MAKAUNIYA CE

By Jiddasmapi

17.9K 991 101

Ta mak'ance ta dalilinshi Amma baisan dahakan ba, ya wulak'anta ta, anci mutuncinta a gidansu.. More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
page 35
page 36
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
Completed✔

page 37

375 20 2
By Jiddasmapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 37...
*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Daddy ne yayi dariya yace "to masha Allah idan har abinda muke zargi a tsakaninsu ya tabbata to babu Wanda zai kaini farin ciki, domin ni na d'auki Hamma Yarda Kamar d'an Dana Haifa ne"

Baby tace "ai Daddy nima zanyi farin ciki matuka idan ta Aureshi sabida yanada hankali gashi kuma yana girmama na gaba dashi, kuma yanada fara'a"

Mommy tace "yanzu dai muyita Addu'a Allah yasa hakan ya kasance sannan mu  kara zuba musu ido, mugano menene a tsakaninsu, idan yaso kafin mutafi sai ayi maganar Aurensu ko?"

Daddy cikin fara'a yace "kwarai kuwa Hajiyata"

Minal saida ta gaji da gudun kafin tasamu wuri ta zauna tana naki, Hamma Yarda dariya yayi yakarasa wurinta yace "sorry Hajiya nasan kin gaji sosai kawo kopin nasa miki"

Minal had'e rai tayi ta kauda fuskarta gefe,
Cikin tsokana Hamma Yarda yace "shikenan tunda bakyaso ni bari naje na shanye"

Minal taso tayi fishi taki shan Nonon Amma yanda takeson Nonon yawuce misali, Turo baki tayi tace "gashi kasamin kad'an"

Kwashewa yayi da dry kafin ya d'iba mata, karb'ar kofin tayi ta d'aura a bakinta saida tayi Tass kafin ta sauke.
Haka sukaci gaba dazama agidan har sukayi one weak,
Acikin 'yan kwanakin Minal Nono kawai takesha, idan har batasha Nono ba tofa ranar akwai matsala, komin dare sai Hamma Yarda yaje ya nemo mata tasha kafin take iya bacci, Abun har mamaki yake baiwa su mommy, 'yammata kuma sai zuwa gidan suke wai sunason Baby da Minal suzama kawayensu, wani lokacin Inna ta korasu wani lokacin Baby tabasu numbarsu.

Hamma Yarda kuma yakamu da soyayyar Minal bana wasa ba, Sam bayason yaganta tayi tagumi zaije ya zauna agefenta yayi ta bata labaran dariya, har saita warware tafara dariya.

Ta b'angaren su Mommy kuma gani suke kamar Minal da Hamma Yarda suna soyayya, hakan ba karamin dad'i yayi musu ba,
Ita kuma Minal a matsayin d'an Uwa ta d'auke Hamma Yarda kamar yanda Baby ta d'aukeshi.

Yau da yamma su Minal suna zaune acikin gida bayan Minal tagama shan Nonone, taji zuciyarta tana juyawa, da sauri ta tashi tabar wajen mutane, Amai take shekawa tsakaninta da Allah, mommy ce takarasa wurinta tanayi mata sannu, Minal ciwon ciki take sosai, Rike cikinta tayi tana kuka, Mommy ce taji gabanta yana fad'uwa Dan ita tunda dad'ewa taso ta fahimci wani abun, innace ta karaso wurin tana tambayar Ko lafiya?
Ganin Minal tana amai rike da ciki itama taji gabanta yana fad'uwa, hannun Minal tariko tana kallo, da sauri tace Muga idonki Minal?
Minal da ta fita a hayyacinta ta mike tazo wajen Inna, bud'e idonta tayi tana dubawa, Innace tayi Salati cikin kuka tace "Shikenan wannan yaron ya cuceki Minal cikine dake".

