Part 10/11

371 22 0
                                    

🐲🐲🐲
           UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based on true Life Story)(full of sorrow)

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist

Dedicated to.
My New Born Baby.
Allah ya rayamin ke cikin baiwa da hazak'a,yabawa mahaifiyarki lafiya da kwanciyar hankali duniya da lahiri,ya bud'ewa mahaifinki wato My best Broza,Allah ka rayashi tare da Anti deejersa,tnx 4 giving me a baby.

(10)&(11)

Uhm bayan rabuwa ta da Khamis da wata uku, yasamu karayar arziki inda duk wani duk'iyarsa ta lalace yazama babu komai se gidan dayake ciki.

Mama tana farincikin natafi zataci arziki ta aura masa wacce takeso,kwatsam saitaji labarin cewa aiii gobara ta kama gidan mai na Khamis, kuma b'araryi sunje company d'insa sunyi sata sun tafi da motar da'aka kawo masa kaya aciki.

Tashin hankali tashiga sosai,shi kuwa Khamis be wani damuba sosai,saboda rashin matarsa dayakejin zafinsa,kuma dama Malamai sunsha fad'a masa matarsa tana da arziki a jiki itace silar arzikinsa.

Zuwa tayi gidan tana kuka,tace".....Khamis kayi hak'uri da abinda yafaru,daman nasan tunda ka rabu da yarinyarnan nasan bazata barka a banzaba to nima nayi alk'awarin bazan zauna banza ba.


Yace"....haba Mama kidaina cewa haka ni nasan Fatima bazatamin komai ba kawai de k'addarace Allah ya bamu ikon cinyewa."


Da sauri tace"..... Kaide Allah yabaka ikon cinye  jarabawa,amma wannan ba k'addara bace,kuma wlh saina d'auki mataki akan yarinyar nan,fuu ta fice ta barshi cikin tunani."

Allah kabamu iyaye na gari Amin.

*************************

To mutumin damuka had'u dashi ya nacemin damaganar aure,nikuma sam aure baya raina,amma tsabar naci seda yaje har gun kawu na yamasa magana.

Daganan kuma kawu na yace"....dole nayi aure ko inaso ko banaso,haka na hak'ura na yarda da auren.


Uhmm Mahaifiyar Khamis najin zanyi aure taje ta samu boka tace masa ya hana auren gaba d'aya,haka kuwa akayi har lokacin da'akayi zasu kawo kaya basu   kawo ba kuma har lokacin be daina zuwa guna  ba,nima kuma ban hanashi ba saboda nasan ina sonsa amma bada aure ba.

Uhmm Allah kamana mafita me kyau.

Shekarar mu d'aya da Ahmad amma babu maganar aure a junanmu,duk da muna mutuk'ar son junanmu amma ba halin auren juna.

Ana haka ne na tsinci kaina da samun juna biyu,wato inada ciki.

Tashin hankali na shiga Mara misaltuwa nan na sanar da Ahmad yace".....yana son abinsa amma na bijire nace wlhh saina cire cikin to na haifeshi da wani ido zan k'alli jama'a?"

Don haka naje na samu wani likita nace"....don Allah ya zubarmin da cikin,yace"....cikina yanzu watansa daya na bari se ya kai wata uku,haka na tashi na koma gida badon raina yaso ba.

Kuma banfad'awa kowa ba,saboda tsoron abinda ze biyo baya.

Cikina nakaiwa wata biyu na koma gun likitan,nan yabani wani magani yace nasha zai fita,duk da ina tsoro amma haka naje nasha maganin amma kusan kwana biyu magani yak'i aiki.

Na koma na fad'a masa yak'ara bani wani,amma the result is the same.

Don haka nakoma gun wani likitan saboda azatona wannnna bayason yamin abinda nakeso,Uhm anya Fatima daga gunsane kuwa.


Sabon likitan Dana canzama haka the same thing,haka naketa canza doctors Amma duk d'aya, harna gaji nadaina zuwa gun likitoci kuma ko irin laulayin masu ciki banayi.


Haka naketa zama sainaji Allah ya d'auramin son abinda ke cikina,don haka sena yanke hukuncin fuskantar komai akansa.


Uhmmm Anya Fatima zaki iya kuwa.

To muje zuwa donjin abin al'ajabin dake gaba.

Taku a kullum:::Young Novelist.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Alk'alamin Auta

UQUBAR UWAR MIJINAWhere stories live. Discover now