part 51

58 4 0
                                    

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

UMMIEN2018

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

ina mika sakon ban hakuri ga daukacin makaranta wannan littafi a bisa jina shuru da kukayi na kwana biyu sakamakon wasu dalilaii❤️

      💝ZATOH💝

     page 051.

sunana khadeeja al-hussein...

mahaifina dan asalin manguno ne a jihar borno,kuma malami neh na islama hakan yasa wajen tafiye~tafiye na mallanta yafado cikin garin maiduguri a unguwar furii...

inda ananne yahadu da yagana wato mahaifiyata...

yagana yar uban gidansa ce...dan haka ba adauki lokaci ba aka sanya ranar aurensu kasancewrta mace mai saukin kaiii...

bayan bikinsu kuma da shekara ta haifo danta namiji inda yaci suna umar(ya faruq),bayan shekara bakwai kuma sai ni khadeeja (kubra),sai nusaiba,falmata,sai autan mu faysal...

muntaso munga mahaifinmu mai sassauran ra'ayi akanmu domin koh komai shike zaba mana kasancewarsa babban malami...

koh fita nanda makwafta zamuyi maman mu bata da hurimin bamu iznin zuwa muddin bashi yace muje ba...

haka muka taso cikin tsatstsauran  ra'ayi na mahaifinmu...

bama kamar ni wanda bansan dalilinsa ba...

lokacin da na kammala secondry schl nawa ma shi yaxaba mani course dinda zankaranta a jami'ah...

domin koh ya faruq ma shine yaxaba masa inda yanxu shi ma'aykaci neh a ma'aikatar nefa...bayannan kuma yaxaba masa matar aure yanxu haka suna zaune a unguwar gwange na cikin maidugurii tare da yarinyarsu guda daya...

alokacinda nafara zuwa makaranta yasamin dokar kan lallai idab zantafi makaranta saina saka hijabi har ksa sannan kuma nasaka nikap da safa...

wanda nikuma hakan kwata~kwata baya cikin ra'ayi na sabida inason shiga irinta yanxu...

shi mahaifina a ZATON sa...sanya hijabi da su nikap shine kaxama cikakken mai hankali nanko baisan ba haka abun yake ba...

ni bana iskanci amma kuma shigar kaya masu kyau na matukar birgenii...

hakan yasa na zabawa kaina mafita idan zanfita nayi kalar shigar dayake so ya ganni bayan nafita kuma na cire hijabi da su nikap da safa...

wanda mutanen cikin unguwannan da dama muna haduwa dasu a makaranta amma basu san cewa nice kubra ta unguwar nan ba...

Abinda nake fatan mahaifina ya fahimata shine...

bawai ta wajen dressing ne za'ah iya banbance yan iska dakuma salahai ba sabida imani ba a tufafi yake ba sai ciikin zuciyar mutum...

sannan kuma inda ace nice shi wlhy baxan takurawa yayana tun farko ba...barinsu,zanyi naga kamun ludayin kowacce daga cikinsu...idan naga akwai gyara a lamuransu sai ina masu gyara cikin lallalma domin koh yayan,yanxu ka haifesu baka haifi halinsu ba...

yanzu na tabbata wani yaxo yace masa ya ganni dashigar banza sai yace sam ba haka bane sabida baya barin yayansa su fita cikin kalar wannan shigar...yanxu mahaifina da'ace za'asa shi a gaba ace yakawo halina wlhy koh guda biyu cikin goma baxai kawao ba sabida yadaurani akan ra'ayinsa...

yanxu haka ina da shekaru 24 a duniya.....acikin kannena biyu nusaiba tayi aure a gombe sai kuma kanwa ta wacce take 100lvl a makarantarmu...saikuma karamin kaninmu dayake ss2 a secondary...

kunji takaitaccen tarihi na...

takarasa tana murmushi...

duk jikinsu yayi sanyi kuma basuga laifinta ba koh kadan saina mahaifinta domin koh bai tsaya ya fuskanci wacece yarsa ba koh kadan ballantana yasan ta inda yakamata yafara mata gyara...

husnah kam wayarta ta dauka dake ajiye a gefe ...

sallama suka mata daganan sukayi sallama tarakasu bakin kofa...

bayan ta shiga gida ta tarar mahaifiyarta zaune cikin kitchen tayi tagumi da alamun akwai abinda ke damunta...amma bayanda batayi akan tafada mata damuwarta ba takii...

dole ta hakura tawuce dakii...


PLS COMMENT AND SHARE👏🏻

FATEEMA FATEH
(CONCEALER)
(TA UMMY)
WHATSAPP NUMBER:09076427357




💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

  UMMIEN2018

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

         ummie fateh🖊️

ZATOHWhere stories live. Discover now