayyana gare ni, sannan duk lokacin da zai buɗe bakinshi ya furta min wata kalma yakan kasance gaskiya ni kuma a ko yaushe akasin gaskiyar nake faɗa mishi"

"Ita gaskiya dokin ƙarfe ce Saudat, zata iya jin ciwo ma wanda yake kai amman ba zata taɓa bari ya auka ba, ta yuyu gaskiyar zai mishi ciwo amman ko babu komai zuciyar ki zata samu nutsuwa zaki samu sauƙi daga dukkan fargaba"

"Ba lallai na same shi ba, saboda zayyad yayi min nisa, kada nayi kuskuren sanar ma kowa sirri na domin hamma khamis ba zai taɓa yarda da hakan ba ya kawo ni nan ne don tseratar dani daga al'amarin da ya gabata a rayuwa na da kuma wanda yake bibiyar shi, aunty yusrah ta gargaɗe ni sau tari da wa'innan kalaman ba zan iya ba aunty Aisha......inaga kawai haƙuri zamuyi da juna °i no desty to is him (I'm not destined to be with him)" na ƙarasa tare da saka ƙasan gyale na ina share hawayen dake faman sintiri saman fuska na kuka na daɗa kufce min,

Cikin zafin nama Aisha ta fincike hannu na tana bina da mugun kallo,
"A kan me zaki nemi taimako daga wurin wanda ta kasa tsaida ma kanta decision ɗaya lokacin da take cikin halin da ya kusa fin naki muni,
Yusrah aminiyata ce na santa ciki da waje amman sai yanxu na fahimci ita ɗin mai son zuciya ne kanta kawai ta sani.... A irin haka ne ta kasa yiwa khamis hukunci lokacin da ya dinga azabtar da ita, bata nuna mishi ita ɗin mai ƙima bace ta koma wurin shi cikin sauƙi bayan ya dawo gare ta, ba don shi ɗin masoyin asali bane yanda ta nuna mishi zallar soyayya da tuni ya watsar da ita a kwandon shara,

Yanzu ta zaɓi ganin hawayen ki da kasancewar ki maƙaryaciya a kan farin cikin ki? Ta zaɓi ki rasa komai wajen rufe abunda watan wata rana dole ya fito? Wa ya faɗa mata zayyad yayi miki nisa? wa...ya...faɗa..mata? Oya ɗauki waya ki kira shi ki faɗa mishi duk gaskiyar ki ai aure kika yi a can baya ba zina ba"

Ɗaukan wayan nayi da ƙarfin gwiwa don kalaman ta sun shige ni sosai har danyi dialling numbern zayyad sai kuma na fasa na juyo don tambayan ta,
"Idan abban jannat ya samu labari fa! Yaya zanyi?"

"Wani lokaci sai munyi taking eisk kafun mu samu wasu abubuwan a cikin rayuwar mu, indai yana son ki da gaske kaman yanda kika faɗa khamis saidai ya samu kyakkyawar labari a sanadin hakan da kikayi, kira shi yazo"

"Allah yasa" nace lokacin da kiran ya shiga kaman mai jira ya ɗauka, nayi mishi kwatancen gidan aunty Aisha a kan yazo zamuyi magana sannan na kashe wayan,

  ****
"Na san na ɗaga maka hankali na saka ka fito daga gida kayi haƙuri"

"Babu komai boɗɗi, ki sanar min abinda ya saka kika min wannan kiran gaggawan Allah yasa ba wani abu ne ya kuma faruwa ba"
Ya faɗa yana kallon fuska na da yayi jaa ga kan hanci na kaman wanda aka baɗa wa yayi, idanu na sunyi ciki_ciki alamun nayi kuka duk kwalliyan fuskana na goge shi a jikin gyale na garin share hawaye bai ankare ba sai gani yayi wasu hawayen suna bin kunci na, kafin yayi magana nayi saurin tare shi,

