part 6-10

107 8 0
                                    

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

  UMMIEN2018

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

dedicated to :
ummuh adnan
ummuh alqasim
maryam fateh




     💝ZATOH💝

      6――10

Kuka suke kamar wayanda aka aykowa da sakon mutuwa,
ammi kam tana jinsu amma koh a kwalar rigarta domin koh ba yau tasaba ganin wannan iskancinnasu ba!

ganin yanda zahra ke kuka ya sanya husnah dakatawa da nata nafara lallashinta
saida kowacce tayi kamin husnah ta zayyaneh mata yanda sukayi da mami

kiyi hakuri kinji dear nah!
kinsan halinsu ammi sarai
su gani suke kamar shigarda mukeyi shine zaisa muzamo masu xubda mutuncin mu a waje nankoh basu san 💝ZATOH💝 zanubi bane!
takare maganar tana wani tura baki kamar a gabansu take zancen

hmmm,ki rabu dasu yanxu kitashi ki shirya domin koh yanxu naga wajen 2 ma takusa karmuje muyi late wannan dunkum din yahana mi shiga!
fadar husnah kenan tana murguda baki
wannan dabi'arsu kenan duk maganar daxasuyi sai sun murguda baki wanda wasu suke ZATON kamar rashin kunya ce
amma kuma haka dabi'arsu take

itama shiryawa tayi cikin shiga irinta husnah wanda banbancinsu colour ne nata purple💜 na husnah pink💗

wanda takalmansu yaxamana iri daya wato have cover

koh kai kagansu kasan sun hadu ba karya sosai ba kadan ba

bayan sun fito suka ga ammi na kokarin shiga daki ganinsu datayi neh yasata dakatawa tana binsu da kallon takaici domin koh shigar da sukayi kwata kwata bai kamace su ba!

lallema yarannan,watoh haka kukeso muzuba muku ido yan anguwa suna gulmarmu ace mun barku kun lalace koh?

hava ammi wai kema so kike yanxu kisa mubata wannan wankan damuka dauka?

gaskiya hakan ba mai yiyuwa bane😏
fadar zahra kenan!

fada mata dai😏
inji husnah da fada itanma tana wani murguda baki

ammi kam rike baki tayi tana kallonsu,halinsu na matukar bata mamaki
kwata kwata yarannan basa shakkarsu sannan kuma akayi musu fada su hau kuka kamar wayanda aka dake su

itacen gefenta ta wawuro tayi kamar zata jibgesu aykuwa  a dari sukai waje suna kyalkyala daria domin koh sunsan halin ammy tsaf yanxu saita mammakesu

saida suka tsaya suka gama dariyarsu kamin sukayi bakkin hanya suka tsare mai adaidaita sahu

saida aka saukesu abakin gate domim koh napep din bana makaranta bane baza a barsu su shiga dashi ba

UNIMAID(university of maiduguri) aka ijiyesu

kowa kallonsu yake cikin sha'awa domin koh babu wanda yasan cewa ba yan biyu bane sai wayanda suke anguwa daya,sabida tsabar kamar da suke gashi kuma halima yazo daya saidai abinda ba a rasa ba

suna isa bakin lecture hole sukayi turus ganin mallam dunkum acikin class yana lecture kamar wata mace tsabagen yanda yake maganar kaman wanda aka sashi dole ,sukoh yan class sunyi kamar ruwa yacisu babu mai magana sabida yanda ake tsoronshi amma banda zahra da husnah!

kinsan mai za'ayi husnah?
ah ah sai kin fada

kawai zo mu waske mushiga sai munga karshen fitsararsa yau dinnan

sukadai ne masi wannan tsaurin idon kaf cikin class din,kwata kwata basa jin shakkarsa koh kadan

husnah ce tayi gaba zahra tabi baya wajen shiga kamin suka jero gwanin birgewa ga duk wanda yagansu amma banda shi,sabida shikam haushi suke basa yaran sosai ba kadan ba sabida tsaurin idonsu yafi karfinsu

saida suka zo tsakiyar hole din yadaka musu tsawarda saida class din yadauka wanda yayi sanadiyyar nutsar da sauran masu surutu acikin class din

out i said!!
yakara fada musu cikin tsawa! amma shiru kakeji kamar wayanda basusan dasu yake ba!

ganin yana dunfarosu neh yasa cikin zahra kadawa,,,,,husnah ganin zahra na shirin bada sh cikin jama'a yasa ta maka mata uwar hararar da babu shiri ta dawo setti

karasowarsa gurin baiyi wata~wata ba ya kwadawa zahra wani marinda saida taga wuta
aykuwa ganin haka yasa husnah ta maka wani uban ashar dinda shima kansa saida yaji babu dadi!

kai wani irin mara hankali neh mallam?

a wani doka ne akace idan dalibi yayi maka laifi ka dau hukuncin duka akansa?
wlhy kayi kadan karamin dan……

marinda tajineh yasata yin shuru daga abinda tayi niyya

Aykuwa saiji kake tas karan wani marin dayasa yan class yin tsit

kamin kiftawar ido kuwa wani karan marinne yakara giftawa cikin wannan hole dinda saida ya ansa!😨…………

PLS COMMENT AND SHARE👏🏻

FATEEMA FATEH
(CONCEALER)
(TA UMMY)

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

   UMMIEN2018

💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

         ummie fateh🖊️

ZATOHWhere stories live. Discover now