Minal tayi baya baya zata fad'i da sauri Hamma Yarda ya riketa, ya d'auketa cakk sai d'akin Inna, A hankali ya kwantar da ita akan gado yana me tausaya mata, Baby ce ta d'ibo ruwa aka yayyafawa Minal da karfi tasaki ajiyar zuciya, hawayene yafara bin fuskarta masu d'umi, Mommy ce ta riko hannunta tace " kidaina kuka idan Allah ya yadda bazaki zauna da cikin nan ba, dolene azubar dashi".... Da sauri Inna ta katse Mommy tace "bakida hankaline Maryam? Wani irin magana kike? Kinsan hukuncin Wanda yazubar da ciki kuwa? To kul karna sakejij kinyi irin wannan maganar koda wasa"

Mommy ce tace "kiyi hakuri Inna bazan karaba insha Allah to amma ina tunanin idan har mutane suka San ta haifi d'a ba Aure wazai Aureta?"

Hamma Yarda ne yace "ni zan Aureta Mommy"

Inna tace "yawwa yanzu abinda za'ayi asibiti zamu kaita a tabbatar da hakan, sai muci gaba da kulawa da ita idan ya gagara ma saiku tafi kubarta anan idan ta haihu saita koma, idan yaso sai ayi bikin a can"

Minal duk abinda suke fad'a tana jinsu, shiru kawai tayi musu Dan ita batasan ma me zata fad'a ba.

_bayan kwana biyar_

Minal ce ta tashi da tsakar dare ta tashi Baby, baby ce ta tashi a firgice tace "meya faru?"
Minal da idanunta suka cika da hawaye tace "Baby wallahi bazan iya bacci ba"

Baby tace "meyasa?"

Minal tace "Baby banason cikinnan ya dameni banasonshi wallahi"....shiiiii Baby ce tarufe bakin Minal da hannunta tace " bakida hankaline? Ana yabonki da sallah sai gashi alwalama yana nema ya gagareki, Dan Allah kada kikara wannan maganar kinji? Bagashi Hamma yarda yace zai Aureki ba, Kinga idan bakyason Ku zauna a garinnan sai in roka Daddy yasiya muku gida a Abuja"

Minal juya bayanta tayi ta kwanta, bargo taja tarufa daidai wuyanta tace "Baby kidaina kawomin maganar namiji yana sona, da kinsan abinda yake kaina to na tabbata bazakiyimin maganar Kowani namiji ba"

Baby cikin muryar lallashi tace "kiyi hakuri my sister insha Allah bazan karayi miki maganar namiji ba, Amma inaso kizauna kiyi tunani akan Hamma Yarda kidubi cikin kwayar idonshi kiga tsananin soyayyar dayake miki.....Dan Allah Baby ya isa nace miki banason kinamin maganar namiji"

Baby bata kara cewa komai ba, ita lamarin Minal yana d'aure mata kai matuka.

Bilal bashida magana kullum sai maganar Minal, Afrah tana kula dashi daidai gwargwado, wani abinda yake bata haushi shine idan tayi mishi Abu sai yace "Dan Allah ki nemamin Minal" wannan maganar ba karamin haushi yake sata ba, kamar kullum yauma Bilal yana kwance akan gado sabida zazzab'i dayake damunshi, Doctor ne yazo yayi mishi gwaje gwaje, Kiran Afrah yayi yace "ina Mahaifinku?"

Afrah tace "Daddy yayi tafiya sai jibi zai dawo"

Doctor yace "yayanki yana cikin matsala, kudaina barinshi yana tunani sabida lafiyarshi, idan yaci gaba da wannan tunanin tofa zuciyarshi zata iya bugawa"

Afrha share hawayenta tayi tace "to doctor nagode"

Komawa wurin Bilal tayi ta riko hannunshi tana kuka tace "yaya meyasa zakasa wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar a ranka? Yarinyar nan fa bata Sonka, da ace tana sonka wallahi data zo Inda kake, shawaran dazan baka shine kacire Yarinyar nan a ranka ka manta da ita kayi rayuwarka  yanda kakeyi ada"

Da karfi Bilal ya kwace hannunshi, cikin tsawa yace "tashi kifita"

Afrah tabud'e baki zatayi magana yace "nace kitashi kifita"

Ganin yanda ranshi ya b'aci ne yasa ta tashi a fusace tafice a d'akin, sai d'akin Hajiya babba, tana zuwa tafad'a akan gado tana kuka me sauti, Hajiya babba ce tafito daga toilet tana ganin Afrah tace "Wace wannan nake gani a d'akina kamar matar Bilalu?"

