Part 26/27

305 23 0
                                    

569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soo golden a pen,We writer's assiduously percieven No pain,so Magical Our creative golden pen,Be hold our worlds,A product of our pen savour Our worlds for it will  cause u no pain~*


🐲🐲🐲
          UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based On True Life Story(Full Of Sorrow).

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.

Dedicated to
  Granny Ummee Aysha.
Allah yak'ara lafiya yaci gaba da baki kwazo akan komai na.

Hmm inamatuk'ar ji da comment dinku fans,musamman Anti Fauziyya,Mrs Ridwan.

Safe trip Ummin Naeema,Allah yakaiku kuma yadawo daku lfya,gonna miss u.

(26)&(27)
     
               Ina zuwa bada b'ata lokaci ba naje gunsu amma kash anmusu transfer zuwa wani garin,tashin hankali nashiga sosai nabar gun jikina,kwakwalwata,zuciyata dama komai nawa ciyo suke min.

Haka nazauna a cotonue na sati d'aya amma narasa abin yi,bayan sati biyu na koma kano inda naji mummunan labari Wanda ya kusan tafiya da kwakwalwata dama rayuwata gaba d'aya.

Bayan na iso bantadda Baiwar Allahn  a gidanba,tana dawowa tafara cewa ina kikaje? haka nan nafad'a mata meke faruwa,zama tayi takama hannuna tace"...Fatima kiyi hak'uri da abinda zan fad'amiki Dan Allah kisama ranki ruwan   sanyi".

Tsoro ne yakamani nace"....meyafaru ne wai kiketamin waennan maganganun?,a hankali tace"...ke musulmace kinyi imani da k'addara,Allahn dayabaki Fatima ya karb'i abinsa,Allahn dayafiki sonta ya amsheta sede kiyi hak'uri. "

Nayi tsawon minti ashirin ban motsa ba tunanina ya tsaya cak, bana fahimtar komai kamar ma ba'a duniyar nakeba.

Jijjigani tayi sosai tukun na motsa,ina tuno abinda yafaru kawai senayi dogon suma.

Bantashi daga sumar danayiba seda nayi kwana uku,da kuka matashi inacewa Dan Allah Fatima karkimin haka wlh nayarda na  mutu ki rayu,Wayyo Allah na Fatima kidawo bazan....kawai senasake suma bansake sanin inda kaina yakeba se bayan kwana hud'u,Ashe allurar bacci akamin don likitan yabada tabbacin inhar na tashi to zaniya zaucewa.

Dana farka ina kuka ina r'okama y'ata gafara gun Allah,Matar ce ke bani hak'uri da lallami.

Gidnata muka koma nazama ba uhm ba uhm uhm,ko abinci setayi dagaske,danace zanje gun Hajiya tace".....ai  batanan tayi tafiya kuma natambaya bansan inda tajeba kuma randa akayi rasuwar ta tafi.

To bayan tafiyata abinda yafaru a gidan Hajiya inda Fatima take SHINE.

Wannan ganin dana musu randa zantafi  Cotonou, to bayan sunje asibiti akabasu gado,bayan kwana biyar ta warke sosai har sun dawo gida.

Kunsan yadda ciwon kyanda yake,to sanadiyyar sane ta rasa ranta.

Haka akamata sutura aka kaita gidanta  na gaskiya.

To ita kuma Hajiya tayanke  shawarar zuwa gun iyayena tunda tanada labarina kuma tasan garinmu,hotunana dake gunta ta d'auka se Wanda tayiwa gawar Fatima da wanda mukayi tare da'ita da Y'arta.

Batasha wiya gun gano gidanmu ba,bayan taje sun tarbeta hannu biyu suka nemi susan daga ina take kuma watake nema tunda basusan taba.


Tafad'a mata komai nata sannan tasanar musu da abinda yake tafe da'ita,a razane Mama  tace"...Kina nufin Fatima Y'ar mu kinsan inda take?,tace"...a da ba amma yanzu sam bansan inda takeba,kuma ni wlh koda kayan da kud'in duka sun b'ata nayafemata ,saboda naji dai-dai lokacin data tafi customs sunyi kwacen kaya to ina tsammanin Harda ita,to may be abinda  yahanata dawowa kenan,amma muna addu'a tunda dukanmu munsan meke damunta Allah ya tsareta a duk inda take.

To rasuwar Fatima ce ta k'ara raguzamin rayuwa,saboda ina tsananin sonta har cikin raina,to a haka na baro kano nakama hanyar Lagos.

Acikin mota muka had'u da wata mata da yaranta, to dayake inda son yara akwai wata Y'ar k'arama acikinsu mai suna Fatima,haka kawai naji inasonta don haka ko'ina muka sauk'a innaga abu sena siyama yaran.

Gata yarinyar bazata wuce sa'annin Fatima na ba,gata itama kyekkyawa  da'ita, to ahaka harnafara  janta da wasa dayake kujerunmu na kusa.

Nace"....miye sunan ki cikin gwarancinta tace"...Fatima,sontane ya sake shiga ta a karo na biyu nace"....Allah ya rayaki ya miki albarka cikin gwarancinta tace"...mamin a raina nace"...itama tanada wayo Kamar Fatima ta.

Tohm kubiyoni donjin yazata kaya ne.

Taku a kullum Young Novelist.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎


Alk'alamin Auta✍✍✍

UQUBAR UWAR MIJINAWhere stories live. Discover now