Part 20/21

331 26 0
                                    

🐲🐲🐲
         UQUBAR UWAR MIJINA.
🐲🐲🐲
(Based on True Life Story) (Full of Sorrow).

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.

Dedicated to UQUBAR UWAR MIJINA Fans ina godiya matuk'a da kulawarku a gareni naga sak'onku kuma na gode,lokacin danaga yawan Msges dinku har kishi ya kamani don ganin duka msges d'in na Novel ne lol,Tnx daku nake tunk'aho Fans,Wannna page d'in na kune.

Rashin lafiyace takamani kuma alhamduliilah naji sauk'i,Nagode da Addu'a.

Allah yabaki lfya Bestie Na'eema I miss u a lot.

Bestie Aisha karkiyi ciwo fa Kinga bame kawomin kindirmo fa,kuzo keda Yaya.

Anti Rabi'ah ina gaisuwa.

My Troublesome Sayner Happy Graduation Allah yak'ara lfya da Ilimi yasa ayi amfani dashi.Amin.

(20)&(21)

       Washe gari da safe bayan  mun tashi nayi sallah  a d'akin na fito waje,a parlour na tadda matar da wata budurwa a zaune.

Har k'asa na tsuguna na gaidata ta amsa fuska a sake tace"....Fatima ga k'anwarki mufeeda kuma inason sanin meyakawoki garin kano cikin dare har waennan miyagun ke Neman halakaki?."

Murmushi nayi na fara bata labarin rayuwata batare dana b'oyemata komai ba,hatta garinmu ban b'oye mata ba.

Jinjina kai tayi tare da share hawayen dake fuskarta tace"...insha Allah zan taimaka miki karki damu,haka rayuwa take kowa da abinda yake ganin yayi masa dai-dai."

Kwana na biyu da zuwa gidan tafiya takama Hajiyar zata tafi k'asar Togo da Ghana siyayar kaya saboda tanada kud'i, tana siyowa kayan tazo tasaida anan kano babbar Y'ar kasuwace.

Bayan ta tafi naci gaba da zama nida Y'arta Mufeeda wacce babu ruwanta gata da son mutane,Kuma tanason Fatima Sosai saboda in akaga Fatima a hannuna to Mufeeda na Makaranta,don ko makarantar Islamiyyace da'ita take zuwa haka intaje   zasu dinga d'aukarta.

Bayan kwana hud'u Hajiya ta dawo da siyyara kayan kasuwarta,haka tayi mana siyayya ba kad'an ba musamman Fatima wacce nata yafi na kowa kyau da tsada.

Godiya mukayi mata harta nuna bataso saboda Allah tayi,Kayan Fatima Mufeeda ta kwashe ta tafi dasu d'akinta tace"...Anti Fatima Munbar miki d'akin ki kije ki huta mukam munk'ama sabon d'aki."

Murmushi tayi tace"....to Allah ya kiyaye hanya daman ta hanani walawa a kan gadon, Hajiya tace"...A'a kam kar'ayiwa Y'ar uwata  Sharri kam don batada rigima ko kad'an. "

Bayan ta hutane washe gari tashiga garin kano don rabawa  Y'an kasuwa kaya,su Fatima kuma suka tafi makaranta.

K'irane ya shigo wayata,d'auka nayi naga sabuwar number amsawa nayi tare dayin shiru,muryar data doki dodon kunnenane yasani tashi cikin mamaki nace"...Khamis!!!,yace"...Na'am Fatima kina lafiya?nace"...lfya kalau ykk y hidima da aiki?,Be amsaba illa cemin dayayi ya Ilham nace"...tana lfya tana gun mama".

Da mamaki yace"...to ke kina ina?,uhmm ina kano gun Y'an uwanmu yace"...to ngd kibani izini inason naje naga Ilham nasan banmata adalciba dana watsar da'ita tun tana k'arama,Uhm aii bakomai komai ya wuce, godiya yamin sannan na katse k'iran.

To yau yakama watana biyar a gidan Hajiya kuma alhamduliilah tana kula damu sosai,Zaune muke a parlour Hajiya tace".....Fatima inaso kifara business banason zamanki haka don haka na yanke shawarar nan gaba idan zan tafi tare zamuje kiga yanayin kasuwar kuma kisan hanya daganan kuma zanbaki jari kema kifara kasuwanci dashi Allah yasa mu dace."

Godiya nayi mata sosai kuma naji dad'i.

Ashe wannan tafiyar itace silar  rushewar farincikina,itace sanadiyyar rashin zaman lafiya ta.

Tohm Ku kasance tare da YOUNG NOVELIST.

TAKU A KULLUM.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Alk'alamin Auta ✍✍

UQUBAR UWAR MIJINAWhere stories live. Discover now