Afrah tamike fuskarta duk hawaye tace "Hajiya babba kema tsokanata zakiyi? Inji da abinda Bilal yamin ko inji da maganarki?"

Hajiya babba ce tayi 'yar dariya tace "habawa Afrah, keda kika nuna Bilalu yafini matsayi awurinki, Har wani hararata fa kike idan kuna tare, ni dama nasani ba sonki yakeba, nasan wannan ranar tana zuwa, kad'anma kika gani ai, bani kika maida kamar wata bare ba?"

"Dan Allah Hajiya babba ki kyaleni najida abinda yake damuna"
Tana fad'an haka ta juya tayi kwanciyarta.

Bilal ranshi idan yayi dubu to yau duk sun b'aci, wayarshi ya d'ako yashiga wurin call, Number Latif yake kira sai yaji ana mishi warning, tunawa yayi ranarda yadawo daga India yasiyi kati ya jefa a aljihunshi, tashi yayi yafara Neman rigar daya cire ranar, cikin sa'a sai ga rigar d'auka yayi yasa hannunshi cikin aljihun yana laluba, jin yayi ya tab'a wani takadda, Saurin Ciro takaddar yayi yana dubawa, warewa yayi yana dubawa da fari baiso ya karanta ba, wata zuciyar tace ka karanta, karantawa yafara, a take jikinshi yafara Rawa ganin rubutun dayake jikin takaddar, yasar da takaddar yayi yad'au makullin mota yafice da gudu, me gadi ne zaune yanajin redio ganin Motar Bilal yazo da speed yana kokarin b'alla get yasashi tashi da gudu ya bud'e mishi kofar, Bilal gudu kawai yake akan titi, mutane sai kallonshi suke,
Gani yake kamar motar baya mishi gudu burinshi kawai ya iso inda yayi niya.

Daddy yafito daga Bedroom nashi yana dariya, Waya ya d'auko yadanna wurin Call, dariya yayi me isarshi kafin yace "Alhj Nura Allah yasa kar asami matsala domin yafita da mugun gudu" dariya  yakara kwashewa dashi yace "shifa baisanma ina gari ba, zatonshi bana gida, akula Dan Allah kar a sami matsala, idan fa aka samu to kaima kana cikinta" katse wayar yayi yana dariyan asara.

✔ote & comment

   Wattpad

_@Jiddah S Mapi_

Continue Reading

You'll Also Like

180K 36.4K 54
Becca Belfort i Haze Connors, choć przez swoich znajomych zmuszani do spędzania razem czasu całą paczką, od dawna się nie znoszą. Dogryzają sobie prz...
762K 46.4K 49
𝐈𝐧 𝐭𝐡𝐞 𝐓𝐚𝐧𝐠𝐥𝐞𝐝 𝐰𝐞𝐛𝐬 𝐨𝐟 𝐇𝐞𝐚𝐫𝐭𝐬, 𝐚𝐧𝐝 𝐩𝐮𝐫𝐬𝐮𝐢𝐭 𝐨𝐟 𝐓𝐫𝐮𝐭𝐡𝐬, 𝐋𝐨𝐯𝐞 𝐰𝐞𝐚𝐯𝐞𝐬 𝐢𝐭𝐬 𝐦𝐞𝐬𝐦𝐞𝐫𝐢𝐳𝐢𝐧𝐠 �...
3.1M 252K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...
2.9M 191K 89
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...