Part 18/19

340 22 0
                                    

ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain.

🐲🐲🐲
         UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based On True Life Story )(Full Of Sorrow)

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist

Dedicated to
Fans,Allah yabar k'auna, nagode matuk'a,banda bakin godemuku sede nace"...Allah yabar k'auna.🤝🤝.

(18)&(19)

Yau da safe bayan mungana ayyukanmu nace"...Goggo inaso naje nagaida su Mama,tace"...toh Allah yakaimu anjuman,Amin."

Tun alokacin nakejin gabana nafad'uwa nakejin sauyi ajikina,Amma sena alak'an tashi dacewa k saboda zan tafi da Fatima gidanmune abun yana bani kunya kuma dawani ido zan kalli su Baba.

Shiryawa nayi nad'auki  jakata Wanda kayanmu ne aciki ak'alla zasukai Kala goma,sallama na musu nafito cikeda kewarsu.

Harna fita senaji kamar namanta wani abun,komawa nayi nace"....Goggo anya banyi mantuwa ba kuwa?,tace"... Mantuwar me kuma Fatima to ki duba."

Zama nayi kamar karna tafi harseda  Goggo tace"....ko kunfasa tafiyar ne?.nace"...A'a zamu tafi daga haka na tashi nace"...toh Goggo ayafi juna nizan wuce Sena dawo,tamin adawo lafiya nafita."

Gun shiga motoci na nufa inaji  ana k'iran sunan cikin garinmu anma banshiga ba,kawai sena nufi inda naji ana k'iran kano.

Zama nayi kuma nandanan motar tacika muka kama hanya,a zuciyata nake tunanin to ina zanje kuma gunwa zan sauk'a nida banida dangi acan,Nide kawai zuciyatace take bani umarnin danaje kano.

Da yamma muka iso kano  saboda akwai tafiya tsakaninsa da yobe,bayan mun sauk'a a park sena nemi wani bench nazauna nasiya abinci mukaci.

Toh muna zaune har magrib  har isha'i har mutane suka fara bajewa,amma narasa inda zan nufa.

Goyon Fatima nayi nafara tafiya batare da sanin inda na dosaba,Can misalin k'arfe goma nazo gun wata bukkar mai shayi nazauna.

Mutane nagani suna isowa gunmu da sauri natashi nafara tafiya cikeda fargaba,wani lungu na lab'e sunzo wucewa  sai abunda yake cikin buhunsu ya fad'o.

Wani wawan ihu nayi ganin kan mutum aikuwa da gudu na fantama na jefar da wayata da kayana,aikuwa suka bini da gudu babban su yace"...Ku d'akko mana yarinyar Ku kashe uwar."

Jin an ambaci kashemin Fatima ne yasani k'ara speed harnazo bakin titi,wata motace tazo wucewa nafara d'aga musu hannu ina Neman taimako amma bata tsayaba kuma ga mutanen sun kusa kamoni.

Wata jeep nagani da gudu nashiga gaban na tsuguna nace"...Dan Allah a taimakamin,Wata matace tafito tace"....lafiya meyafaru?".


Da hannu nake nunamata waenda sunkusa zuwa nace"....Zasu kasheni kitaimakeni,da sauri tabud'emin motar tace"....shiga muje ina shiga suka iso gun da gudu ta figi motar muka bargun."

Daya daga cikin sune ya jefi motar da wata adda,aikuwa yasamu glass d'in motar kuma dai-dai inda nake, aikuwa glass d'in yafashe yasamu fuskar Fatima nan da nan goshin Fatima yafashe.

Ihu nayi  nace"...innalillahi Fatima!Fatima!!Fatima!!!,amma ina ta suma,muna shiga cikin garin kano tayi asibiti damu."

Muna zuwa  aka k'arbeta akayi emergency da'ita,bayan kamar minti 30 aka fito da'ita harta farka kuma anmata dressing d'in gun.

Matar ce ta k'arbeta tana mata sannu,ta sallame su sannan tace"... Muje gida ku huta dare yayi.

Haka nabita muka shige motar,haka kawai naji matar ta kwantamin arai,kobabu komai  ai Allah ya aikota tacece mu.

Wata unguwar masu kud'i  muka nufa,unguwar babu gidaje sosai sai manya manyan gidaje tsirara.

Wani Babban gida muka nufa tayi horn aka bud'e babban gate d'in, shigar da motar tayi sannan ta umarceni dana  fito.

Wani Babban k'ofa ta nufa ina biye da'ita, Babban parlour ne mai cikeda kayan alatu ga manyan kujeru komai kana gani kasan na masu dukiyane.


Zama nayi a k'asa ina rik'eda Fatima,tace"....Hau kujera ki zauna y'ata ina zuwa. "


Abinci takawomin da ruwa,rabona da abinci tun safe kuma shima nacine ba cikin kwanciyar hankali ba saboda yadda gabane ke fad'uwa ashe abinda ze samemu kenan.

Abincin naci nabawa Fatima itama,sosai mukaci saboda muna tare da yunwa.

D'aki tanunamin tace"....kishiga kije kiyi wanka itama kimata wanka na ajiyemiki kaya akan gado."

Tashi nayi ina jinjina tausayawa irin na matar nan kuma tayarda dani batare da tasan ni wacece ba,haka na shige nayi wanka nayiwa Fatima nasaka kayan danagani akan gadon.

Kwanciya nayi  a makeken gadon dake d'akin, nandanan bacci mai dad'i ya d'aukeni.

To Asuba Tagari Fatima Anti Fatima Ummin Fatima.

Allah ya yayemiki abinda ke damunki aduk inda kike.😭😭😭😭😭😭

Taku a Kullum.
My New Fb Account For My fans,4 ur comment nd ideas.
(Hajaratou Bintu Muserh.)Add up u gonna get any answer to ur Questions.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Alk'alamin Autah.

UQUBAR UWAR MIJINAWhere stories live. Discover now