"Kayi haƙuri ya zayd, ba zan iya auren ka ba don ban dace da kai ba"

"What?! What are you saying? Ban fahimce ki ba"

"Ni BAZAWARA CE hamma zayd, na taɓa yin aure da wani a baya"

Shiru ne ya ratsa tsakanin mu na ƴan sakwanni, ya kasa gaskata abinda kunnuwan shi suka ji, ta yaya za'ayi yarinya mai shekaru 15 zuwa sha shida kacal a duniya ta kasance bazawara? Me yake faruwa ne? Ya tambayi zuciyar shi,

Jin yayi shiru yasa na fara masa bayanin abinda ya faru gudun zargi "ni ba ƙanwar khamis bace, iyayen shi ba su bane nawa kuma bamu haɗa wani dangantaka na kusa ko na nesa dashi ba, iyaye na suna can ƙauyen wuroɓokki kuma a can nayi aurena na farko" daga nan na kwashe labarin aure na da YARIMA da zama na dashi har izuwa mutuwan shi da kuma yanda baro ƙauyen, zuwa lokacin idanun zayyad sun gama tara ruwa ƙiris ya rage su sauƙo saman fuskar shi,

Ɗaga kanshi sama yayi iskan fanka yana fifita mishi idanun shi ko zai samu ya iya controlling kanshi,
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel..... La ilaha ha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin"

"Yanzu ni korarriya ce, bani da ikon shiga cikin wuroɓokki domin da sun ganni kashe ni zasuyi, tun ba yau ba ma naso kaika wurin mahaifi na mu gwada magani ko za'ayi nasara amman saboda wannan dalilin na gagara, ta yaya korarriya ta dace da mutum mai gata gaba da baya irinka? Kada ka manta kai saurayi ne ni kuma sauran wani"

Kifa kanshi yayi saman cinyar shi zuciyar shi yana suya, shi yayi tunanin ƙaddarar shi shine mafi ƙunci da wuya amman ashe akwai na wanda yafi nashi ƙuntatuwa, tunda shi yana cikin ƴan uwan sa ko wani garin Allah idan ya waye yana ganin Mahaifiyarsa tare da mahaifin sa ga ni'ima da wadata da Allah yayi musu,

"Saudat koda ƙaddarar ki tafi haka muni bani da matsala kuma na yarda dake a hakan nake son ki, ban damu ba, kuma ba zan saurari maganganun wasu mutane ba,
Ba kyanki ko kuma budurcin ki nake so ba, ke ɗin nake so zuciyar ki nake son samun matsuguni, buri nake ki zamo uwar ƴaƴa na kuma surkuwar mahaifiya ta, muradina kawai ki kasance ƙarƙashin inuwar aure na"

"Amman dangin ka fa? Zasu amince?"

**********
Anyi Sallah da sati 2 kowa ya watse muka ɗau hanyar makaranta, sabon tafiya sabon rayuwa,
Fiye da rabin damuwa na sun ragu don tun daga ranar da na bar gidan su zayyad babban yaya ya fita sha'ani na kwata_kwata ko magana mai tsayi bayi shiga tsakani na da shi amman bai fasa min kowa ba cikin hidiman da ya saba, kafin na tafi school ma saida su aunty yusrah suka kwashi rabon su don idan ya waiwaye mu mukan jiƙa sosai,

Na fuskanci abubuwa da dama wanda suka ɗaure min kai lokacin da na shiga makarantar don a lokacin da za'a kaini ganin niƙi niƙin shopping da sulaiman ya saka a kaini dashi nayi tunanin yawan shi ya tsananta amman da naje naga yaran dake rayuwa a wurin irin tsadadden rayuwan da akeyi na ƙarya da tsananin gaye, jinkai, competition na nuna dukiya, da kuma gasar ilimi sai na ganni ni ba kowa ba a gaban su.............🤦🏻‍♀️

Love You my fans🥰

#team SS💙
#team SZ❤️

*Ummu Najma ce😘*

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora