part 11-15

95 5 0
                                    

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

  UMMIEN2018

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

allah kajikan iyayenmu baki daya wayanda suka rage allah ya kara musu lafia da nisan kwana wanda xasu amfana dashi duniya da lahira😍

     💝ZATOH💝

           11――15

Yan class sunyi tsit a class din kowa yacika da al ajabin wayannan marasa kunyar,basuyi tunanin har abunnasu yakai haka ba!

marinda malamin yayi wa husnah ne yasa zahra ta wanka masa marin farko ganin hakane yasa husnah itama ta kara masa ta dayan gefen!

Hmmm mallam bari kaji abinda baka sani ba!
idan kaga ka mareni na kyaleka toh bawai ina tsoronka bane amma kasake koh da wasa ka kara marin husnah wlhy sai kasha mamaki sosai ba kadan ba!
aykin banza kawai😏
fadar zahra kenan tana murguda masa baki!!

mallam karkayi tunanin marinda kamin na rama!!
koh kadan ba haka abin yakeba,marinda kai wa zahra na rama mata dafan ka fahimta??

koh gobe idan ka ganmu karkayi gigim kara daura hannu akanta idan ba haka ba wlhy sai kayi dana sanin zuwanka garin😏

Shikam a duk tsawon rayuwar babu wanda yataba masa irin wannan tozarcin da yarannan suka masa,sabida shi ba mai shiga abinda bai shafesa bane balle harta kai ga an masa irin wannan rashin kunyar wai mari??
marin ma kuma yara kana da akalla zai basu 10yrs amma suka mareshi?

hmm lalle dole ya koya musu hankali

mtseww husnah ta doka wani uban tsaki🤕

fisgo hannun zahra tayi a fusace suka bar hole din,direct wajen hawa bos suka tafi suna zuwa koh suka shiga sai

napep suka tara bayan an sauke su amma babu wacce tayi magana har xuwa wannan lokacin,ana saukesu suka fada gidan su husnah koh sallama babu balle suyiwa mami sannu da gida sukayi dakin su!!!

chilli husnah tayi da jakanta kawai ta fashe da kuka

zahra kam tasan haka zata faru domin koh tasan halin husnah da shegen ragontaka,ita taga kokarinta ma da bata fara kuka tun cikin napep ba har saida sukazo gida!

am sorry sis kinga idan kina kuka nima fah kuka zanyi😔
takare maganar kaman zatayi kukan!
jin haka yasa husnah tsayawa da kukan tafara magana cikin takaici

Wlhy sis wannan mutumin ya raina mu sosai ba kadan ba
kawai danshi lecture shine akace masa ya maremu a gaban student gayyar son ya jawo mana raini a class??

zahra tace hava sis yanxu kam ay shikkenan tunda mun rama na tabbata yanda yakeji da kansa a cikin makarantarnan yanxu kam zai zubda su a gefe ya fuskanci abinda yakawosa har yakoma garinsu!!
domin koh marinda na masa ma kadai wlhy na tabbata yashigesa ballantana kuma wanda kika masa!

bakiji yanda karar marin ta karade cikin hole dinba neh?
takara maganar tana kwashewa da dariyar mugunta wanda husnah ma ta mance da wani bacin randa ya kunsa musu takama dariyar itama
…………

Salatinda sukaji mami nayi neh ya ankarar dasu akan subutar bakinda sukayi

aykuwa a dari sukayo waje suna kokarin rufe maata baki domin sun tabbatar ammy najin wannan batu kashinsu ya bushe kamin su dady su dawo gidan

mami dan allah kiyi hakuri kar ammy da jiyoki ta shigo g……

menene ake cewa ayi shuru kar najiyo na shigo?

muryar ammy suka jiyo daga kofar gidan
aykuwa a dari suka doshi daki amma kamin su sami zarafin shiga muryar mami ta ratsa dodon kunnensu

Wlhy idan kuka sake kuka shiga dakinnan kun shiga uku a cikin gidannan!

cak suka tsaya a lokaci daya domin koh yanda tayi maganar babu alamun wasa acikin muryarta koh kadan

shigowar ammy ne yasa cikinsu kara kadawa domin koh muddin taji abinda sukayi kashinsu yabushe yanda sukaga ran mami ma ya baci ballanta kuma ammy da tafi mami xafi sosai ba kadan ba💃

ba tambayarku nake ba mai kuka aykata nace????

wayyo dan allah ammy kiyi hakuri wlhy baxamu karaba

suka fada cikin kuka

yaya mai sukayi neh wai?
nankoh mami ta kwashe duk abinda taji suna fada ma ammy

salati tayi tasanar da ubangiji

ku tsuguna a gurin kamin na karaso,wato ga sa'annin ku a tsaye kuma kuna tsaye koh?

kafin ta rufe baki har sunkai kasa

saida aka musu tas kamin ammy ta umarce su maza ko wacce ta dauko tsintsiya

share gidan tsap tasa sukayi da wanke~wanke kamin ta kadasu gidanta ma saida sukayi wanke wanke da shara kamin ta bukaci su samu guri

nasiha ta musu sosai mai shiga jiki wanda sunyi kamar sun dauka amma koh ba haka ba,
yana shiga ta kunne daya yana fitane

sallah sukayi kamin kuma suka xauna domin huce gajiya sabida dukkansu ba gwanayen son ayki bane amma kuma sun iya saidai basa sonyi

Wajen 5:30pm suna zaune sukaji sallamar ya abdallah
aykuwa nan suka natsu kamar basu nr masu surutu kamar sun ari baki ba...

tsoronsa sukeji sosai sabida shikadai ke cin kaniyarsu idan sunyi laifi

gayshe sa sukayi ya ansa masu cikin sakin fuska,ammy ne tafito ciki fara'arta sosai kamar ba ita ke daure fuska dazu ba!

gaysheta yayi tamasa ya aiky kamin ta bukaci zahra takawo masa abinci batayi gardama ba takawo masa saida ya gama cin abinci tas kamin yace bari yashiga yagayawa mami yadawo

ahanyar fitane sukayi clashing da wani yaro dan 11yrs gaishesa yayi kamin suka wuce tare gida mami

itama hakan ta suka gaysa cikin sakin fuska
ta tambayeshi kozaici abinci??

ah ah mami saida koh huzaifa ne zaici donnaga yanxu yadawo daga islamiyya

saida yaro yaci abincinsa yayi wanka yachanxa kaya suka wuce masallaci tare da ya abdalllah

FLASH BACK



PLS COMMENT AND SHARE👏🏻





FATEEMA FATEH
(CONCEALER)
(TA UMMY)


💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

   UMMIEN2018

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

         ummie fateh🖊️

ZATOHWhere stories live. Discover now